Skip to content

Chapter 9

Chapter 9

Dan Mace Book One Complete Hausa Novel 1,298 words 0 views Progress saved
Download Book

kuma ya rage na mai niyya,iidan ka ji baka iyawa kana fita daga gida zaka iya wucewa gararinka,idan ka daidaici lokacin tashi ka biyo ayari a dawo tare,,ruwanka ne kuma rayuwarka ce. Lokacin da baba ya fara harkar bin y'an siyasa,sai ya zama babu ruwansa da wani binciken muna zuwa ko bama zuwa duk da a bayama ba damuwarsa kenan ba,shi dai yasan duk k'arshen term zai biya school fees na gaba d'ayan mu,wad'anda suke zuwa da wad'anda basa zuwa,damuwarsa shi ne a tattara masa shaidar biya na gaba d'ayan mu a bashi,shin mutumin da aka bawa shaida kamar haka ta yaya ne ma zai san wanda bai je ba.? Life goes on,,bayan tsayin shekaru da muka shafe still rayuwar gidanmu yana a yadda yake babu wani sauyi,kullum abu biyu ke yawo a tsakani dad'i/kishiyarsa da rashin watar zaman lafiya,,cikin hukuncin ubangiji a dai² lokacin dana kammala secondary school Allah ya kawo min mijin aure daga cikin y'ay'an abokan Baba,,tunda aka tsayar da ranar aurena nake cikin damuwar barin gida,a zahiri kuma ba wai ina damuwa bane saboda zan tafi,sai dan a wannan lokacin duka damuwata ita ce Hauwa,tunani na a kullum yadda zan tafi na barta,saboda ban san yaya rayuwarta zata kasance ba bayan bana gida,na san matar babanmu bata kula da kowa a baya ba da yake cikin gidan bare yanzun nayi tunanin za'a fara,tak'amarta kuma shi ne bata haifa ba,babu wanda zata raina sannan baba ya nuna fifikon soyayyar mu akanta,shi yasa tunda ta shigo gidan bata tab'a cewa muyi wannan mai kyau ne,ko mu bar wannan bashi da kyau,tunda aka tsaida ranar aurena hankalina ya kasa kwanciya,,but a wannan lokacin Hauwa tayi abunda ni ya kamata ace nayi,kasancewarta mai k'ananun shekaru a kaina,kamata yayi ace ni zan kwantar mata da hankali,amma abun mamakin shi ne ita da ake ganin bata da cikakken hankali ita take kwantarmin da hankalina,a duk lokacin da zata ganni cikin damuwa takanyi k'ok'arin taga ta sanya murmushi akan fuskata,har Allah ya kawo lokacin aurena,aka yi biki lafiya aka kai ni d'akina,a daren daya zama daren farko na rabuwarmu da Hauwa,ya kasance ni ina kukan rabuwa da ita a karon farko tun bayan tasowar mu,itama tana kukan shiga sabuwar rayuwar da babu ni a cikinta,a hakan ina kallo y'an gidanmu suka wuce suka barni,naji babu dad'i sosai duk da ba zaman lafiya muke yi ba,amma ganinsu kad'ai a tare da ni nasan zai bani kwanciyar hankali,,tsakanin gidan mu da gidan da nake aure babu nisa,but mu a gare mu a wannan lokaci gani muke kamar an gama nisanta mu da juna,bayan y'an rakiyar amarya sun watse ango ya shigo d'akin amarya.." Shiru Annie tayi tana sauke numfashi da kallon Nuraz sannan taci gaba "A bisa tsarin addini komai angona yayi min,na tabbata mijina na sona haka nima ina sonsa,kasancewar mutum ne shi daya dace da burin kowace y'a mace,,bayan komai ya lafa,duk wata hidima an k'are,aurenmu ya samu wasu kwanaki haka nan sai nayi nufin tuntub'ar babanmu akan maganar ko zai bari Hauwa ta dawo gurina dan a yadda na kula da ita cikin lokacin tana cikin damuwa da takurawar y'an gidanmu,amma kuma idan na tambaye ta duk lokacin da ta zo gurina bata iya sanar dani sai dai tace min komai lafiya,ni dai haka nan duk lokacin da zata fad'amin haka nakan ji ban gamsu ba,shi yasa lokaci guda nayi nufin samun babanmu da batun,mijina ya bani goyon bayan na karb'o ta ta dawo hannuna,cike da wannan k'arfin guiwa da sa hannunsa muka je tare har gaban Baba da maganar,duk da a d'ar² muke bcos bamu sani ba zai amince ya bamu ita ko bazai amince mana ba mu dai gamu nan a probability.... #Share. #Real Smasher. 💠💠💠💠💠 *©®2020.* *'DAN MACE..* (Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥 *WATTPAD:REAL-SMASHER898.* https://my.w.tt/29u2S26SG2 Pᴀɢᴇ 4. #Sᴏᴜʀᴄᴇ Mun samu Baba a gida,bayan mun shiga mun gaisa da y'an gidanmu,muka samu Baba da batun,lokacin da muka gabatar da buk'atar mu ta son tafiya da Hauwa amma sai da amincewarsa,bai nuna mana komai ba yace muje zai yi tunani,idan zai iya bamu ita to,,ni dai tunda naji ya ce haka jikina yayi sanyi,dan Baba mutum ne shi kaifi d'aya,idan zai yanke hukunci da k'arfin guiwarsa yake zartarwa a take,haka ma idan bazai yi ba a take yake yankewa,but matuk'ar kaga yana abu kamar baya so,tabbas there's something behind,idan anyi sa'a kana da saurin fahimta ka gano dalilinsa na k'in amsa maka kai tsaye yace bazai yi ba ko akasin haka,jiki babu k'wari muka yi sallama da Baba muka tafi,,kwana biyu tsakani muka ji shiru and there's nothing in return akan maganar,mijina ya sake tuntub'ata ko zan sake tunawa Baba maganar irin ace ko mantawa yayi.? Gudun kada nace wani abu shima ya ga laifi na,tunda ni dai na fahimci Baba bazai bamu ita ba,na amsa da "Toh" amma a zahirin gaskiya nasan Baba bai amince zai bari Hauwa ta bar gida ba,,lokacin da na je gida mun gaisa da Baba kafin nayi masa maganar ya haumin fad'an akan wane dalili zan d'auko masa mijina nace muna so ya bamu Hauwa.? Tunaninmu bazai iya kula da ita bane ko yaya muke tsammani.? Ni dai nayi shiru na kasa cewa komai,k'arshe bayan ya gama fad'an yace "kuma kinji na fad'a miki ko da wasa bana son a sake min irin wannan titsiyen,ni ba lusarin uba bane da zan d'auki y'ata na bada ita zuwa wani gida al'halin nasan ba aure nayi mata ba,duk hak'k'in dake kaina dai² gwargwado ina rok'on Allah ya bani ikon kamanta saukewa,daga yau bana son a k'ara min maganar za'a tafi da ita wani gida,ban amince da barinta gidan nan ba" ni dai tunda yake fad'an kaina ke k'asa kuma har ya gama banyi ko tari ba,sai dana tabbatar ya gama na bashi hak'uri,nuna min yayi babu komai,daga nan ban samu damar shiga gida ba nayi masa sallama na wuce gidana,,da na dawo mijina ya ganni ni d'aya ya tambayi ina Hauwa? Na bashi hak'uri sannan na fad'a masa Baba yace muyi hak'uri da karb'ar Hauwa,duk dai yadda muka yi da shi sai na gyara batun cikin sanyin kalamai na fad'a masa ta yadda ba zai zargi komai ba,duk da yaji rashin dad'i amma haka ya gwada min babu komai muyi hakur'in,,a b'angaren Hauwa kuma zamanta a gida gashi nan dai za'a ce,tun bayan barina gida rayuwa ta fara yi mata wahala,wani abun a lokacin da nake gida duk da ba shiga harkar y'an gidan muke ba,sukan raga mata ko don ganin idona,to amma da yake yanzun bana nan kuma an ganta yarinya ce k'arama duk wanda ya deb'o cin mutuncinsa sai ya sauke kanta,haka nan dai take ta hak'uri da duk abunda za'ayi mata,har lamarin ya fara neman fin k'arfin shekarunta,bayan wani lokaci ta yanke shawaran sanar dani halin da take ciki,ta zo muka yi maganar da ita ta fad'a min duk halin da take ciki,sai na ji ban ji dad'i ba,to amma yaya zanyi tunda Baba baya so nayi masa maganar ya bamu ita,shawaran da kawai na bata shi ne daga ranar idan ta dawo daga makaranta ko wani gurin zuwa,ta daina zama a gidan tunda ganinta a tare da su shi yake janyo mata shiga damuwa da wahala,na bata damar idanma bata da shi ta dunga zuwa gidana

Table of Contents

Chapters

180 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180