Chapter 55
Chapter 55
ya kalleta yace "Sai ya tambaya.!?" Ta gyad'a kai,ya girgiza kansa yace "Ki sanar masa" tace "Toh ai bai tambaya ba!" Yace "there's no need to ask" tayi shiru tana tunani,ta jiyo shi yana fad'in "Idan kika fad'a masa ba tare daya tambaya ba,zai fi d'aukan maganar serious" ta jirkita kai gefe,silently tace "Toh",suka yi shiru duka,har suka zo skul d'in babu wanda ya sake magana,ta sauka tayi masa godiya,sannan tayi masa sallama,tana kallo ya fara tafiya da reverse kafin ya juya kan motar ya d'auki hanyar fita daga skul d'in,sai da taga yayi nisa sosai sannan tayi ajiyar zuciya ta fara tafiya,tana daf da shiga class wayarta tayi vibration,ta ciro ta daga jaka ta tsaya answering,sunan Aatif yasa ta tsaya gefe ta zauna saman wasu kujeru,sai da suka fara gaisawa ya tambayi lafiyarta,sun tab'a hira kad'an yace zai shigo anjima kad'an idan ya fito daga office,tace Allah ya kawo shi lafiya,har zai katse kiran tayi saurin cewa "Idan ka zo i'll tell u the story ko.!?" Tayi furucin kamar tana tambaya,yayi murmushi yace "Duk yadda kika ce" tayi ajiyar zuciya kad'an tace "sai ka zo toh" suka yi sallama,kiran yana katsewa ta tsaya tunanin yadda zata fuskance shi ta fad'a masa,da kyar ta lalubo idea sannan ta tashi ta shige class ganin tahowar Mr.Thomas Martin. Bayan sun fito daga lectures suna tare da Veronica Jackson,Maria Robles sai Sarah Alee da yake ita y'ar 9ja ce karatu ya kaita suke gaisawa sosai har mutunci ya had'a su suke fita tare,a wajenta ta san su Maria da Veronica kasancewar apartment d'aya suke zaune,suna tafiya za su cafeteria kiran Aatif ya shigo wayarta,ta d'an tsaya kad'an ta fito da wayar tayi answering,sallama tayi masa ya amsa yana fad'in "Ina gimbiyata za taje ne take tafiyar k'afa.!?" Tayi murmushi tace "Ba dai ka ganmu ba.!?" Yayi murmushi yace "A'ah ban ganku ba amma dai na gano ki ke d'aya" tayi murmushi tace "Ba ni kad'ai bace ai" yayi murmushi cike da zolaya yace "Idanuna ni kuma ke kad'ai suka nuna min" tayi murmushi bata ce komai ba,yace "Ina za kuje ne.!?" Tayi ajiyar zuciya tace "cafeteria" yace "Okay.! Bari mu tafi tare" tayi saurin katse shi tace "A'a mu had'u a can" yayi shiru kamar bai son hakan sai kuma yace "Ok.!",basu jima sosai da shiga cafeteria ba suka sa akawo musu drink da snacks,tana zaune tayi facing inda duk mai shigowa za ta gansa,ta hango shi yana shigo wajen,sanye yake da white trouser da white shirt mai V-neck,idanunsa a cikin sunglasses mai duhu,tunda ya shigo ta kalle shi haka nan taji gabanta ya fad'i,ta lumshe ido a hankali ta bud'e taci gaba da kallonsa har ya zauna d'an nesa da su kad'an,k'arshen had'uwa,kyau da tsari Aatif yana da su kuma ya kai namijin da ko wace mace za tayi fatan samunsa,tsarin rayuwarsa da komai nasa cikin nutsuwa yake yinsa and dai² iyawarsa yana bawa duk wanda suke tare girma da muhimmanci,fari ne shi sosai dan ya fi Nuraz haske,kana kallonsa zaka gane yana tattare da duk wani nau'in hutu da jin dad'i,sai dai fa idan ana batun kyau dole ne a fara ambaton Nuraz kafin ace shi,asalin mahaifinsa D'an Nigeria ne daya fito daga jihar Gombe,k'aramar hukumar Akko,cikin garin *KUMO* haka ma Mamansa itama y'ar Gombe ce amma ita ainihinta a *JEKA DA FARI* ta taso,,kiranta yayi duk da ya ganta bata d'auka ba ta nemi excuse wajen su Sarah ta nufi inda yake,tun kafin ta k'araso ya zare glasses d'in idonsa yana sakar mata murmushi,ta sake yi masa sallama ya amsa,ta zauna tana gaishe shi,cikin sakin fuska ya amsa mata yana tambayarta lectures,shiru suka yi na wani lokaci kafin yasa a kawo musu drinks,ta kalleshi tace "Bana shan komai fa",ya kalleta zai yi magana tace "Ai mun sha tare da su Sarah" ya tab'e baki kad'an bai kulata ba yasa waiter ya kawo,ya tafi kawowa tayi shiru tana tunani,ya d'an buga table d'in kad'an,tayi saurin kallonsa yace "Yaya ne.!?" Ta girgiza masa kai tace "Nothing" yace "Allah ya sa" tayi saurin kallonsa saboda kalmar daya fad'a sai taji kamar Nuraz ne a gurin,tayi shiru ta sunkuyar da kai ya katse mata tunani "Ehmn.! Wane labari ne kike son fad'a min.!?" Ta d'ago da sauri tana had'iyan wasu irin terrified saliva's,a hankali tayi blinking idanunta tace "My story" ya gyara zama yana murmushi yace "Wawhh.!" Tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya yace "Kin yi shiru,and u know am eager naji" ta d'anyi calming kanta sannan a hankali ta fara fad'a masa,tunda ta fara yake kallonta da wani irin yanayin tausayinta a idanunsa har ta gama,fuskarta da hawaye sosai ta d'ago idanunta for da first time tunda ta fara magana ta kalleshi,yadda ya zuba mata idanunsa ko k'iftawa babu yasa taji duk guiwoyinta sunyi sanyi,a hankali cikin mutuwar jiki ya ciro handkey ya mik'a mata,ta karb'a a hankali ta goge fuskarta,ta mayar masa ya karb'a yasa a aljihu,kusan mintuna biyar taji bai ce komai ba,ta kalleshi yayi shiru da alamun tunani yake fuska da damuwa,kamar za tayi magana Sarah ta k'araso ta musu sallama,Nusrah ta kalleta tana k'irk'iro murmushi,suka gaisa da Aatif ta kalli Nusrah tace "Baby we will go home" Nusrah tace "Ku jira mu wuce tare sai ku sauke ni a hanya" Sarah za ta amsa Aatif yace su tafi zai kaita gida da kansa,tayi saurin kallonsa za tayi magana taga bai kalleta ba,suka yi sallama da Sarah,tana zaune su Maria suka zo wucewa,suka yi waving d'in juna tana kallo suka fita daga cafeteria,a hankali tayi ajiyar zuciya,bayan tafiyarsu babu jimawa Aatif ya mik'e yace "Muje na kaiki gida" ta tashi bata ce komai ba har suka fito inda yayi parking,ya bud'e mata front seat ta shiga,ya rufe ya koma side d'in driver ya shiga,sai daya fara sa seatbelt sannan ya tada motar suka fara tafiya a hankali har suka fita daga skul d'in,a bakin apartment d'insu ya tsaya,da wani irin murya ya rarrasheta,after ya nuna mata shi ita yake so ba komai ba,suka yi sallama yace idan ya isa gida za suyi waya,ta masa fatan komawa lafiya,a hankali ya d'age glasses yayi reverse tana d'aga masa hannu,har ya kusa fita daga arean sannan ta juya zata shiga gida,ta fara tafiya ta hango motar Nuraz tana shigowa line bata tsaya ba ta shige ciki. Tun da ta dawo ta shige d'aki tayi zamanta a can tana jiran kiransa,har after maghreb bata sake fitowa ba,sai da Lolly tayi kiranta jin shirun ya yi yawa,ta fito rik'e da wayarta ta zauna kusa da ita,Lolly ta kalleta tace "Ke kam baby kina jin dad'in zama kiyi shiru,shi kenan shi mutum sai yayi ta zama cikin d'aki shi kad'ai" tayi murmushi bata ce komai ba,wayarta ta duba taga ko Aatif ya kirata,taga babu alamun miss call akai,ta bud'e network ta fad'a duniyar gizo²,nan ma ta duba babu sak'onsa,tayi shiru tana tunani,har to 11 tana zaune shiru duk bayan mintuna ta sake dubawa ko ya kira sai taga bai kira ba,zuciyarta ta damu sosai,Nuraz ya saci kallonta ya ganta a damuwa,yayi shiru yana tunanin yadda zai tambayeta ko ta samu sun yi maganar da shi.!?,idea ya zo masa ya d'ago yana niyyar tambayarta ta mik'e tana k'irk'iro hamman k'arya tace "Aunty good night" ta kalleta tace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180