Chapter 10
Chapter 10
tana yini,a take tace min A'a Baba ya hana ta yanzunma bai san ta zo ba,ina jin haka dabara ta zo min,nace to me zai hana ta dunga shiga gidan su k'awarta Maimunatu tana zama can idan ta dawo daga school,idan yaso sai tayi zamanta a nan har lokacin islamiyya yayi,which means ita da gida dai sai idan taji tana son yin bacci ta koma. Tace min "Ehh! To yaya wannan shawarar d'in dai ina ganin zaifi koh.?" Nace mata "haka nake tunani,kuma ina ganin ko Baba ma idan ya sani ba zaiyi fad'a ba" tace "haka nima nake gani,tunda dai ai ina kusa da gida,kuma duk abunda za'a fad'a masa ma ba lallai ne ya yarda ba ko.?",tun bayan tafiyarta sai ya zama daga wannan ranar idan sun dawo daga boko sai tayi wucewarta gidan su Maimunatu duk da ba makaranta d'aya suke yi ba amma zaman unguwa d'aya da had'uwarsu a islamiyya aji guda yasa suke k'awance sosai duk dama Hauwa ta kasance tana yin baya² da shiga sabgogin mutane,lokacin data fad'awa Maimunatu zata na zuwa gidansu,sosai Maimunatun tayi murna dan ita har ga Allah tana matuk'ar k'aunar Hauwa,itan ce dai da bata bada fuska ba yasa ko itama da kanta tayi baya² da ita tunda ta san ba'a k'awance dole,,cikin hukuncin ubangiji sanda Maimunatu ta fad'awa Hajiyar su hauwa zata dunga zuwa tana zama a nan,Hajiya ta amsa mata da k'arfin guiwarta bcos Maimunatu ita kad'ai ce y'arta mace,daga Yayanta sai ita su kad'ai suka mallaka,da taga tana murna itama tayi maraba da zancen,cikin tak'aitaccen lokaci rabin rayuwar Hauwa ya koma gidansu Maimunatu,idan ta fita tun safe ba ita zata koma gida ba sai dare lokacin kwanciyarta bacci,da safe ta sake shiryawa ta tafi makarantar boko,k'arfe 3:00pm sun tafi islamiyya,su da samun zama sai misalin 6:00pm idan sun taso daga islamiyyar yamma,rayuwarta ta koma gaba d'aya ta koma gidan su Maimunatu,,bayan b'illowar wannan al'amari na rashin zama tsakanin y'an uwanmu,idanunsu da hankulansu sai ya sake dawowa kanta,aka fara kai tsaiguminta gurin Baba akan tana tafiya yawo ba'a ganin k'afarta sai dare,abincin gidanma bata ci,maganganu dai barkatai haka aka cakud'e su,wani abun ma k'irk'irarsa suka yi suka fad'a,tun Baba bai fara tanka musu ba,sharrin yau da gobe ya janyo har ya fara tuhumar inda take zuwa tayi dare,a karon farko lokacin da ta sanar masa gidan Alhaji zakar labbo take zama,ta kawo masa dalilinta na yin hakan,ya gamsu kuma tun daga nan bai sake d'aga maganar ba,sai da aka sake soko mata sharrin k'arya tayi masa wancan lokacin,idan ta fita ba gidan Alhaji zakar d'in take zuwa ba,tana dai fakewa ne da can d'in a matsayin garkuwa,amma a zahiri yawon ta take tafiya,kwararo² babu inda ba'a santa ba yanzun saboda gantali,,ranar da aka kawowa Baba wannan maganar saboda zugashi da aka yi ya fusata sosai,maganar tayi masa zafi da yawa,ba tare da yayi bincike ya tabbatar da gaskiya ba yayi duka wa Hauwa,bayan nan ya yanka mata warnings masu tab'a zuciya akan ko da wasa ya sake ganin k'afarta a waje sai ya karairaya yasa an hura wuta da su,,a wannan ranar Hauwa tayi kuka sau babu adadi har taji tamkar hawayen idanunta sun k'are,yanayin maraici,damuwa da kad'aici ya sake mamayeta,cos a wannan lokacin bata da wani da zata sanarwa taji sanyi,ni d'in da muke sharing damuwarmu ban jima da zuwa ba,ita kuma Baba ya ce ko da wasa yaga k'afafunta waje sai ya sab'a mata,dan haka ta rasa mafita,a haka ta ci gaba da daurewa ta zauna cikin habaici da gori,makarantar da zata d'auke mata kewa itama ya hana zuwanta saboda a baya na fada maka Baba yana da halin yarda da abunda za'a fad'a masa,and baya damuwa da binciken gaskiya,kullum tana zaune gida ga damuwa ga kad'aici sai cin ranta suke,a gefe guda ga takurawar y'an gidanmu,,duka da yake ba shekaru gareta ba sai ta kasa yin wayon ko wani ne ta fad'awa yazo ya sanarmin halin da take ciki,,bayan kwana biyu da faruwar al'amarin Hajiyar su Maimunatu ta kula da rashin zuwanta tasa Maimunatun ta shiga ta duba ko lafiya bata ganinta cikin kwanakin.? Bayan zuwan tan suka d'an keb'e a d'aki duk dama an samu su ido,a hakan tayi iya kar k'ok'arinta cikin bada sallahun azo a fad'a min halin da take ciki ko Allah zaisa na rok'i Baba ya kyaleta taci gaba da zuwa makarantar,ta kwashe duk abunda yake damunta ta zayyanawa Maimunatu,tana kuka Maimunatun na taya ta har ta gama bata labarin abunda ya faru,Maimunatu tayi mata alk'awarin in sha Allah zata yi duk k'ok'arin da zata iya ta zo ta sanar min,Hauwa tayi mata godiya suka fito tare,da ta rakota bakin k'ofa suka sake tsayawa a nan suna ci gaba da y'an maganganunsu,kafin suyi sallama aka samu wani cikin y'an gidanmu ya kaiwa baba gulmar ga Hauwa can ta fita,babu b'ata lokaci Baba ya zo ya iske su zaure suna magana,nan d'in ma bai tsaya bin ba'asi ba ya korata gida bayan ya sauke mata kyawawan rankwashi masu shiga jiki,Maimunatu na kallon yadda take kuka,ta fice tayi gidansu da yanayin damuwa,,bayan komawarta gida bata iya fad'awa kowa ba har Hajiya data aikata,kuma ko da ta dawo ta tambayeta ce mata tayi tana lafiya daga haka bata sake cewa komai ba,,yanayin rayuwar gidansu Maimunatu rayuwa ce da suke yinta a sauk'ak'e,yanayin mu'amalar su da zaman takewarsu sun kasance suna gudanar da rayuwar su tamkar abokai tsakanin iyayen da y'ay'an,idan suna tattare da damuwa iyayen suna jansu a jiki su ji damuwarsu,itama Hajiya mahaifiyar sun a lokacin data kula da yanayin da Maimunatun ta shiga cikin kwanakin,haka ta sata gaba da tambayar lafiya take ganinta cikin damuwa.? Tana ta tambayarta da damuwa a fuskarta,tana lallab'ata saboda tana so ta sake sosai sannan taji mene ne ya kawo sauyin da aka samu,zuwa lokacin kasancewar damuwa tayi mata yawa sai bata sake b'oyewa mahaifiyartan ba ta zayyana mata komai da yake faruwa da Hauwa,,Hajiya ta shiga damuwa ta rarrashi Maimunatu sai da ta kwantar mata da hankali,and ta bata albishir idan Alhaji ya dawo zata san yadda tayi aka nemawa Hauwa'r sassauci,cos tana ganin lallai rayuwarta a cikin gidan akwai hatsari,sannan su da suka sani baya daga cikin hak'k'in mak'otaka kana ganin b'arna tana faruwa ka rufe baki ka zuba ido,dole tana bukatar inda zata zauna ba tare da tsangwama ko takurawa ba,ya dace ace itama ta zauna ne kamar ko wane d'a da yake k'ark'ashin iyayensa cikin y'anci,,sun gama maganar a ranan bayan Abba'nsu ya dawo tayi masa bayanin abunda ta ji daga bakin Maimunatun,shi kansa yayi mamaki sosai ace irin haka tana faruwa,abunda ya sanarwa Hajiya shi ne bai san yaya zai yi ya iya taimakawa ba,Hajiya ta kawo shawaran ya nemi mahaifin Hauwa suyi magana,idan ya fahimce shi,shi kenan ta san zai sassautawa yarinyar kuma rayuwarta zata samu salama,kwanaki biyu tsakani Alhaji zakar ya samu Babanmu a k'ofar gida,bayan sun gaisa cikin mutunci kamar yadda aka saba Abba'nsu Maimunatu yana kallon Baba yace "Malam Baba! Gurinka na zo,wata y'ar magana nake so muyi da kai,yau kwana biyu kenan ina sa rai da ganinka Allah bai nufa zamu had'u ba sai yanzun,ina fatan ba zaka damu da abunda zaka ji daga gare ni ba.." Baba yana kallonsa da mamaki,murmushi kwance saman fuskarsa yace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180