Skip to content

Chapter 142

Chapter 142

Dan Mace Book One Complete Hausa Novel 1,277 words 0 views Progress saved
Download Book

kawai,idan har akwai wata mahaifiyar a bayan wacce ta kawo ni izuwa wannan duniyar tabbas zai kasance ita ce,tarbiyyana da komai itace,idan na yi kuka ba ta samun nutsuwa har sai ta ga na yi dariya,idan ina farin ciki tana yin sama da nawa,for nothing other than ban yi kuka ba,itan y'ar baiwa ce kuma abun alfahari a gurin kowane ahali,tabbas da ace ana iya tambayar mutum lokacin da za'a raba shi da wanda yake so,a lokacin da mutuwa ta kusanci d'aya ko a bashi damar musanyawa da wani abu,hak'ik'a da na rok'i a barmin ita,na musanyata da sauran dangina,duk da mun kasance bamu tashi mun san dangin mahaifiyarmu ba a kullum suna nan a cikin zuk'atanmu,muna marmari da begen ganinsu ko da sau d'aya ne a rayuwa kafin mutuwa ta riske mu ko su d'in,sai dai har zuwa yanzun muna k'aunarsa ne kawai amma su d'in babu wanda ya damu da rayuwarmu bare su neme mu,ko su san halin da muke ciki,har yanzun bamu samu wani mutum d'aya wanda a tarihi za mu nuna muce ya fito daga dangin mahaifiyarmu ba,shin a wannan zamanin da muka kasance muna rayuwa mu kad'ai idan bamu so juna ba waye za mu so? Dangin mu basu damu da mu ba,basu san inda muke ba,babu wanda yake kulawa da mu,suna nan a raye ko sun mutu bamu sani ba,amma kasancewata tare da ita yasa a kullum na kasance ina yiwa Allah godiya tare da jin cewa ban rasa ahali ba,ba don komai ba sai saboda itan ta kasance d'aya daga cikin ahalina,tabbas ina alfahari da samunta!" Hawaye su duka suka share saboda yadda maganarta ta tab'a musu zuciya,Annie kuwa gaba d'aya ta kasa samun bakin magana banda hawaye babu abunda take sharewa,Lolly tayi murmushi tace "Saboda haka nake jin idan na kira ta da sunan Mahaifiya ban yi ba dai² ba.." Sun jima sosai a gidan yayin da duka hirar ta su ya kasance kalmomin yabo ga Annie da labarin rashin sanin inda ahalin mahaifiyarsu suke,a nan itama Nusrah zuciyarta ta cika taf da begen nata ahalin mahaifiyar har ta sake k'udurcewa a ranta lallai za ta sake yiwa Abbah magana ko da ace ba zai kaita ba lallai tana buk'atar ya ba ta address,ita da kanta sau ta neme su,wajen misalin k'arfe 9:00pm suna kan yin hiran Nuraz ya kira ta,tana d'auka bayan ta yi sallama,maganarsa a low tone yace "Madam kin manta da ni gaba d'ayan" tayi murmushi da sauri ta tashi ta haura sama,tana cewa "ta yaya zan mantawa da rayuwata? Idan na manta da kai ashe zan manta da kaina" yayi murmushi yace "kawai kince haka ne Madam,but na san hidima yasa an manta da ni,tunda ga shi daga zuwa rakiya ank'i a dawo" tana kwanciya a saman bed d'inta na gidan tace "No! Ba haka bane fa,kawai dai babu dad'i mu taho mu barta ita kad'ai ne,su Abbah muke jira har yanzun su zo,uhn! Sai nake jin ma kamar na kwana a nan" yayi murmushi yana cewa "to ko za ki gwada?" Tana dariya tace "Idan ka fad'a ba zan k'i ba" ya jinjina kai yace "Wai sai yaushe za ku taho?" Tace "Muna jiran su Abbah su zo" ya tab'e baki yana adjusting kwanciyarsa yace "Ni dai a dawo da wuri a san yadda za'ayi da ni" murmushi tayi muryarta a low tone tace "Me zan yi?" Yace "Ohooo! Kin fi kowa sani" ta shagwab'e tace "well,kawai ka zo mu tafi" yace "Ke kina wasa ko? A hakan zan wani biyo ki? Ko so kike na yi miki ciki a gabansu?" Kyalkyalewa tayi da dariya tana rufe baki tace "Allah yasa ban ji abunda kace ba" shi kansa sai da ta fad'i hakan ya tuna me yace,yayi dariya yace "idan kuma kina so nazo shi kenan dama ai muna da d'aki a nan right?" Ta kad'a kai tace "Ehh muna da shi" yace "Shi kenan ga ni nan,yau a nan za mu kwana",tayi sauri ta katse shi "wai da gaske kake yi?" Yayi dariya yace "absolutely sure" tace "Ka rufa min asiri kayi zamanka,yanzun za mu dawo" cikin zolaya yace "A'aahh! Dama ai asirinka a rufe yake" Tace "Pleasee!" Tana shagwab'ewa,da kyar yace mata ya yarda but tayi sauri,idan ba haka ba zai biyo sahunta,ta amsa tana dariya,tana gama wayar ta fito tana murmushi ta jiyo maganar Father In-law d'inta yana tsokanar Lolly,tayi dariya a fili tace "hali zanen dutse!" Ta sauko k'asa lokacin ta tarar da su har sun mik'e za su tafi,ta kalli lokaci taga 10pm yayi,here tayi realizing sun b'ata almost one hour suna magana,a gurguje taje ta d'auki kayanta suka yiwa su Annie fatan alkhairi had'e da sallama,kamar kada su tafi haka suka dunga ji sai da Rafeek yayi da gaske yasa su gaba yana zolayarsu sannan suka fita suna waiwayen Annie kamar wanda ba za su sake had'uwa ba,a mota suna tafiya kasancewar Lolly ce a front seat kusa da Yallab'ai dake jin tuk'i da kansa,Nusrah ta zauna kusa da Bareerah a back seat,da yake mota d'aya suka zo da shi babu security,Rafeek sai tsokanar Lollyn yake yi ganin tunda suka taho tayi shiru ta kasa cewa komai,fuskarta duk ta nuna damuwa,lokacin kuyinas their car parked tun da bikin ya matso yadda take shige da fice ya sake mata suna yake kiranta da *KIN FI AMARYA*,duk lokacin da yaji tsokana da hakan yake kiranta,basu yi nisa ba ta biye masa lamari ya canja salo,kunyar tafiyar nasu tare yasa gaba d'aya Nusrah ta kasa motsawa tana jin kamar ta shige cikin seat d'in,har suka iso gida tunda ta rufe idanunta sai da taji sunyi parking sannan ta bud'esu a hankali ta kalli harabar gidan,as their car parked guards suka bud'e ta fito da sauri cikin jin kunya,duk gaisuwar da suke yi mata bata tsaya amsawa ba ta shige ciki da sauri,tana shigowa bata jita ba direct ta nufi bedroom d'in da suka sauka,a nan ta tarar da Nuraz kwance daga shi sai nickers yana waya,tana shigowa yayi mata alamar barka da zuwa,ta kalleshi tana yin murmushi da sauri ta ajiye jakarta ta wuce bathroom,lokacin da ta fito ya gama wayar yana dai kwance har lokacin,yana ganin ta fito ya sakko daga saman bed d'in yana yi mata wani irin kallon dake narkar mata da zuciya,tayi baya a hankali tana sakin murmushi,yace "ina za ki je kuma?" Ta kad'a masa kai,abunda ya faru a mota ya dawo mata a rai ita kad'ai ta kyalkyale da dariya,ya rik'o ta yana cewa "What are u laughing?" She nodded again tana b'oye d'uriyarta,ya rik'o waist d'inta yana cusa kansa tsakanin neck d'inta yace "Ba ni labarin naji" Tayi ajiyar zuciya tana sake yin murmushi tace "nothing" yace "anya zan yarda babu komai?" Tace "why not?" Because da kunya ta iya fad'a masa abunda ta gani,daga nan ya d'aga ta yace "ok! Muje a ba ni kulawa" tayi dariya tana kai hannunta saman beard d'insa. ***** Tun da suka bar gidan Annie take zaune a gurin tak'i yarda ta tashi,Abbah dake shigowa lokacin ya yi musu rakiya bayan ya yi addu'o'in neman tsari da kariya ya kulle k'ofofin gidan duka,ya dawo inda take fuskarsa d'auke da murmushi mai tattare da nutsuwa,yana fara tahowa inda Annien take ta sake

Table of Contents

Chapters

180 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180