Chapter 19
Chapter 19
tafiya yasa Maimunatu bayan ta goge hawaye ta juya ta kalli maidservant d'insu tace "ina ganin da kunje gida kafin mu san abunda ake ciki,mu zamu zauna a nan muga yadda hali zai yi" da girmamawa suka amsa,mata ne su biyu y'an manya sai driver'nsu suka yi musu sallama da addu'ar neman sauk'i sannan suka d'auki hanyar komawa gida,hospital ya rage daga Hajiya sai Maimunatu dake ta addu'ar Allah ya tashi kafad'un Hauwa,suna ta zaune a ward d'in a bakin theatre room sun zuba idanunsu akan entrance jira suke suga an fito da ita,kusan awanni biyu da mintuna suka sake zuwa suka wuce har lokacin ba'a fito da ita ba,Hajiya ta kasa hak'uri ta mik'e tana zarya hankalinta a tashe,fitowar Dr Fahad yana cire mask daga bakinsa yana matsowa inda Hajiya take yasa taji hankalinta ya sake tashi,ajiyar zuciya yayi yace "Alhamdulillah! Hajiya y'arki da jikanki suna lafiya,but due to condition na yadda haihuwar yazo mata it seems nak'udan ma na dole ne akasa tayi,kwanakin EDD d'inta sun nuna sai first of next month and yanzun muna farkon month,baby'n ku ya sha wahala sosai,ya zo jikinsa babu wadataccen k'wari ina ganin kamar zamu rik'e su na wani lokaci duk da itama a halin da ake ciki a yanzun zata iya kaiwa kwanaki uku bata tashi ba,but idan an shirya su za'a wuce da shi baby unit cos yana bukatar asa shi cikin na'urar d'umama jarirai (incubator)." "Alhamdulillahillaziiy bii ni'imatihi tatimmus'salihaat..!" Fuskar Hajiya k'unshe da farin ciki ta d'aga hannu sama tana hawaye tana jera addu'o'i,kallon Dr Fahad tayi idanunta suna sake kawo hawaye tace "Na gode Dr da wannan albishir d'in,,yanzun kam na samu nutsuwa da jin wannan labarin.." Murmushi Dr Fahad yayi mata sannan yayi musu sallama ya wuce bayan ya sake fad'a musu za'a fito da ita yanzun babu jimawa,Maimunatu tana murmushi ta kira Abba'nsu ta fad'a masa zancen haihuwar,kafin wani lokaci ya k'araso hospital d'in shima jin abunda ya faru,yaji mamaki lokacin da yaga Hauwa kwance kamar gawa babu inda yake motsawa a jikinta,yana kallon Hajiya yace "Hajiya anya yarinyar nan da rai a jikinta kuwa.!?" Tayi murmushin k'arfin hali tace "Tana numfashi mana,ka kalleta sosai zaka gani.." K'ura mata idanu Alhaji zakar yayi a hankali yaga cikinta yana d'agawa kad'an²,jaririn da bai gani ba nan ma ya tambaya a tunaninsa ko ya zo babu rai ne tunda yasan duk wacce ta haihu ana ganin yaronta a kusa da ita,Hajiya tayi masa bayanin yadda duk suka yi da Dr Fahad,a nan ta sanar masa su kansu basu samu damar d'aukan yaron ba an nuna musu shi lokacin da za'a wuce da shi baby unit,ya tausaya musu sosai,yayi musu addu'ar neman sauk'i,ya jima sosai shima a hospital d'in kafin suka wuce gida da Maimunatu ya rage sai Hajiya kawai a hospital. Tsananin ciwo da wahalar da hauwa tasha a wannan lokacin fad'arsa zai zama kamar b'ata lokaci,to the extent lamarin ya zarta duk tunanin mai tunani,a hakan da take tun bayan da aka fito da ita daga theatre bata sake sanin inda kanta yake ba har aka cinye kwanaki uku tana kwance bata san ina yake mata ciwo ba,tana halin rayuwa ne ko mutuwa.? Or even ma ace tasan ta haihu duk bata san abunda yake faruwa ba,,Baby kuwa idan ya farka yayi kuka a cikin kwanakin,sai dai ayi amfani da electric breast pumper,cos hakan kad'ai shi ne solution da yaron zai samu cikakkiyar kulawar daya kamata ya samu ta wajen shayar da shi nonon mahaifiya,wanda shi ne sinadarin da zai k'ara masa kuzari da lafiya tunda yazo a wahale,,idan ya farka yayi kuka Hajiya ke zuwa ta rarrasheshi cikin nuna so da tausayawa ga wannan uwa da d'a da har lokacin basu ga juna ba,da yake a kullum tunda aka mata aikin tana under medication bayan alluran da ta sha kafin aikin da wanda akayi mata bayan anyi aikin,har a rana ta hud'u bata farko ba and babu wanda ya iya ganin kwayar idanunta,jikinta kam zuwa lokacin Alhamdulillah ya fara sauk'i duk da Hajiya ta damu sosai da rashin tashinta,a cewarta kwanaki uku Dr yace mata,tun tana tambayar Dr Fahad anya lafiya har yanzun bata farko ba,yana fad'a mata tayi hak'uri komai lafiya bai san dai a ina aka samo matsalar data hanata farkowar ba,but daga yanzun zuwa ko wane lokaci shi dai yasan zasu iya sa rai da tashinta,Hajiya dai taji zancen Dr Fahad ne amma k'asan zuciyarta damuwa ce sosai. Misalin karfe 3 da y'an mintuna na dare Hajiya tana tsaye saman abun sallah tana kai kukanta ga Ubangiji akan al'amuransu ta farka,idanunta suka fara motsawa a hankali kafin ta fara k'ok'arin bud'e su da kyar,yadda jikinta yake a d'aure bata fasa juya kanta tana kalle² ba,kud da babu yalwataccen haske yanayin k'amshin da d'akin ke fitarwa ya bata tabbacin ba a gida suke ba,tunanin abunda ya kawo su nan d'in ta fara,bayan ta gama y'an tunanukanta bata gano komai ba ta tab'e baki a hankali tana k'ok'arin tashi ta zauna,zafin da taji a gefen cikinta yasa ta sakin marayan ihu da ya kaiwa Hajiya sak'on ta farka,,muryarta dishi² take magana tana kira taji ko akwai mutum kusa da ita ya taimaka mata,Hajiya dake zaman tahiya da sauri ta k'arasa ta sallame sallah,ko addu'ah bata jira tayi ba ta taso da sauri tayi gurinta tana fad'in "Alhamdulillah.! Hauwa'u kin farka.!? Sannu kinji Allah yayi miki albarka,ya kara muku lafiya.!" Juya kanta tayi tana kallon shade d'in Hajiya dake tsaye kusa da ita tace "Hajiya zanje toilet.." Da sauri Hajiya ta amsa mata,ta taimaka mata suka je tayi fitsari ta wanke bakinta suka dawo,saman gadon ta sake zama bayanta jingine jikin pillow Hajiya ta fita ta dawo da nurse ta dubata ta fita,sannan ta had'a mata tea ta bata,tana gama sha muryarta har lokacin bata fita sosai tace "Hajiya me muke yi a hospital.!? Mene ne ya same ni a ciki na naga anyi min d'inki.!?" Hajiya tace "haihuwa kika yi,amma aiki suka yi miki." Idonta ta d'an bud'e sosai ba kamar da farko ba data tashi da suke a shanye tana kalle² a d'akin,ganin babu jaririnta da aka ce an ciro mata a hankali ta sauke idanunta hawaye suna gangarowa cikin muryar kuka tace "Hajiya ya mutu ko.!?" Ido Hajiya ta zaro tana kallonta tace "waye ya fad'a miki haka.!?" Tace "Hajiya ai to ban ganshi ba.!" D'an murmushi Hajiya tayi tana dafa hannunta tace "kada ki damu daughter yaron ki yana nan a raye,an sashi dai a na'ura ne saboda yazo da rashin kuzari,an jima kad'an idan Allah ya kaimu zaki je kiga abunki kinji.!? Ki kwantar da hankali." Sai lokacin taji wani irin nutsuwa ya saukar mata duk da nauyin da har lokacin take ji a k'irjinta a hankali ta zame jikinta ta amsa ta koma ta kwanta,bayan an fito a masjeed Hajiya ta kira wata nurse d'in ta sake zuwa ta duba jikin nata kafin Dr yazo,da safe Dr Fahad ya shigo duba jikin cos tun tun kafin ya k'araso hospital aka sanar da shi ta farka,yana zuwa ko zama baiyi ba a office ya shiga duba jikin,komai nata yana lafiya sai ciwon da ba'a rasa ba,hajiya ta tambaye shi ko za'a iya bata abinci kuma cos tunda ta farka tea kad'ai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180