Chapter 20
Chapter 20
ne a cikinta,Dr Fahad yace "Ehh!" Za'a iya bata but ya zama mai ruwa²,sai kuma fruits da za'a k'ara mata da su,saboda wajen yin bayan gida kada ta wahala su samu matsala a aikin nata,godiya Hajiya tayi masa sosai,Dr Fahad ya fita ya barsu tana lallab'a ta,,y'an gidanmu duk da bama zaman dad'i sun je duba Hauwa da yake tana cikin halin jinya sai bata sani ba,ni kuwa tunda aka yi mata aikin naso na zauna nayi jinyarta saboda duk duniya nice tata da ya kamata na zauna da ita bayan mahaifiyar mu,itan bata raye sai ni,ni d'in kuma dana nuna zan zauna da ita Hajiya tace kada na damu naje na kula da gida na ita zata zauna da Hauwa har zuwa lokacin da za'a basu sallama,a zahirin gaskiya mahaifan Rafeek mutanen kirki ne,sun yiwa Hauwa rik'on amana,ko dai ace su suka kawota duniya iya gatan da zasu bata kenan,bare ba su suka haifeta ba matsayin suruka kawai take a gurinsu,ranar da Hauwa ta farka ranar ne farkon da kaji d'umin mahaifiyar da tayi silar zuwanka duniya,lokacin shayar sa kai yayi ta tafi ganinka,yanayin d'akin da kake ciki da yadda yake fitar da hucin zafi saboda yawan na'urori yasa Hauwa ta shiga damuwa,bayan duk damuwar da ta shigo da shi the resemblance of Rafeek in ur face as if it were being torn apart ya sake jefa zuciyarta a damuwa a lokacin da aka ciroka daga incubator aka mik'a mata kai,zuciyarta a raunane take ta kallonka,tunda ta farka take tunanin dalilin da yasa take jin ciwuka sa yawa a ranan but bata iya gano dalilin zamanta a hospital ba,amma lokacin data d'auke ka a karo na farko da niyyar ta shayar da kai yadda al'amarin ya faru ya dawo mata kamar a lokacin ne komai yake occurring,ta daure ta shayar da kai tana kallonka cike da soyayya mai tattare da tausayi take zubar da hawaye,har ta gama shayar da kai bata iya tashi ta fita ba,kana jikinta kana bacci yayin da ita kuma tana ci gaba da kuka tuna yadda komai ya faru,kula da nurse d'in dake d'akin tayi da halin da take ciki yana neman sawa ka fad'o daga jikinta tayi saurin karb'e ka daga hannunta ta mayar cikin na'ura,bin nurse d'in tayi da ido,idanunta suka sauka kan takardar dake jikin na'urar mai d'auke da sunan *RAFEEK Son* a hankali ta kai hannu ta ciro hawaye na ci gaba da zuba a idonta,nurse d'in ta bita da kallon tausayi tana tambayarta ko lafiya,da kyar Hauwa tayi shiru tana kallon rutun har lokacin tace "Dan Allah y'ar uwa zaki iya min wani taimako.!?" Tace "fad'i kada ki damu in sha Allah idan ina da yadda zanyi na taimaka miki zanyi" Godiya Hauwa tayi mata tace "sunan nan nake so ki canja min" Nurse d'in tace "Ohh! An sawa baby'n suna.!?" Hauwa tace "Ehh! Ansa masa" murmushi nurse d'in tayi tace "Masha Allah,mene ne sunan.!?" Ba tare da Hauwa tayi shawara da kowa ba tace *"NURAAZ.!"* "Wow.! But dan Allah zan iya tambayar ki.!?" Nurse d'in ta fad'a tana kallon Hauwa da kanta ke k'asa tace "fad'i tambayarki",tace" Ma'anar sunan nan da kika fad'a dan Allah zaki fad'a min,na ji sunan yamin dad'i sosai",bata d'ago ba tace "Treasure of noor",tace "gaskiya na gode,but nace ba.. Za ki iya min kyautar baby'n ina sonsa sosai",murmushin k'arfin hali tayi ta d'ago kanta dake k'asa tace "Wannan shi ne farin cikina,amma tunda kina sonsa na baki" Murmushi nurse d'in tayi cikin jin dad'i tace "Kai amma gaskiya na gode sosai,kyautar baby sukutum,Allah dai ya k'ara muku lafiya Maman baby" Hauwa tace "amin'',tana zaune nurse d'in tana mata hira tunda ta kula tana cikin damuwa,har ta rubuta sunan tace mata "kinga sunan yayi.!?" Da kyar Hauwa ta sake d'aga kai ta kalli takardar,ganin *NURAZ RAFEEK* a jiki bar'o² wasu hawayen suka sake taho mata,da sauri ta girgiza kai tace "A'a" kasa fahimtar abunda take nufi nurse d'in tayi har ta matso kusa da ita tace "bai yiba kenan sunan.!?" Ta gyad'a mata kai "me za'a rubuta to.!?" Sai data share hawayenta tana sake kallon yaronta dake kwance cikin incubator jikinsa duk anyi connecting na'urori yana bacci tace *"NURAZ BIN HAUWA."* *#Posting abun so ga reader's,#Comments abincin writer's,mu daku kamar k'waryar sama dana k'asa ne,idan akwai d'aya babu d'aya al'amarin baya tafiya dai²,it's better ace mun faranta ran wad'anda suke k'aunar mu fisabilillah.!* #Share. #Real Smasher. 💠💠💠💠💠 *©®2020.* *'DAN MACE..* (Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥 *WATTPAD:REAL-SMASHER898.* https://my.w.tt/29u2S26SG2 Pᴀɢᴇ 8. #Hᴜᴍɪʟɪᴀᴛɪɴɢ Kallonta nurse d'in ta dunga yi kamar taga bak'uwar halitta,can da taga ba zata iya shiru ba ta janyo kujera ta zauna tana kallon Hauwa tace "Dan Allah kiyi hak'uri y'ar uwa idan har maganata zata sa kiji babu dad'i" da kai Hauwa ta amsa mata saboda kukan da take har a lokacin yak'i bari tayi magana,nurse d'in tace "Idan babu damuwa can we be a sister's so that sai muyi maganar a matsayin y'an uwa ba mai kula da yaro ba.!?" Hauwa ta sake kad'a mata kai,godiya tayi mata sannan tace "dan Allah mene ne dalilin da yasa kika ce asa masa sunanki al'halin na san yana da mahaifi.!?" Sai da tayi k'ok'arin tsayar da sababbin hawayen dake sake taho mata sannan tayiwa nurse d'in tak'aitaccen bayani akan matsalolin da suka samu wanda sune silar da suka janyo musu fad'awa mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki,da ta samu ta d'an fad'awa nurse d'in,wacce lokaci d'aya taji har zuciyarta ta aminta da ita,wani irin kuka take tunda ta samu ta fitar da maganar daga ranta,burinta kenan a lokacin yadda take ciki damuwa ta samu wanda zata fitarwa da maganar ko zata huta da rad'ad'in dake addabarta,tausayin Hauwa da baby yasa nurse bata gama jin labarinsu ba sai da tayi musu hawaye,tana kallon Hauwa bayan sun gama maganar tace "kada ki damu yar uwata,in sha Allah komai mai wucewa ne,,da yardar Allah lokaci zai zo da Rafeek zai neme ku duka,a lokacin zaiji kunyar wulak'anta kyautar da Allah yayi masa,in Allah ya yarda sai Yaron da nuna baya k'auna ya zame masa jigon da bazai tab'a samun kamarsa ba a rayuwa,,fatan da zan masa shi ne Allah ya nuna masa hanyar gaskiya komai tsayin lokaci..",sun jima sosai nurse d'in tana mata hira saboda tana son rage mata damuwa,da Hauwa zata tafi nurse d'in ta fad'a mata sunanta *AAEDAA* Hauwa ta mata sallama ta koma room d'in da take,da yake duka a ward d'aya suke,tana shiga d'akin su Hajiya suna zaune tun fitarta suna hira da Maimunatu,tayi sallama suka amsa ta wuce saman gado ta kwanta tayi shiru bata sake magana da kowa ba,,bayan wani lokaci Hajiya taje ganin Yaro ta tarar da abunda Hauwa tayi,tazo tana mata fad'an me yasa zata yi haka,al'halin kowa yasan Yaro nasu ne ita da Rafeek.? Babu kunya Hauwa ta fashe da kuka but ta kasa magana,Hajiya jikinta yayi sanyi ta matso ta rarrasheta,Hauwa tayi shiru cikin sanyi da lallami Hajiya ta tambayeta ko me yasa tayi hakan.? Bata b'oye ba ta sanar da Hajiya kaf abunda ya faru a ranar da incidence d'in ya faru,Hajiya taji bak'in cikin abunda ya faru musamman sakin da Rafeek yayi,amma da yake babu yadda za tayi tunda ya riga ya yanke hukunci tace "ai shi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180