Skip to content

Chapter 37

Chapter 37

Dan Mace Book One Complete Hausa Novel 1,271 words 0 views Progress saved
Download Book

mu tafi.." Malam ya dakata yace "zaku fita.!?" Suka ce "Ehh.! Za mu fita" Yace "maza ku fita,ta ina za ku tafi.!?" A gaggauce suka ce "Ta k'afa" Ya girgiza kai yace "Ban amince ba" Suka ce "ta baki" nan ma yace "A'ah.! ku dai zab'i wani gurin" Suka ce "To to ta hanci" Ya jinjina kai yace "Toh.! Kuyi min alk'awari idan kun tafi ba zaku sake dawowa jikinta ba" Suka yi shiru basu amsa ba,yace "ko na ci gaba da karatu ne.!?" Suka ce "A'ah.! Za mu tafi." Yace "Toh kuyi al-k'awarin ba zaku sake dawowa jikinta ba" Suka ce "mun yi.." Yace "idan kuka sake kuka dawo,aka sake kawomin ku nan zan k'ona ku,kun amince.!?" Suka amsa sun amince,yace "to ku yi bankwana sannan ku yi gaggawar fita" haka suka yi yadda yace ta shiga jera atishawa,daga cikin gida malam yasa aka kawo masa wuta a kasko,ana kawowa ya dunga banka mata turaruka da ruwan addu'ah,ba'a jima ba ta shiga ware idanunta Malam yana kallonta yace "Yaya sunan ki.!?" Ta juya ta kalle shi ta kalli su Annie dake zaune da manyan idanunta,cikin muryarta mai sanyi tace "Ina ne nan.!? Waye ya kawo ni nan.!? Ina Abbanah yake.!?" Malam ya sake kallonsu yayi murmushi yace "Alhamdulillah.! Alaa kulli halin.. Yanzun kam ta dawo" Ta sake yin y'an dube² tace "Ina Binitta take.!?" Aka rasa wanda zai bata amsa,sai Malam da yace "yarinya mene ne sunanki.!?" Ta fashe da kuka a hankali tace "NUSRAH.!" Malam ya kalli su Annie dake gefe cike da al'ajabi yace "Alhamdulillah.!" Annie da Nuraz suka masa sannu da godiya,yayi murmushi ya had'a musu magungunan da za tayi amfani dasu da zasu sake taimaka mata,Annie tayi masa alkhairi sosai saboda ya fad'a musu ba'a biyansa sai dai mutum ya bada sadaka da abunda yayi niyya,suka sake yi masa godiya sannan Annie ta rik'o hannunta tace "Tashi mu tafi gida daughter.!" Ta d'ago ta kalli Annie tana share hawaye sannan ta mik'e a hankali jikinta a sanyaye suka yiwa Malamin sallama suka fito,a mota suka tarar da shi zaune yayi shiru yana tunani suka shiga suka zauna,Annie ta kalleshi kad'an taga fuskarsa da damuwa tace "Sannu habibiiy.!" Yayi ajiyar zuciya ya d'aga kansa ya kallo Nusrah dake baya zaune ta jingina kanta da seat tana hawaye,a hankali ya dunga driven cikin mutuwar jiki har suka k'araso gida,malam buba dake bakin get yayi musu barka da dawowa,suka k'arasa ciki yayi parking,Annie ta fito ta bud'e mata k'ofa,ta fito a hankali tana kallon gidan,ta rik'e hannunta suka wuce ciki,Nuraz ya biyo su da ledar magungunanta,a parlor ya tarar da su Annie tana amsa gaisuwar Bareerah,ya bawa Annie ledar yana sake kallonta har lokacin bata daina ajiyar zuciya ba,Annie tana masa sannu ya amsa ya wuce bedroom d'insa. Annie ta juyo ta kalleta a hankali tace "daughter muje kiyi wanka kiyi break.!" Ta d'ago a hankali ta kalli Annie hawaye yana sakko mata tace "Mama dan Allah ina ne nan.!? Ban san ku ba.!" Annie tayi ajiyar zuciya tace "Muje ciki zan fad'a miki" ta mik'e a hankali tana rik'e kanta da take jin yana mata ciwo suka nufi bedroom d'in Annie,ta had'a mata ruwa tayi wanka,sannan ta fito mata da wasu kayan tasa,ta kawo mata breakfast taci sannan Annie tace ta kwanta ta huta idan ta tashi za su yi maganar,,ta amsa jikinta yayi sanyi,bata jima sosai da kwanciya ba bacci ya d'auke ta. Har bayan asr prayer bata farka ba,sai da Annie taga lokacin sallah yayi nisa sannan tazo ta tasheta tace tayi sallah,ta amsa sannan ta wuce bathroom ta d'auro alwala ta dawo ta tada sallah,bayan ta idar Annie tace taje taci abinci yana dining,ta girgiza kai a hankali tace "Na k'oshi" Annie ta kalleta tace "A'ah daughter rabonki da abinci fa tun na safe" ta kalli Annie tace "Bana jin yunwa" Annie ta takurata da kyar taje parlor taci,bayan ta gama ta zauna shiru tana tunanin me tazo yi gidan nan.? Annie ta kirata suka koma bedroom,ta zaunar da ita bayan ta nutsu tayi mata bayanin duk abunda ya faru da dalilin zuwanta gidan,ta dunga kuka bayan taji labarin abunda ya faru da ita Annie ta rarrasheta har sai da tayi shiru,sake kwantar mata da hankali Annie tayi,ta mata alk'awarin zuwa gobe idan ta huta sai suje gidansu,,a tsorace ta kalli Annie tana girgiza kai tace "A'ah.!" Annie tace "me yasa.!?" Ta sake fashewa da kuka,Annie tana ta rarrashinta sai data saurara da kukan sannan ce "Tsoro nake ji" Annie tace "Ki kwantar da hankalin ki babu abunda zai faru in sha Allah" Ta girgiza kai tana cewa "Bana son zuwa" Annie taga hankalinta ya fara tashi tace tayi shiru to su zasu je ta fad'a mata address d'in gidan,tana share hawaye tace "Kada kuje kuma,ko kunje ba zasu yarda da abunda zaku fad'a ba" Annie ta kalleta tace "Saboda me ba zasu yarda ba.!?" Ta sake share hawayen da suka zubo tace "Bcos of my stepmother" Annie tana ta kallonta tace "Ur stepmother.!?" Ta girgiza kai tace "Duk abunda tace yayi shi yake yi,ba zai yarda ba shima" Annie tana jinjina kai data tuno maganar da aljanun nan suka yi da Malam sai tayi shiru tana tunani a ranta,zuwa wani lokaci ta d'ago ta kalli Nusrah tace "Bani dai address d'in gidan,idan munje basu yarda ba shi kenan mun fita hak'k'in ku duka" ta goge hawayenta ta fad'awa Annie address d'in. Suna gama maganar Annie tace ina ta ajiye ledar da ta bata d'azun,ta mik'e a hankali tana d'agowa suka had'a ido da shi yana tsaye daga bakin k'ofar bedroom d'in,ta sunkuyar da kanta ta wuce kamar wacce k'wai ya fashewa a ciki,ta d'auko ta dawo Annie tasa Bareerah ta kawo mata garwashi a kaskon turare tayi mata hayak'i. Washe gari da rana Annie suka shirya ita da Nuraz zasu je gidan su Nusrah,tunda taga suna shirin fita hawaye yake ta zubo mata,ta d'aga kanta a hankali ta kallesu,Annie tayi mata sallama suka fita,,gidan ba b'oyayye bane kamar yadda ta bada address d'in haka suka dunga bin kwatancen har suka tsaya bakin get d'in gidan,babban gida ne sosai na alfarma daga gani kasan masu gidan suna hutawa sosai,yayi parking a bakin get suka fita tare,Annie tana gaba yana binta suka yi knocking get man d'insu ya bud'e yana kallonsu ya gaishe ta,Annie ta wuce tana amsa gaisuwarsa suka nufi entrance d'in gidan,a bakin k'ofa suka tsaya suka danna doorbell,mintuna biyu suna ta tsaye a wajen sannan aka bud'e. Sanye take da bak'in skirt daya tsaya kasan guiwarta sai white long sleeve na mata,wuyanta da butterfly bak'i,kanta ya sha kitson attach,yanayin shigarta shi ya bayyana musu matsayinta na christian and maidservant,ya tab'e baki yana d'auke kai dan yadda ta tsaya ta kafe su da ido,Annie tayi mata murmushi kad'an kafin ta tambaye ta "Are they here!!?" Ta kalli Annie ta kalli Nuraz da fuskar rashin fahimta tace "who are u looking for.!?" Nuraz ya kalleta a kyankyame yayi siririn tsaki,duka suka kalleshi a tare,ya banka mata harara bai ce komai ba,Annie ta sake kallonta tace "the owners of the house.!" Gyad'a mata kai tayi ta basu hanya,suka shigo parlor'n,aljannar duniya komai na more rayuwa zai yi wahala ace babu shi cikin gidan,ta nuna musu

Table of Contents

Chapters

180 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180