Skip to content

Chapter 143

Chapter 143

Dan Mace Book One Complete Hausa Novel 1,273 words 0 views Progress saved
Download Book

sunkuyar da kanta k'asa tana yin duk addu'ar da yazo bakinta saboda yadda take ganin abubuwan suna faruwa kamar ba gaske ba,Abbah ya k'araso cikin rantsatstsen parlor'nsu da yaji wasu irin royals na musamman masu kama da anyi musu feshin gold,ya zauna yana fad'in "Rabbigfirliiy watuub alayya innaka antat'tawwabul gafuur",sun zauna shiru na wani lokaci kafin Abbah yayi gyaran murya,a hankali yana kallonta yayi ajiyar zuciya ya fara magana "Arhm! Ina son cewa wani abu,but i just don't know idan nace zan fad'i abunda yake raina yanzun maybe ko zan takura ki?" Annie dake tunanin yadda rayuwar ta nan gaba zai kasance tayi ajiyar zuciya a hankali ta d'ago tace "Babu komai" yayi murmushi yace "Na gode" shiru parlor'n yayi na wani lokaci kafin Abbah ya numfasa,a hankali ya fara da fad'in "Alal hak'ik'a even though na san dukan mu babu yaro,and then yanayin mu'amalar ki ya tabbatar kina da sani,ina da tabbacin ba za ki tab'a yin abunda yake ba dai² ba in Allah ya amince" sai da yayi shiru kafin ya d'ora da fad'in "A gaskiya na yi matuk'ar farin ciki,kuma ina yiwa Allah godiya da wannan baiwar da yayi min,though a bayan na yi aure sau biyu,na san kina da labari wani kuma kin san abunda ya faru,but duk dai ina son sake sanar da ke ne ba don komai ba sai domin ina tsammanin samun zaman lafiya,nutsuwa da kwanciyar hankali daga gare ki,a zamanin aure na farko bayan shekarun da muka d'auka tare da ita KHADIJAH,duk da Allah yayi mata rasuwa,alhamdulillah tun da muke zaune da KHADIJAH ban fuskanci wani matsala gareta ba har Allah ya karb'i rayuwarta,sai dai wacce na aura a karo na biyun a zaman da muka yi duk da shekarun ba su da yawa na fuskanci matsaloli masu tarin yawa,wanda har kullum na tuna ina jin bak'in cikin kasancewa da irin wannan matar,sai dai ita rayuwa duka kana yin naka tsarin ubangiji yana nasa,sannan rayuwar kanta tana tafiya ne bisa doro na k'addara,abunda Allah ya nufa shi yake kasancewa,wanda bai so ba kuma ba ya kasancewa,sai dai ina fatan zaman da zamu yi yanzun zai kasance zama na amana,duk abunda kika gani zan yi ba dai² ba za ki tallafeni ki yimin jagoranci zuwa kyakykyawan hanya,kamar yadda idan na ga za kiyi zan nuna miki hanyar da ya dace" Annie dake sauraron jawabin Abbah ta kad'a kai a hankali tace "In sha Allah ina fatan hakan,ina rok'on Allah ya ba ni ikon yi maka biyayya tare da sauke hak'k'ok'in da suka rataya a wuyana" Abbah yayi murmushin jin dad'i ya amsa da "Ameen",daga nan yayi mata jagoranci zuwa bedroom d'insu,here na basu guri kun san soyayyar manya yafi k'arfin idanuwan mu. *Asubah ta gari (A²)...* ***** Rayuwar gidan Annie ya kasance wani irin rayuwa ne mai cike da tsafta da girmama juna,kasancewar su duka ba yara bane,but tsarin zaman sun abun burgewa ne ga kowa,tun daga kan yanayin soyayya,kulawar da suke gwadawa juna idan ka shiga gidan za su sa kayi tunanin auren sun tun na saurayi da budurwa ne,yayin da a b'angaren Abbah ya kasance tun da ya samu Annie matsayin matar aure yake jin wani irin nutsuwar da bai tab'a samun irin ta ba a duka rayuwarsa ta baya,haka itama Annie a nata gefen sai take jin kamar da can ba aure tayi ba yanzun ne tayi shi a inda ya dace,even though mijin tan na baya da ya rasu yana sonta sosai but soyayyar Abbah gareta ya zame mata tamkar wani babban *KUNDIN* da bata tab'a bud'e shafin sa ba bare tayi karatu a cikinsa. Cikin sati biyu da su Lolly suka sake yi a Nigeria tare da su bayan sun huta gajiyar biki,a nan Nusrah ta yi tunanin yiwa Abbah maganar zuwa dangin Mamma'nta,saboda rabonta da su baza ta iya tunawa ba,lokacin da ta yiwa Abbah maganar yayi shiru bai ce komai ba,da ta takura masa yace ta bari idan sun samu lokaci zai kaita,tayi shiru tana tunani because an d'auki tsayin lokaci take cewa tana so ya kaita ko ya barta taje yana hanawa,a gefen Abbah kuwa duk wannan hanya² da yake mata ba don komai bane sai don tsoron abunda zai iya faruwa,kasancewar bai manta irin rabuwar da suka yi da dangin Khadijah ba a lokacin da ta rasu,k'aramin yak'in da aka yi akan sun nuna suna so ya basu Nusrah su tafi da ita duk da ba yarinya bace k'arama da za ace idan tayi wayo za'a dawo masa da ita,Abbah yace ba zai iya ba ita kad'ai yake da,suyi hak'uri su bar masa y'arsa,an kai ruwa rana sosai lokacin har daga baya dai aka rabu dutse a hannun riga,daga nan ne tunda suka yi fushi basu sake zuwa ba saboda mangaganu da akayi musayarsu,shima kuma Abba'n sai bai kaita ba saboda sun nuna basa buk'atarta ya rik'e y'arsa,suna cikin wannan rigimar da Abban ta dage akan lallai ita ko address d'in ya bata taje da kanta,cikin satin ayyuka suka tasowa Rafeek,dole yasa suka tattara har su Annie suka nufi UK,unlike su Hajiya da su tun a satin da aka yi biki suka koma,a cewar Rafeek ko da suka yi magana da Abbah yana tambayarsa me za suje yi Uk? Rafeek yace yana da kyau suje honeymoon ne,Abbah dai yayi dariya but a zahiri ya fahimci dalilin aminin nasa na yin hakan,kasancewar ba ya iya b'oye masa komai haka shima,ko da suka sauka a k'asar lokacin da aka zo d'aukansu a airport har suka zo gida babu wani maganar da suka ji daga garesa,sai da suka shigo cikin mansion,a nan idanunsu suka tarar da abun mamakin da basu tab'a zato ba,kasancewar sati uku kenan basa k'asar,sannan a saninsu apartment biyu ne a gidan daga nasu sai na Hajiya,yanzun kuma sai lsuka tarar da k'arin guda ma'ana apartment d'in sun koma uku,duka suka tsaya kallon Rafeek because sun san aikinsa ne,yayi murmushi yana kallonsu kamar yadda suke yi sai yak'i cewa komai,Lolly tace "Yallab'ai! Wannan ginin fa?" Ya kalli su Nuraz yana yin murmushi yace "Na yara na ne",ta kalleshi da mamaki tace "wane yaran na ka?" Murmushi ya sake yi yana wucewa cikin apartment d'in Hajiya yace "kin fi kowa sanin wane yara nake nufi" quickly ta biyo bayansa tana cewa "Please Yallab'ai ka yi min bayani!" He didn't stop yana ci gaba da tafiya yace "u will soon understand" Su kansu su Nusran da suke tsaye ganin tafiyarsu da abunda suka ji yana fad'a ya ba su mamaki,sai dai babu wanda yayi tunanin wani abu,duka suka biyo bayansu,kafin su k'arasa shigowa Hajiya ta taho tarbarsu,ganinsu duka sunaa shigowa yasa cike da farin ciki ta bud'e baki,duk sai ta rasa wanda za ta fara tarba a cikinsu saboda yanayin da suke ciki ya tabbatar mata suna cikin kwanciyar hankali. Tarba na musamman da ta shirya saboda ta san da zuwan sun ya k'ayatar da su,bayan sun anci an sha aka zauna hira a parlor'n tsohuwar,ana tsokanar juna da wasa da dariya abun gwanin burgewa,yanayin ranar ya fi komai yiwa Hajiya dad'i,cikin tsananin farin cikin yadda family'n suka had'e kai tayi murmushi tana sake yiwa Allah godiya bisa wannan ni'imar da yayi a garesu. Da dare a time d'in kowa yayi shirin bacci bayan sun gama

Table of Contents

Chapters

180 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180