Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Dan Mace Book One Complete Hausa Novel 1,271 words 0 views Progress saved
Download Book

d'aya tilo,bak'ar fata jinsinmu da ya fito daga Africa,,,ba kowa nake nufi ba face mahaifin da yayi silar zuwanka duniya wato *SUPERIOR."* A mamakance a kuma razane ya d'ago yake kallonta bayan mik'ewa tsaye zubur da yayi,,bakinsa da duk wata gab'ar dake jikinsa tana aiki banda kyarma babu abunda yake sakamakon abunda yaji ta ambata yace "Annie is he my Dad..!? Shi ya haifeni kike son cewa..??" Tace "K'warai wannan mutumin shi ne asalin mahaifinka." Wani murmushi ya saki mai ciwo yana kad'a kai alamun abunda yaji bazai tab'a faruwa ba yace "Impossible! Annie ace kamar wannan mutumin shi ne Daddy na,,kin san wane ne shi da kike dangatashi da ni..?? Abeg.! Annie stop this drama,mutumin fa da kike magana baya zama k'asar nan,shi da ahalinsa sun jima basa nan,idan ya shigo ma within k'ananun hours yake barinta,me zai had'a mu da shi.? And how zai zama mahaifina.? Annie! Ba sai kinyi haka ne zan fahimci asalina ba,yau idan kika ce min bani da mahaifi wollahi Annie i will accept my fate a duk yadda yazo,zanyi hak'uri cos haka ubangijina yaso na kasance,Annie even a bite wollahi ban tab'a tsammanin irin wannan furucin daga gare ki ba,but for the sake of Allah nake rok'on ki,ki rufa mana asiri dan girman Allah Annie mu zauna a matsayinmu please..! Na amince na yarda da k'addara,please and please ki bar maganar nan ma kawai ya wuce.. Na hak'ura da sanin ko ma waye mahaifin nawa.." Hannayensa ya had'e cikin rashin sanin abunda zai sake fad'a ya runtse idanunsa,Annie dake ta kallonsa da tausayi ganin bai yarda ba tace "Habibiiy..! Did i tell u such things a baya can..??" Yayi saurin girgiza kai alamun A'a,tace "why yanzun kake neman k'aryata ni..?" Idanu ya zaro yasa hannunsa d'aya ya dafe bakinsa d'ayan kuma ya d'ora shi akansa yace "Annie! Ta ina na isa nace kinyi k'arya.?" Had'e rai tayi tace "gashi yanzun mun fara." Da sauri ya rik'e ta yana marairaicewa yace "I'm really sorry Annie idan har abunda nayi yasa kinyi tunanin na k'aryata maganarki,ki gafarce ni wollahi bazan sake ba.." Duk sai ya koma abun tausayi cikin k'ank'anin lokaci jikinsa ya d'auki wani lalataccen rawar tsoro,a hankali tana d'auke kanta gefe tace "It's okay!" Kallonta yayi yana langab'ar da kai yace "kin hak'ura.?" Ta gyad'a masa kai kawai,shi dai Allah ya sani tun da yaji sunan mutumin da tunaninsa yake kawo masa ko a mafarki hanya bata isa ta had'o su ba bare a gaske ace suna da wata alak'a ya shiga tashin hankali,d'agowa yayi da kansa dake sunkuye a karo na sau babu adadi yana jinjina kalmar mahaifinsa ya kalleta fuskarsa har lokacin da alamun rashin yarda da abunda yaji,tambaya yake shirin watso mata kafin ya kai ga yin hakan tayi saurin tarar numfashinsa "Ina so ka saurare ni a yanzun,,cos na riga na san abunda kake shirin tambaya ta,tun kafin muzo wannan gab'ar na shirya domin sanar da kai wannan muhimmin sirrin,,dan haka idan kaji wani abu daya shige maka duhu bayan na gama kana iya tambayata,ni kuma zan sanar da kai asalin yadda aka yi hakan ya faru da yardar Allah.." Ajiyar zuciya yayi ba tare da yace komai ba yana ta kallonta,idanunsa,zuciya da jikinsa duk jinsu yake kamar sun daina motsawa sosai ga wani irin tsoron da yake jin yana taso masa a rai,Annie da ta kula da halin firgicin da ya shiga ta dafa kafad'arsa tana fad'in "Kada ka damu habibiiy,ko mai zai zama dai² da yardar Allah,,sannan ni a yanzun abu d'aya kawai nake da buk'ata daga gare ka,shi ne ina so kayi min *ALK'AWARI* bayan kaji labarinka daga gare ni,ina so ya zama ba zaka tab'a sawa ranka damuwa akan abunda ya riga ya wuce ba.." Kai ya girgiza mata a hankali sai dai bai ce mata komai ba,kamar mai tunani itama Annie tana kallonsa ta ci gaba da fad'in... "Abunda ya faru..!" *FLASHBACK...* *(The beginning of the story).* *"RAFEEK ZAKAR LABBO* shi ne cikakke kuma asalin sunan mahaifinka,wato *CHIEF ECONOMIST* kamar yadda kaji na ambata a farko ne,sai dai kamar yadda na sani ne kuma kaima ka sani a yanzun al'ummah gaba d'aya tafi kiransa da *SUPERIOR* kuma shima wannan sunan yake amsawa,wannan suna ne da zan iya ce maka ya samo shi ne tun bayan da d'aukakar sa ta bayyanar da shi a duniyar shahararru,,asalin iyayen Rafeek ba y'an garin Kano bane,zama da yanayin canjin gurin aiki irin na ma'aikatan force ya kawo iyayensa garin Kano,Allah ya had'a mu mak'otaka da su,tun kafin su haifeshi har zuwa bayan haihuwarsa muke zaune tare da su cikin unguwa d'aya,asalisu sun kasance Fulani ne su da suka fito daga jihar *YOLA*,,Mahaifin Rafeek Alhaji Zakar Allah yayi masa rufin asiri da dukiya dai² shi wanda duk wani bawa da yake neman rufin asiri a gurin ubangiji ya samu kamar wannan a iya cewa ya more,kasancewar iyayen Rafeek tun a wancan lokacin suna da arzik'in su dai² su,mahaifinsa Alhaji Zakar ya kasance mutumin k'warai daya rik'e muk'amai da dama a cikin hukumar su ta *CUSTOMS* kafin Allah ya kaishi matsayin *ASSISTANT COMPTROLLER* a b'angaren d'amarar tasu,daga nan ne kuma bai sake yin gaba ba saboda ajiye aiki da yayi (ma'ana yayi retire). Duk wanda ya san su yasan mutane ne su na gari masu mutunci da ake zaune da su lafiya,tun farkon zuwansu kafin a samu mahaifinka,babu wanda zai zo yau yace sun tab'a yin ko da musayar yawu,haka ko bayan haihuwar Rafeek zuwa tasowarsa babu abunda ya canja,,a d'abi'u irin na yarinta ko wane yaro zaka ga da irin abunda tunaninsa da ra'ayinsa yafi karkata akai,ko nace muradinsa da idan ya girma zai so ya zama,,a wancan zamanin lokacin da shekarun Rafeek suka yi dai² da wannan stage bayan tasowarsa cikin hukuncin ubangiji,ya kasance gwani wanda yake da burin ganin ya nemi na kansa a k'ok'arinsa na ya wadata kansa ta inda ko ya girma ba zaiyi kukan rashi ba,,sab'anin sauran yara sa'anninsa da zaka tarar dole sai sunje gida suna y'ar murya suke samun biyan buk'atunsu,,sau da yawa a wannan lokacin tun bashi da shi,da y'an kud'in makarantarsa da yake ragewa yake siyo y'an k'ananun kaya da basu fi karfin aljihunsa ba a shaguna yana siyarwa a k'ofar gidansu,yau da gobe aka ce a gurin ubangiji tafi k'arfin wasa,akan wannan hali da mahaifinka ya d'auka mutane suka fara yi masa kallon shirmen yarinta yasa shi yin hakan,yayin da shi a gare shi bil'hak'k'i ya d'auki al'amarinsa,lokaci² idan ya samu yan kud'ad'ensa ba tare da yayi shawara da kowa ba zai je ya siya yan abubuwan da suke da rangwamen kud'i,kama daga kan sweet,chewing gum,biscuit da sauransu,ba don komai ba sai dan ya tallafi kansa ta hanyar neman halal d'insa and ba tare kuma da ya jira anyi masa a gida ba,and ba dan ya rasa gata ko idan yace ayi masa a gida za'a gagara yi masa ba,sai dan yana so ne ace wata rana shima ya dogara da kansa,,,tun a farkon lokacin daya fara wannan sana'a a lokacin da jama'a suke kan yi masa dariya,sam bai d'auki hakan wani abu ba,ya maida hankali sosai wajen ci gaba da siya yana siyarwa,had'e da nunawa mutanen dake masa dariya,dariyarsu bai dame shi ba,duk da wasu a ciki sukan

Table of Contents

Chapters

180 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180