Skip to content

Chapter 11

Chapter 11

Dan Mace Book One Complete Hausa Novel 1,273 words 0 views Progress saved
Download Book

"Toh! Alhaji Allah yasa muji alkhairi" Alhaji zakar ya kalleshi da murmushi shima a fuskar sa yace "In sha Allah ma alkhairi ce." Gyara zama Baba yayi yace "Toh Alhaji ina saurarenka,wace irin magana ce wannan d'in.?" Sai da Alhaji zakar yayi ajiyar zuciya ya san tabbas maganar da zai yiwa Baba,idan har bai masa kyakykyawar fahimta ba zasu iya samun sab'ani,haka kuma idan yayi shiru yaci gaba da zuba ido yasan lallai rayuwar marainiyar zata sake shiga wani halin,to amma da yake yayi nufin aikin alkhairi ne har zuciyarsa shi yasa sai ya daure yace "Dama Malam baba magana ce nazo da ita nake son mu tattauna,Allah yasa zaka fahimce ni,dan ba akan komai nazo muyi magana da kai ba sai akan gidanka." Baba yana kallonsa yace "Akan gida na..?" Alhaji yace "K'warai kuwa,akan gidanka." Baba yana binsa da wani irin kallon mamaki da rashin yarda ya sake daurewa yace "Toh ina jinka.." Alhaji zakar yana kallon Baba ya fara zayyana masa duk abubuwan dake faruwa a gidansa,da mugun mamakin yadda akayi ya sani Baba yake ta kallonsa,har ya gama magana Baba bai ce masa komai ba,Alhaji zakar yayi shiru yana ta kallon baba yaji ko zai yi magana amma yaji shiru,dole tasa shi tambayar baba "Malam Baba baka ce komai ba..?" Baba dai yana kallonsa har lokacin da kyar ya bud'e baki cikin kaushin kalami yace "toh Alhaji me zance.?? Tunda Allah yasa munafukai sun fara sawa gidana ido,har sun fara yawo suna yamad'id'i da ni a gari,da tona asirin gidana.. Zance ya lalace tunda har al'amarin gida na ya shiga gari.." "A'a Malam Baba kada kace haka,wannan magana sam baka fahimci yadda take ba,,ni dai ka sanni kuma kasan ba mai shiga harkokin da ba'a sani bane,amma tunda kaga na tsayar da kai nayi maka magana kasan ba zai wuce na hango maka damuwa bane a cikin gidanka na sanar da kai. Toh amma tunda har Allah yasa magana ta batai maka ba,Allah ya huci zuciyarka kuma ya baka hak'uri idan har na b'ata maka rai.." Ajiyar zuciya Baba yayi yace "ai Alhaji wannan batun tunda kazo da shi na san bazai wuce tsaigumi aka kai maka ba,kuma kaima ga shi ka tabbatar min,amma tunda haka abun yake,kafin a fara zagina akan maganar yarinyar nan,dole ne tunda yake nine mahaifinta na zartar da hukuncina akanta ta yadda babu wanda zai sake zuwa min da magana makamanciyar wannan,,zan aurar da ita kowa sai ya huta,da ta d'auko min maganar da zata fi k'arfi na gara na zartar da hukuncin da zan kashe bakin mutane.." Alhaji yana kallon Baba da mamaki yace "Malam Baba aure kace.?" Baba yace "Haka nace",cikin muryar rarrashi Alhaji zakar yace "kada kayi haka malam Baba,yarinyar nan duka nawa take da zaka ce zaka aurar da ita.? Ko a k'auye yanzun tuni an waye an daina irin wannan auren,bare mu da muke cikin birni,,ya kamata kayi tunani dai kafin ka zartar da hukuncin da zai iya kaika ga yin dana sani a gaba." "Alhaji ina ganin wannan hukuncin shi ne dai²,tunda har Allah yasa ka fad'i sak'on da ya kawo ka,kana iya tafiya na gode.." Alhaji yaci gaba da kallon Baba da mamaki "Amma malam Baba ban tab'a tsammanin haka daga gareka ba,wannan al'amari idan har ka tsaya ka nazarce shi da kyau,na tabbata zaka gane gaskiyar da nake son ka fahimta." "Alhaji maganar fahimta ya k'are,tunda har ka fad'i sak'on daya kawo ka,yanzun naka ido ne,,abunda nake fad'a maka a yanzun shi ne batun auren Hauwa na gama yanke hukunci,in sha Allah cikin satin nan zan d'aura mata aure,da ma hak'k'i na ne na aurar da ita ga wanda yayi min,yadda nayi niyya haka zanyi aure babu fashi.." Cikin takaici Alhaji zakar yaci gaba da kallon Baba but bai sake ce masa komai ba ya mik'e da niyyar barin gurin tunda al'amarin yafi k'arfinsa,ya yiwa Baba sallama yana niyyar shiga gida,Baba dake zaune har lokacin yana kallonsa cikin d'aga murya kamar wanda aka bawa umarnin yin magana yace "Yawwa Alhaji ina da wata y'ar maganar nima." Waiwayowa Alhaji zakar yayi yana kallon Baba duk da yaji haushinsa amma haka nan daga inda yake tsaye yace "fad'i maganarka ina sauraronka." Shima Baba daga nan inda yake yace "Yawwa! Dama ina so ne na baka cigiya tunda har Allah yasa nace zan aurar da ita,ba tare da samun tsayyaye ba shi ne nake son shaida maka,ko da Allah zai sa ka samu wani mai rangwamen gata kamar ta da yake buk'atar auren,dan Allah ina rok'on alfarma ka sanar masa yazo gida na ina da matar da zan bashi sadaka.." Cike da takaici Alhaji zakar ya bi Baba da kallon sakarci ba tare da ya ce komai ba ya juya zai shiga gida,baba yaga yayi masa magana bai tanka ba hakan tasa shi sake cewa "Yawwa Alhaji,,nace tunda yake Allah yasa har kana ganin tayi k'arama da aure yanzun,kuma kai d'in kana da ma'aikata a gidanka,shin mai zai hana ko su ne ka nemawa d'aya daga cikinsu aurenta tunda kana tausayinta tayi k'arama da aure.. Ka ga dama jihadi kake son yi.. Shi ne sai naga zaifi kyau na sanar da kai,sadaki ma kad'ai idan ka biya ya wadatar a d'aura musu aure,daga nan sai ka ajiyeta a gidanka,kaci gaba da kulawa da ita ko itama ka bata aiki a gidan naka,tunda yake ni mahaifinta na yi ba dai² ba.." Maganar ta yiwa Alhaji zakar zafi,still bai tanka ba ya wuce gida ransa a b'ace har yaji nadamar samun Baba da maganar,shigarsa gida a cikin wannan yanayin suka yi maganar da Hajiya,yadda suka yi duka da baba ya sanar da ita tunda ita ta sashi shiga maganar tun farko,,Hajiya ta lallab'a ta kwantar masa hankali,followed by maganar ta akan me zai hana tunda har Allah yasa al'amarin ya zo da haka kuma Baba da kansa ya bashi damar neman auren yarinyar ga hadiman gidansa,su nunawa masa cewa maganar da yayi cikin izgili a shirye suke su tabbatar da cikarta..??,Alhaji ya zuba mata ido yana kallo cikin rashin fahimta but yayi k'ok'arin yin magana "Hajiya me kike son cewa..?" Tace "so nake ka amince da batun neman auren yarinyar." Yace "Hajiya wane irin batu kike yi haka.? Ni zan nemi auren k'aramar yarinya kamar wannan,sa'ar y'ata fa.?? Ita kike cewa na nemi aurenta..?? Yarinya y'ar shekara sha hud'u.? " Tace "Alhaji nifa ba kai nake nufi ba." Yace "to waye zan nemawa aurenta.? Kin san dai bani da ikon zartar da ko wane irin hukunci akan ma'aikatan gidan nan cos bani ke da su ba,mu kuma ba wani babban d'a namiji gare mu ba bayan Rafeek,idan munce shi,duka shekarunsa nawa suke.? Besides yanzun yake shekara ta biyu a jami'a." Hajiya tace "ni dai alhaji kawai kayi hak'uri da batun shekarunsa,wannan al'amari ne da ya kamata ace munyi iya kar k'ok'arin mu wajen ganin mun taimakawa marainiyar nan,ina tausayin rayuwar yarinyar nan har zuciya ta,kallonta nake kamar Maimunatu na,idan a yanzun da muke da dama bamu taimaka mata ba,mu yaya zamu yi a gaba..?? Kada fa ka manta taimakon maraya abune mai kyau,kamar yadda annabi (S.A.W) yace a hadisi:"Ni da mai taimakon maraya,zamu kasance kamar haka ✌🏻a gidan aljannah,sai ya raba tsakaninsu da wani abu,maleek (R.A) yayi nuni da

Table of Contents

Chapters

180 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180