Skip to content

Chapter 96

Chapter 96

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

wa Allah yayi maka shi, domin shine mai dukkan karfi.......)_ Tun Mummy na jiran Badariyya a daki, har ta koma leke ta window da kofa, karfe 11 agogon parlon ya buga, a tsorace ta sake kiran Badar karo na ba adadi, har lokacin wayar a kashe take, zama tayi akan kujera ta Shiga jero salati, "Ina Badariyya ta Shiga har wannan lokacin, ya ilahi kasa ba wani abun bane ya same ta, tagumi tayi tanata sambatu dan hankalinta Sam yaki kwanciya, Har karfe 1 na dare babu labarin Badar, sai a sannan ne ta fara kiraye kiraye waya tana kuka Dan gaba daya ta gama tsurewa, duk wanda ta kira wayarshi a kashe, wayar Daddy ce kadai ta shiga, shi kuma bai dauka ba saboda gajiya da yayi, yar da wayar tayi ta fashe da kuka tana dana sanin barin Badar ta fita, gaba daya idonta ya rufe burinta kawai a fasa auren Nadeeyah da Musaddiq, Sam bata hango matsala a fitar da Badar tayi ba, sai gurin hudu bacci barawo yayi gaba da ita, ana idar da sallar asuba Daddy ya kira ta saboda ganin misd calls dinta da yayi, firgigit... ta farka tana fadin Badariyya, "Hello Badariyya kina ina?, gyaran murya Daddy yayi yace "ina Badariyyar ta tafi? Wani irin kuka Mummy ta fashe dashi tace "Badariyya bata kwana a gida ba, na rasa inda ta tafi, na kira wayarta har naji ba dadi na kasa samunta, cikin halin ko in kula Daddy yace "kinsan duk inda take zata dawo, ki kwantar da hankalinki, ai ba yarinya bace, big girl ce.. na turo miki kudin kayan kitchen, zuwa anjima kuje ku siyo, bana son muyi abubuwa cikin kurarren lokaci, yana kaiwa nan ya kashe wayar, Ajiye wayar tayi ta cigaba da rero kuka, "da wani baki zata fada musu cewa tana da masaniyar inda Badar taje, wa zata fadama ya fahimceta har ya taimaketa, Goggo ce ta fado mata a rai tayi saurin kiranta, saida wayar ta kusa katsewa sannan ta daga dakyar, yanayin muryarsu daya ko wannensu cikin kunci yake, Mummy ce ta fara fada mata damuwarta, nan take Goggo tace "rabu da ita zata dawo da kafarta, kin manta haka uwarta ma tayi, kina zaune zata dawo, ke dai kije kisan yadda zakiyi wadannan matsiyatan kar su shigo cikin zuriarki, dan babu alkhairi a duk inda suka sa kafa.. da kalaman Goggo hankalin Mummy ya kwanta ta mike tayi wanka tayi sallah sannan ta zauna tana tunanin ta inda zata bullo, kawarta Hajiya Martai ce ta fado mata, nan ta kirata ta kora mata matsalolinta, minti talatin Hajiya Martai ta bata tace ta sake kiranta zata sa wani malami yayi bincike akai, ko minti daya bata kara akan minti talatin din ba ta kirata, a sanyaye Hajiya Martai tace "Hajiya zainab wannan auren babu abinda zai hana shi sai mutuwa, akwai rabo mai karfi a tsakani, kuma akwai wani babban al'amari da zai taso marar dadi wanda Allah ne kadai ya barwa kansa sani, saboda haka shawara ce zan baki, in dai ba so kikeyi ki mutu ayi ba, to ki kwantar da hankalinki ayi kina da rai, bayan an daura sai ki shigeta kuyi mata illa har su rabu, amma tabbas akwai aure a tsakaninsu, Ajiyar zuciya mummy tayi hade da share kwallar takaicin da ta ziraro mata tace "to Hajiya martai nagode kwarai, in shaa Allahu naji shawararki, kuma zanyi amfani dasu... shawarwari ta dinga bata marasa amfani na yadda zata kori Nadeeyah cikin kankanin lokaci, sunfi minti talatin suna waya sannan sukayi sallama, sai a lokacin Mummy taji wasai ta mike da karfinta ta shirya zuwa kasuwa...... Shirye shiryen biki sukeyi ta ko wani bangare, Mummy da ahalinta sun danne bakin nufinsu sunata kankajere suna hidima da jikinsu da kudinsu, kowa ya manta da lamarin Badariyya saboda Mummy tayi musu karyar ta tafi cotonou makaranta, amma a zuciyarta kullum sai tayi tunanin inda Badar take da har wannan lokacin bata ziyarci gida ba, in ta tuno kalaman Goggo sai ta kwantar da hankalinta ta cigaba da cigaba da zuba idon ganin dawowarta... Anni itace ta dauki nauyin su cincin da dublan da sauran tarkacen garar amare, ita kuwa Goggo ba baki dan mugun tsoron Anni yanzu Allah ya daura mata, ta kan ce "ina zata iya da wannan matsafiyar, saboda duk asirin da ta dunkulo sai dai ya koma mata ko ya wargaje, ita a ganinta tsafin Anni ne yafi nata, bata san dogaro da Allah yafi tsafi karfi ba.... Tun ana saura kwana uku daurin aure Anty Reemah da Papy suka iso, babu yadda basuyi da Hilal ya biyo su ba, yace sai daren daurin auren zai shigo, hakanan suka kyaleshi sukayi gaba abinsu... Duk yadda suka so suyi bidi'a Mummy ta hana a cewarta Daddy yace bayason komai sai daurin aure, kawayenta ma babu wanda ta gayyata sai makota na kusa da ita, Bikin ya kasance na yan family kawai sai kawayen su Anty Raliya da yan Gombe da yan maiduguri dangin Daddy... Ranar jumm'a ake kamun amare, a cikin gidan akayi decoration wanda ya kawatu da kore da kumbo, Blue kayan kanuri suka sa dukkansu, fuskar nan tasu ta dau kwalliya gwanin kyau da sha'awa, kawayen Husna da yan tsirarrun na Nadeeyah sunyi ankonsu wanda ya dace da kayan amaren, sai su Anty Reemah suma sunyi nasu lafaya mai kyau da tsadar gaske, babu abin da ke tashi a gidan sai kidan piano da wani kwararren mawaki keyi, kida ne taushi mai ratsa zuciya, Ruwaidah da Zainab ne kadai a cikin tsakiyar filin suna rawarsu ta yaran da basu da wata matsala a rayuwarsu, sai gefe yaran makota suma suna rayawa dan kar a barsu a baya, Muryar inna Surayya (M.C Surry k mata) ce ta karade gidan da barkwancinta, nan manya da yara suka hau dariyar labarin da take bayarwa, Hinad... Anty Reemah ta kwala kiranta da karfi.. da dan gudu ta karaso gurinta bayan ta amsa tace "Mum gani, wata leda ta mika mata tace "maza ki kaima Uncle links dinshi, nasan yana can bai gama shiryawa ba, cire dankwalin kanta tayi ta karbi links din ta wuce dakin Musaddiq... A zaune ta sameshi ya tasa kaya a gaba yana tsaki, ya rasa taka mai mai kayan da zaisa cikin sabbin kayan da ya dinka, gashi sai kiran wayar Nadeeyah yake taki dauka, rabonshi da ya sata a ido tun ranar da ya koma lagos, sai jiya da suka iso daga Gombe, shima daga nesa ya hango ta, gaba daya ta toshe duk wata kafar da zata hada da shi, a waya ma saidai in ya kira Hafeez sannan ne zata amsa, shima bawani maganar kirki, zata kashe... "Uncle baka shirya ba? tsaki ya sake yi yace "Hinad ban shirya ba, zo ki zabar min kaya, banason inyi shigar da zata banbanta da ta matata, "Ummm ta fadi tana dariya hade da janyo wata danyar blue shadda taji aikin dark blue, tace "wannan is okay uncle, tun dazu uncle Hafeez ya shirya kai kana zaune, plss hurry up, kayan ya kwasa yace "i hate Hilal, shi ya kamata yayi min wannan ya wani ki zuwa, "kunfi kusa ta fadi hade da ajiye links dinshi a kan kayan ta

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156