Skip to content

Chapter 146

Chapter 146

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

yace "Ina Adamou? Mikewa Papy da Daddy sukayi suka isa gurin cikin girmamawa, "Ranka ya dade, ba Adamu bane, wannan Hafeezu sunansa, "Eh na gane yanzu, ina Adamoun yake, nasan tunda naga gudan jininshi dole shima ya kasance a kusa.... Garammm.... gaban mutanen parlon ya faďi, Sai a lokacin yawancin su suka tuna cewa sunan buzu mai gadi marar asali da galihu *Adamu*, Daddy ne yayi saurin cewa "Kwarai Adamu shine mahaifin Hafeezu da Nadeeyah ne, Allah dai yasa lafiya, ya karashe cikin zullumi ko Adamun ya taba yi musu wani mummunan abu ne, "Lafiya kalau sai alheri, Shareefah ta faďi idonta cike da kwallar farin ciki, "Ina Yayana Adamou?? Dan Allah ku nuna min shi, ku nuna min shi ko zan samu salama a cikin zuciyata.... Kallon kallo aka fara yi a cikin parlon, Papy ne yayi karfin halin cewa Sarki ya zauna sai ayi maganar a nutse, Kamo hannun Hafeez yayi suka koma inda yake zaune, share kwallar da ta ziraro mishi yayi yace "Dan Allah ku kira min Adamou, ashe munada rabon sake ganin juna... Anya ba kuskure kukayi ba? Wannan buzu Adamu, mai gadi ne, bashi da wata alaka da sarauta, inajin kamanni ne kawai, kunsan babu yadda Allah bai iya yi cikin halittarshi... Baffa ne ke maganar cikin taka tsan tsan dan kar ya bata ran Sarkin... Murmushin takaici Shareefah tayi ta nuna Hafeez da hannu tace "In dai wannan jinin Mai gadin ne, to tabbas jinina ne, idan yayana yayi nisa dan Allah ko zan iya samun hotonshi saboda in tabbatar da zancenku in karyata kaina... Cikin azama Daddy ya tashi zai nufi sama, kafin ya karasa Hafeez ya dakatar dashi ya ciro wallet a aljihunshi, kananan hotunan iyayenshi ne suka bayyana, da sauri ya mika mata... *Pappa.....* Ta faďi cikin kuka dan fuskar mahaifinta ta gani a cikin ta dattijo Adamu, shi kuwa Hafeez fuskar Yareemah Adamou Sarki Tidjani ke gani a idonshi, Dan Allah ina yake, Ku faďa mana inda yake?? Sarki ya tambaya cikin ďaga murya... Da sauri fadawa suka shiga faďin Allah ya huci zuciyarka... Baya tare damu, dan uwanku ya rigamu gidan gaskiya, ya tafi inda duk zamu tafi komi daren dadewa, shin dama shi ďin dan gata ne kuka barshi cikin gararin rayuwa? Ya ilahi me muka maida *ZUMUNCINMU A YAU* ace yanzu sai in baka raye za'ayi Zumunci da kai, To Adamu yayi tafiyar da ganinshi yake da matukar wuya, Adamu yayi muku nisa, saidai 'ya'yanshi.... yadda Daddy yake maganar ya sanya Parlon yin shuru, sai tashin sheshshekar kuka.... Cikin matsanancin kuka Shareefah ta zaune a kan carpet tace "Yareemah shine Gata, kalmar Gata in aka zo kanshi an disa aya, Shine ďan Sarkin Agadez *Diya Muradun Abdallah Yallo* na farko, shine Yareeman Agadez.... Kaddararshi a nan take, kaddarar samun magaji a nan Nigeria take, hannayen Hafeez ta rike tana kuka sosai tace "Rubutun Allah baya goguwa, Allah bai nufeshi da zama Sarki ba wanda hakan shine muradin mahaifinmu da duk daukacin mutanen Agadez, lallai sarauta rigar ubangiji ce, ya baiwa mijina wanda yake ďan uwa ga mahaifinka, sannan ya hanamu haihuwa dan dama ya tanade ta ne domin ka.. Wallahi Allah dole ya zama abin tsoro da girmamawa cikin mu bayinsa, domin ya wuce duk yadda muke tsammani, ku duba kuga yadda ya maida dan sarki wanda ya kamata ya zama sarki bawa, mai gadi kaskantacce a gidan bayin da ya kamata su zasu bauta mishi, cikin kankanin lokaci ubangiji ke sauya alkalaminsa, ku dubi nisan Agadez da Nigeria, haka kudurar ubangiji ta ingizo shi nan da taimakon marasa imani da tsoron Allah, duk dan saboda me? saboda yasan akwai wanda ya tanadarwa aron rigar sarautarshi, Lallai zaren kaddara baki ne, ganinshi sai wanda ya halicci kaddarar kanta, haďuwar Taheer da Nadeeyah,, zuwan mu nan domin su biyun duk zaren ne ke janmu ba tare da mun ganshi ba, Allahu Ahad, Allahu Samad, buwayi gagara misali, mai dauke da rayukan da babu wanda yasan adadinsu sai shi kaďai... Naji dadi matuka da Allah bai dauki raina ba sai da naga gudan jinina, rungume Hafeez tayi ta yafito Nadeeyah ta haďesu tana kuka tace "Ina sauran 'yayana? Share hawayen farin ciki Papy yayi yace "ďaya ce ta rage, Zainab, tana can Cyprus tana karatu, ga wacce take rikonta can ya nuna Anty Reemah da hannu, Kiranta gabanta tayi itama ta rungumeta tana mata godiya haďe yin hamdala gurin ubangiji.... Na faďa muku, yanzu kun gasgata zancena? Yareemah Suhail ya faďi cike da kasaita, maida dubansu inda yake zaune shi da 'ya'yanshi sukayi, a harzuke Daddy ya mike yace "Kai ku tashi ku fice min a gida, mikewa Papy yayi ya dakatar dashi yace "Yau ranar farin ciki ce, ka bar shi alkhairin ne zai fitar dashi in shaa Allah..... Labarin irin gatan da Yareemah Adamou ya samu da kuruciyarshi suka shiga basu har kawo sanadiyyar barinshi gida... sannan Sarki ya faďa musu yadda suke da Adamoun ya kuma nuna Taheer yace "Wannan shine dan kanina, shima dan uwan Adamoun ne.... Kallon juna sukayi shi da Nadeeyah yayi murmushi haďe da kashe mata ido, da sauri ta kauda kanta cike da kunya, dadin da takeji a yau kamar an mata albishir da gidan aljanna... Ashe Taheer dan uwan Nadeeyah ne na jini, haba kaunar tayi yawa, Taheer baya taba likewa mace haka, ashe connection din mai karfi ne, Anty Saude ta faďi tana dariyar farin ciki.... Dariya akayi a parlon duk da zuciyar Daddy ta ďan sosu da jin maganar kauna daga bakin Anty Saude..... Baffa ne ya fara basu labarin irin wahalar da Adamun yasha da kuma haďuwarsu da Mamma Suwaiba har mutuwarsu... Cike da jin daďi hira ta barke a tsakaninsu... Har wannan lokacin su Daddy basu san da zaman junior ba dan basu ganshi ba..... Su Mummy bayin Allah suna can dai a rabe har lokacin, sunga karshen asali, kowacce a cikinsu tana cike da dana sanin rayuwa.. Raliya da Reemah ne kadai ke kai kawo a kitchen suna hada hadar haďa lunch, sai Husna, Maleekah da Nadeeyah dake tayasu, Maleekah da Nadeeyah hira sosai sukeyi kamar sun dade da sanin juna, gasu dukkansu wayayyu babu wacce ke jin kunyar yin magana... Bayan sun dan taba abinci duk suka nufi waje dan yin Sallah.. su kuma matan suka nufi daki dan yin tasu a can... Gyara parlon Husna da Nadeeyah sukeyi suna hirar yaushe gamo, labarin abubuwan da suka faru bayan bata nan take bata, ga mamakinta bata ji inda tace "Musaddiq yayi aure ba, sharewa tayi ta kauda tunaninshi a ranta domin yanzu tana son tayi moving forward... rashin ganinshi a cikinsu ya tabbatar mata yana can yana rayuwarshi cikin jin dadi.... Duk wannan budurin da akeyi Musaddiq na cikin daki ya kure volume suna game shi a dole bayason jin wani abu da ya shafi su Badariyya.... Ganin little Nadeeyah tayi bacci ne ya sashi gyara mata kwanciya ya shiga ya watsa ruwa, kananan kaya yasa wadanda suka fitar da kyawunshi sosai, yanzu girma ya sanya Musaddiq ya zama moderate, wannan kibar duk babu ita, sai tsawo sosai da dan murjajjen jiki, kwantacciyar kasumbarshi ya taje ta kwanta lup a fuskarshi, turaruka masu kamshi ya feshe jikinshi dasu sannan ya kashe wutar dakin,

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156