Chapter 9
Chapter 9
ta fadi tana girgiza kai, tsaya a nan in dauko plate, wannan acicin ne zai bari muci tare, Dariya ce ta gauraye parlon ciki harda musaddiq da suka fito tare da Hilal, wani miyau Hinad ta hadiye ta kwalolo ido saboda irin kallon da Hilal ke mata, baya ta fara ja a hankali tana kallonshi, a guje ya bita ta saki wata razananiyar kara ta nufi Sama tana fadin "wayyo Allah Papa zai kasheni,, cike da tsokana papa ya daka mishi tsawa yace, "karka taba min 'ya tunda ba karya tayi ba, duk rabin abincin gidan nan wake cinye wa,? Sanin ci irin naka ne yasa Meerah tayi Maka naka abincin daban, ko ba haka ba Merah?, aaaahhh... Papa pls karka hada ni da Hilal meerah ta fadi fuskarta dauke da murmushi, favourite dinshi na dafa mishi daban, Papa ya murtuke fuska yace nayi karya kenan? Meerah ta daura hannu a kai tace nooo baka yi ba,, Papa ya kalli Hilal yace "to kaji, zo kawai ka zauna Kaci abinci nasan kana jin yunwa, hade rai Hilal yayi yace "nakoshi" yasa kai yayi hanyar daki, kiranshi anty reema ta shiga yi ko waigowa baiyi ba ya shige dakin ya bugo kofar da karfi,, kallo anty reema tabi Papa dashi ya dauke kanshi ya cigaba da cin abincinshi yana yan wake wake, Musaddiq ya mike zai bi Hilal Papa ya tsayar dashi yace dawo Kaci abincinka indai hilal ne yana zuciya da komai banda abinci, ka rubuta ka ajiye ko karfe nawa ne sai ya fito yaci abincin shi, nan take Hinad ta saki dariyar da ta dade tana gimtsewa, Anty reemah ranta ya kara baci tace "walhy zanci mutuncinki yanzun nan, sa'anki ne? Gyada kai tayi tace "sorry mum, dalla yi kiyi ki tashi kije kiyi sallah ki kwanta, da wani katon bakinta Mai shegen surutun tsiya, Papa dai baice komai ba ya mike ya nufi gurin meerah dake tsaye yace "je ki kwanta Dota Allah yayi miki albarka, Ameen Papa,, ta kalli anty reemah tace "gud nyt mum, nyt sweet heart ki gaida Ammi.... ******* Kaduna.. Nigeria Rayuwa ta dan fara sauyawa su mamma suwaiba saboda yar sana'ar da sukeyi, ga hafiz dake harkar fruits, yanzu kullum sai ya samu dari biyar wata rana fiye da haka, ga kuma rarar fruits da yake samu ya taho dasu gida su Sha su kyautar da sauran, Yana matukar Jin dadin sana'ar saboda sana'a ce mai albarka, Saida yayi sati uku yana koyan harkar sannan anty reemah ta turo mishi da dubu dari biyar, a ranar saida yayi kukan murna dan ko a mafarki bai taba tunanin rike dubu hamsin tashi ta kanshi ba, bare dubu dari har guda biyar, Allah kenan in yace "ku fa ya kun" shikenan, (Allah ka datar damu).. Zama yayi da Mai gidanshi sukayi shawarar abunda zaiyi da kudin, d'aura shi yayi akan harkar sosai saboda yanada jarin shi na kanshi, babu inda basa Zuwa saro Kaya basu onitcha, enugu Lagos da sauran guraren sarin kayan fruits,, Cikin ikon Allah da taimakon Papa aka bawa Nadiya admission a fgc malali, Hafiz yayi kokari wajen yi mata komai na tafiya makaranta, haka babanta da Mamma suwaiba duk sunyi mata kokari, Sam bata San tafiya saboda tausayin mahaifanta, wani bangare na zuciyarta kuma ya bata shawarar, Ilimi shine gishirin zaman duniya, kuma ko ba komai zata kauracewa ganin Badariyya, da wannan tunanin ta samu karfin gwiwar tafiya makarantar kwana.... ***** Frederick University.. Gudu yake shararawa cikin motarshi kirar KIA karama ruwan goro, wakar "Rockabye" ta "Anne-marie ya Kure volume yake saurare yana bi a hankali, hon ya latsa da karfi yana sauke glass din motar hade da kallo inda take.. mikewa tayi ta isa gurinshi ta bude kofar gaba zata shiga yayi saurin dakatar da ita, "baya zaki zauna ko kin manta bani kadai bane, rufewa tayi bata ce kala ba ta bude baya ta shiga, ko kallonta baiyi ba ya tada motar ya wuce "faculty of engineering" a kofar dept din ya hango shi zaune yana duba wasu littafai, kashe motar yayi ya fito ya karaso gurinshi yace "heyyy guru" shall we, musaddiq ya mike yana kakkabe jikinshi yace eh mu tafi, waya Hilal ya mik'a mishi yace "call ur mama ta kirani Wai wayarka a kashe, Musaddiq ya dan ja tsaki yace "barta zan kira in naje gida na gaji Sosai, mayar da wayar aljihu yayi ya bude kofar motar ya shiga,, gaisawa musaddiq sukayi da meerah dake baya tana shafa hoda a fuska,. kallonta Hilal yayi ta mudubi yace "madam makeup" an fara, banza tayi mishi ta cigaba da kwalliyarta, jan motar yayi yana murmushin ko a jikina yarinya... Mrs Tijjani Shattima... [04/12 09:46] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU By Aysha Ya'u Kurah 1⃣1⃣ Shekaru sun dan jaaa, cikin farin ciki da akasin shi saboda halin rayuwa na yau zuma gobe madaci, "Nadiya Adam" muje mu rage Miki hanya mana, yamutsa fuska Nadiya tayi cikin damuwa tace bari kawai Rukky, zan samu napep in tafi, Kallonta rukky tayi cike da mamaki dan dai tasan bata da ko Naira biyar a jikinta, hannu tasa ta fara daukar kayanta tace zan kai miki kayan, ki taho a mashin ma wannan ke ta dama, bin ta Nadiya tayi da kallo tace "Haske dan Allah ki barshi kar in matsa muku Kinga hanyar mu ba daya bace, "ke kika rokeni? Rukayya ta fadi fuska a hade,, Girgiza kai Nadiya tayi tace "a'a amma--- amma me Haske tayi saurin katse ta, tace "zo mu tafi dan Allah, kwashe sauran kayan tayi ta bi bayan Rukayya Haske ranta duk a jagule, A gatance ta fara makaranta, tun daga shigarta har Zuwa ss1 third term, tunda ta dawo first term din nan ko sau daya babu wanda ya ziyarce ta, zuciyarta cike take da fargabar abin da yake faruwa da Yan gidansu, number yaya Hafiz Sam bata shiga haka ta mamma, tunda ta shiga motar take addu'ar Allah yasa kowa na nan lafiya, dai dai kofar gida suka sauketa suka wuce cike da kewar makaranta, Jakarta ta dauka ta fara tafiya domin karasawa cikin gidan, A can bakin murhu ta hangi mahaifiyarta idonta yayi jawur hanci duk ruwa saboda wahalar hura wuta, ajiye Jakarta tayi ta karasa kusa da ita, idonta cike da kwalla take kallon mahaifiyarta dake mata murmushi, hannunta Nadiya ta kama zata fara magana suka jiyo tari me karfi babu kakkauci daga cikin dakin, da gudu mamma ta nufi dakin tana fadin subhanallah!! sannu, bin bayanta Nadiya tayi da sauri, ta tarar da abin da ya daga hankalinta matuka, mahaifinta ne kwance cikin bargo kamar jaririn goye, ya rame ainun, idanuwanshi sun zurma sai tari yakeyi hade da kakin jini, kuka mai karfi Nadiya ta saki tana fadin meya sameka Baba?, mamma me ya sameshi,? mamma dake tare jinin da wata tsumma tayi kokarin boye idonta da ya ciko tace "bashi da lafiya ne amma da sauki, wani irin sauki mamma, Ina saukin yake anan?, dan Allah ki kira yaya Hafiz mu kaishi asibiti, nan kukan da mamma ke boyewa ya bayyana, Take Nadiya ta rikice, dan ita dai tun tasowarta bata taba ganin bacin ran mahaifiyarta ba bare har takai ga zubar ruwan hawaye, Durkushewa Nadiya tayi tace "mamma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156