Chapter 135
Chapter 135
kai da akayi... Gaba daya ummul ta manta cewa akwai mutuwa a bayan rayuwa, damar da Allah ya bata ta butulce mishi tayi wasa da ita, lokacin aji na biyu a jami'a, da taimakon Allah da taimakon Sheik na samu na kammala makaranta, Dan kudin da gwamnati ke bamu na scholarship da kudin aikin ginin da nakeyi yasa ni na fara dan karamin business dina, cikin ikon Allah kafin shekara abun ya bunkasa dan har na sai fili nawa na kaina, a lokacin ne kuma Allah ya azurtani da samun mace ta gari Zeenat yar gidan Sheik, Shekararmu biyu da aure muka samu Irfan, daga nan ne kuma duk shekara sai ta haihu wasu suzo babu rai, wasu kuma suyi watanni su mutu, daga kan Maleekah ne kuma haihuwar ta tsaya mana duk da ba haka naso ba, amma zabin Allah shine zabin komai..... ya karashe yana share hawaye haďe da yin murmushin takaicin fitar da irin kunar ukubar da yasha yana yaro..... Babu wanda bai zubda kwalla ba a dakin, lallai mutanen zamanin yanzu banda rikon sakainar kashi da sukayi wa zumunci, harda illata rayuwar juna ma sun kware akanta.... Babu wanda yake da kwarin gwiwar faďin mutuwar Atika domin basu san katse mishi shaukin da yake ciki... Wayar Papy Daddy ya kira domin jin ko sun kusa isowa, kashe wayar yayi yace wa Musaddiq "har sun iso bakaje ka daukosu ba, "Zubair zai dauko su, Musaddiq ya faďi cikin girmamawa.. "Okk to, Allah ya kawosu lafiya, Daddy ya faďi haďe da sake jan sheik da hira.... Motar da Zubair ya sai mata farar matrix sabuwa dall ita ta tuko tazo gidan tare da kayan abincin da ta hadawa bakin, koda ta isa gidan kiran Musaddiq tayi a waya dan ya fito ya tayata shiga da kayan, Fitowa sukayi shi da Hilal suka kwaso kayan abincin, tsokanar Musaddiq Faidah takeyi wanda ya sanyashi yin murmushi haďe da matsowa amsan tray din hannunta, Garammmmm.... sukaji an saki kofar gidan da karfin gaske...... Mrs Tijjani Shatimah..... [11/06 8:34 PM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 7⃣2⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Anty.... Nadeeyah ta faďi cikin dashewar murya, juyowa Raliya tayi ta sake kankame junior a kirjinta, "Na'am Nadeeyah, wayar dake hannunta da take kokarin kira Nadeeyah ta karba ta ajiye a gefe, "Dan Allah kiyi min alfarma ďaya! Dan Allah karki sanar da kowa dawowata, inada dalilai masu karfi da in na faďa miki zaki fahimceni, dan Allah Anty ki dubi maraicina kiyi min wannan taimakon! Cikin sanyin jiki Raliya tace "Nadeeyah nayi miki alkawarin in har dalilanki masu karfi ne zan taimakeki har sai kin cika burinki, faďa min kanwata.... Anty bani da gatan da wuce Allah, bamu da asali ni da yan uwana kamar yadda ake faďi.. na taba ji a bakin wani malamin mu cewar Allah da ilimi sune gatan maraya, babu wanda zai zama maraya sai rago, sannan wannan ilimin shi zai sa ka samu yancinka a cikin al'umma, a yanzu in na zauna tare daku, Mummy da su Anty Raudha bazasu taba barina in yi rayuwar yanci ba, sannan bazan iya jurar ganin yaya Musaddiq da wa------ Shhhhhh... Anty Raliya ta katseta saboda ganin junior na kokarin yin bacci, sabashi tayi a kafaďa tace "ina jinki? Na dade da burin yin ilimi mai zurfi, dan Allah ki goyamin baya in samu abinda zan tsaya da kafafuwa na, banason mu kare a haka ni da zuri'ata, kinfi kowa sanin rayuwar rashin gatan da mukayi mu da iyayenmu, bana fatan mu kasance a cikinta ni da ďan da na haifa, nayi miki alkawarin zan kare mutuncin kaina, zan nemi kuďin halal inyi sponsoring kaina, su uncle Taheer sunyi min duk abinda ya kamata dan uwa yayi maka, yanzu zan fita in nema da kafata har Allah yasa na dace.... "Duniya nada faďi Nadeeyah, ta ina zaki fara? Gabas, yamma, kudu ko arewa? Inada dukkan karfin da zan dauki nauyin karatunki a duk inda kike so, bazanyi hakan bane sai da yardar wani naki, shiyasa na kawo ki nan saboda ita kadai na sani a cikin yan uwanki, in yarintarki na faďa miki cewa duniya kankanuwa ce to kinyi kuskure, domin ko a kaduna north kaďai aka barki an haďa ki da aiki dan bazaki taba sanin ta inda zaki fara ba, ki dogara da Allah sannan ki nemi zabinsa akan duk abinda zai zame miki alkhairi a rayuwarki, in karatun alkhairi ne ni zan dauki nayinshi har ki gama.. In kuma babu alkhairi to tabbas Allah zai nuna miki ta hanyar zama cikin yan uwanki... Gyara zama Anty Raliya tayi bayan Taheer ya disa aya, kallonshi tayi tace "Taheer zauna, zauna muyi magana, ka riga ka zama dan uwa, babu abin da zamu boyeshi a gareka... Bayan ya zauna ta kwantar da Junior ta dubi Nadeeyah, "Tabbas maganganun ki gaskiya ne Nadeeyah, nasani sarai a yanzu in har kika dawo cikin mu wasunmu bazasu bar rayuwarki da ta ďanki su inganta ba, zan jure duk wasu matsalolin da nake gani a cikin yan uwana, zan kauda tausayin nawa domin rayuwarki ta inganta, nayi miki alkawarin babu wanda zaiji inda kike daga gareni, yanzu inada wasu kuďaďe zasu kai 1.2m.. zan baka Taheer sai kayi amfani dashi ku koma can Canada da zama tunda Anty saude nacan, in yaso duk abinda ciko ya biyo baya ka sanar dani, sannan zan dinga turo da wasu yan kuďaden da zata dinga amfani dasu, nayi alkawarin inganta rayuwarki da ta Daddyna in shaa Allah... Hawayen dake zuba a kuncinta Nadeeyah ta share mata ta tsuguna tana mata godiya kamar zata bauta mata.. Kallonsu Taheer yayi cikin tausayawa da farin cikin cewar akwai mai kaunarta a cikin yan uwanta... "Anty Raliya, ba sai kin bani ko sisi ba, nima ki barni in samu ladan marainiya, babu mamaki sanadin hakan ya sanya na samu biyan bukata a gurin Allah sannan zanyi hakan sadakatul jariya Allah ya kai ladan kabarin mahaifina.... Murna sosai Anty Raliya tayi ta dinga mishi godiya da addu'ar samun abin da yake so cikin sauki ba tare da yasha wahala ba.. Bayan yaci abinci ya koma gidansu ya bar Nadeeyah da junior Anty Raliya nata musu hidima kamar kar su tafi.... Wannan shine mafarin zaman Nadeeyah da junior a gurin su Taheer.. Da farko da suka koma Anty Saude kin yarda tayi da zaman Nadeeyah a gidan, Duk da tana kaunar zaman junior haka ta rufe ido dan gudun kar ďanta ya koma gidan jiya, Saida ya tubure yace shima zai bar gidan sannan ne ta amince da sharaďin bazai taba zuwar mata da zancen soyayyar Nadeeyah ba... Ba tare da doguwar jayayya ba ya yarda dan a lokacin so yakeyi yaga ya taimaketa ya mayar da ita cikakkiyar mace..... Cikin sauki yasa Kamal ya turo da result dinta na waec sannan ya fara cuku cukun samar mata makaranta mafi kyau ta mata zalla a canada.... Ba tare da bata lokaci ba ya samar mata ta fara zuwa, da fari rainon junior yana dan bata wahala saboda yadda karatun yazo mata, saidai kuma cikin ikon Allah Anty saude ta hanata fita dashi ko nan da can a cewarta rana na matsa mishi... Soyayya da kauna babu irin wacce
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156