Chapter 116
Chapter 116
abunda zai je ya tarar.... A airport din su Daddy suka jira zuwan su Papy dan su karasa tare, Yanayin da Papy yaga Daddy ya ďaga mishi hankali matuka, kusa dashi ya matso yace "Kayi hakuri Alh Mukhtar, cuta ba mutuwa bace, in shaa Allah zai tashi, kukan da Daddy baiyi ba jiya shi ya saki mai karfi haďe da rungume Papy, share hawaye Anni tayi tace "Mu karasa can asibitin dan Allah, ba sai mun tsaya munyi magana anan ba... jiki a sanyaye Papy ya kama hannun Daddy yana bashi hakuri har suka isa gurin motocin da abokin Daddy ya turo musu... A kofar dakin da aka sa Musaddiq sukaga Hilal rungume da Hijab har lokacin idonshi na fitar da ruwa, daga shi har Zubair babu wanda ya runtsa, yana ganinsu ya mike da sauri ya rungume Daddy yace "Wallahi Daddy sun kasheta, Nadeeyah ta mutu, muje kaji daga bakin doctor... A ruďe Mami tace "Wace Nadeeyar, sai a lokacin Hilal ya lura dasu, nan wani sabon kukan ya kwace mishi ya shiga basu labarin abun da yaji da kunnenshi, Abbati da ya kira Daddy yace su haďu a asibiti shima ya daura daga inda ya sani, nan fa guri ya kaure da kuka, sun ma manta a asibiti suke, Jan Daddy gefe Abbati yayi yace "Ni yau zan koma india, yara kuma sun wuce katsina, na faďa ma Raudha in ta samu miji tayi aure, kayi hakuri dan Allah, Allah ya haďa mu da alkhairi, Murmushin yake Daddy yayi yace "Allah ya albarkaci rayuwarka Yusuf, ai kayi kokari, nagode sosai, Duk da Papy na cikin tashin hankali hakan bai hanashi mikewa da niyyar yi ma Abbati magana ba, rikeshi Daddy yayo yace "Ya cika dan halak, kowa hakan zaiyi in yaji abin da suka aikata, "Dan Allah ka yafe min proff, da sauri Papy yace "Haba, mu su waye da zamu tsallake hukuncin ubangiji, itama lokacin da ta dauko kenan, rayuwarsu ta jin daďi na gidan lahira in shaa Allah, yadda ya karashe maganar cikin rauni ya sanya su sake wani sabon kukan, Duk papy yadda yakai ga matsewa ya kasa saboda shima a karye yake, nan ya zauna ya rufe fuskarshi yana kuka sosai, a duk faďin gurin nan babu wanda yakeda karfin bawa wani hakuri..... Reemah... ki kira danki kice mishi ya dawo min da ďana, tun daren jiya da ya daukeshi ya fita dashi har yanzu basu dawo ba, ki kirashi ya dawo min dashi, tunda shima yana san Nadeeyar in ta gama idda sai ya aureta kuje can ku karata, tunda ke baki san ciwon kanki ba, ki haifi ďa ya dinga juyaki... Mummy na kaiwa aya Anty Reemah tace "Ina airport, danki yana asibiti, ďana bai kai ga yi mishi illa ba, ita kuma wacce kika tsana din da zata dawo gidan duniya da babu abinda zai hana ban aura mata Hilal ba, ai da nasan yasota tun farko da saidai Musaddiq ya hakura tunda shi matsayin uba yake a gurinshi, saidai kashh... yayi nauyin bakin da ya jefa rayuwar Nadeeyah cikin garari, yanzu tunda kunyi sanadiyyar da ta zama gawa, sai ku fara murna ku nema ma Musaddiq hurril aini, tana kaiwa ta katse wayar cike da ďacin rai, bata taba yi ma mahaifiyarta musu ba, amma a yau ta kai bango sosai wanda har ya sata fadin maganganu cikin ficewar hayyaci.... A gigice Mummy ta nemi guri ta zauna tace "Nadeeyah ta rasu, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Raudha dake kiran wayar Abbati tana kuka tace "Whatt... ta rasu? "Wallahi ta rasu, yanzu Reemah ke faďa min, itama tana hanyar zuwa.. Daukar trolley Radiya tayi da sauri tace "Nidai ba ruwana, yanzu nan zan tafi gida gurin 'yayana, Allah ya taimakeni Shamsu bai san labarin nan ba, kallon Raudha tayi tace "Allah ya daidaita ku, Mummy, na tafi kaduna sai kun karaso, tana kaiwa nan ta ruga da gudu da jakarta tana mai dana sanin biye ma zuciya.... A tsure Mummy ta mike ta kira wayar Mahmoud tace ya tambayar mata Zubair wani asibiti suke, Mahmoud ya rude sosai ya kira Zubair dan jin abinda ya faru, sunan asibitin kadai ya iya faďa mishi ya kashe wayar saboda tashin hankalin da suke ciki na cewa Musaddiq ya shiga Coma, Kiran Mummy yayi ya faďa mata sunan asibitin, bata jira abinda zaice ba ta mike ta sanya gyalenta suka wuce tare da Raudha, burinta Allah yasa ba'a faďa ma Daddy abinda ke faruwa ba, tasan yadda zata lauya zancen har ya gamsu da ita.. Kuka ta kakalo ta dinga yinshi cikin motar da zata kaisu asibitin... Da Hafeez ta fara karo yana zaune a bakin gate din asibitin yana kuka sosai, Husna dake tsaye a bayanshi ta dafa kafadunshi a tsorace itama kukan takeyi, kukan rashin Nadeeyah da kuma kukan hali irin na Mahaifiyarta, Mummy na ganinsu ta fito daga cikin mota ta nufosu tana kuka, da sauri Husna tace "Dan Allah karki iso nan da dramarki Mummy, kun kasheta, hankalinku ya kwanta, sai kuyi celebrating ai ba kuka ba, Cike da mamaki ta kalli Husna tace "Auta ni kike faďawa haka, har kin yarda zan iya kashe Nadeeyah da nake so kamar raina, "So indeed, yaushe kika fara sonta? So bayan rai ko, wallahi alhakin Nadeeyah bazai barku sukuni ba, i ha---- toshe mata baki Hafeez yayi yace "Don't say anymore, uwa uwa ce, rungumeshi tayi tana kuka sosai haďe da bashi hakuri.. bayanta ya shiga shafawa yana kwantar mata hankali, yasan irin kaunar dake tsakaninsu, abin da mahaifiyarta tayi bazai taba shafar zamansu ba saboda Zuciyar Husna kamar gold take saboda kyalli.... Bayan sun tsagaita kukan Doctor ya basu shawarar da su bi manyan asibitoci su duba gawarta a samu a sallaceta cikin gaggawa, Suna cikin yanke shawarar yadda zasuyi Mummy ta faďo gurin da suke tana ihu mai haďe da kuka, babu wanda a cikinsu ya kalleta bare har yasan abun da takeyi, Ganin tana neman cika ma yan asibitin kunne yasa wasu Nurses cewa tayi hakuri ta fita daga waje, tana damun patients dinsu, "Sirikata ta mutu sannan ďana na kwance rai a hannun Allah zaku ce inyi shuru, bazanyi shurun ba, ya Allah ka sassauta min, wayyo Allah na shiga uku, Gadan gadan Daddy ya nufota dan ta kure duk wata dauriya tashi, tana ganinshi gab da ita tayi saurin mikewa tana share hawayenta, cike da kissa ta faďo jikinshi tace "Ance Nadeeyah ta mutu, daga sokoto na biyo jirgi na iso nan direct, me ya samu Nadeeyah, me ya sameta?... ta karashe tana kuka sosai, Ran Hilal ya baci matuka na rainin wayon da tazo dashi yayi saurin mikewa zaiyi magana Jamal ya rikeshi, danne hannunshi yayi yace "Karkayi magana, duk lalacewa ita ta haifi mahaifiyarka, dafe kai Hilal yayi yace "shine abun da nake jin haushi matuka, ina ma ace bare ce, wallahi hukuncin da zan mata ba mai sauki bane.. Raba jikinshi yayi da ita haďe da kama hannunta ya fara janta har suka fita waje, bayansu Papy yabi yana cewa "Kayi hakuri Alh Mukhtar, ka kyaleta sai mun koma gida, yanzu fatan mu Allah ya bawa Musaddiq lafiya, kuma Allah ya bayyana mana gawar Nadeeyah cikin gaggawa, Bai saurare shi ba ya hankaďata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156