Chapter 33
Chapter 33
sanďa wani sumameshi ya luma mishi wuk'a a bayanshi saitin da zuciya take, nan take ruwa mai karfi ya kece a cikin kauyen, wani irin ihun murna arnan suka fara yi dan duk sunbi musulman sun musu kisan gilla, harda matansu da ya'yansu, cikin murna suka nufi cikin gidan suka fara kwaso shanaye suna bi takan gawarwakin.... Ma'u kuwa tun tana jiyo ihu har ta daina ji, anan ne jikinta ya bata an gama komai,, cike da murna ta fito gida da niyyar zuwa gidan Haire, a kofar gidan taci karo da Baffa da kaya niki niki a hannu, karbar kayan tayi ta fara murna suka shiga cikin gidan, a tsakar gida ya baje kayan yana bata labarin irin abubuwan alkhairin da ya samo, "Ta ina ka shigo garin nan? Ta jefo mishi tambayar tana kallonshi hade jiran amsa, " Ta bayan gari, saboda bana sann kowa ya rigani fada muku isowa ta, yanzu wanka zanyi in wuce gidan Malam, naga garin ma ba kowa nasan duk suna can maza da mata ana sallar juma'a da wa'azin Hardejo, cike da kissa tace "nima ko sai muje dan bacci ne ya daukeni ban samu zuwa ba, dube dube taga ya fara yi tasan tabbas Atika yake nema, murmushi tayi tace "Amarya tana can gidan Hardejo, ka tafi kabar amarya da nauyinka, nace su Baffa ba'a cika min alkawari ba, cikin rashin fahimta yace "me kike nufi? murmushi tayi a ranta na mugunta ne amma a fili ta nuna na soyayya ne tace "matarka dai ciki gareta, tama kusa haihuwa, a daburce yace "ma'u ban karya miki alk---- katseshi tayi da sauri tace "babu komai ai matarka ce, ni fatana ma mu samu dan namiji tunda naga dukkanku baku da namiji, kaga sai mu samu magaji, murmushin farin ciki Baffa yayi ya mike yace "dauko mayafi mu tafi, zunde tayi mishi ta baya sannan tace " har ka fara zumudi, nima bakaga yadda na kosa ba, komai a gidan nan bana barinta tayi, ganin cikin nema yasa hankalina ya kwanta dan ina tunanin namiji zata haifa mana, rungumeta Baffa yayi cikin farin ciki yace "Ma'u shiyasa nake kara kaunarki, tun farkon haduwar mu kike min halacci har kawo yanzu, nagode nagode, gwalo tayi ma bayanshi tace "Ai mun zama Daya Baffa.... Tun a bakin gidan jauro suke karo da gawa har suka isa kwanar gidan Hardejo, wani irin ihu Baffa ya saka da yaga Hardejo kwance cikin jini ruwan da akayi ya dama gurin, girgizashi ya fara yi ya dinga rusar ihu yana fadin waye ya aikata haka a gareka, waye ni, wayyo ni Allahn Hardejo, Dafa shi wani dattijo yayi a cikin wadanda suka gudu yace "Tashi Muhammadu, yanzu ba lokacin wannan bane muyi gaggawar haka rami a cikin gidan hardejo mu tattarasu duka musasu a ciki domin kuwa yanzu makasan sun tafi hada walimar murna kafin su dawo su mamaye gidajen, kuma kaima muna gamawa ina umartarka da ka gudu da kai da iyalinka, mikewa Baffa yayi a tsorace yana kuka suka shige gidan su biyar da wasu samari, a cikin gidan ma ya daburce ya dinga kuka yana kiraye kirayen suna, ita kuwa Ma'u rashin ganin Atika cikin gawar wakin ne ya fi daga mata hankali, kar dai ta samu ta tsere, dube dube ta fara yi har ta kai ga bayin gefen dakin saudatu, Atika ta gani tana kuka tana nishin nakuda, da sauri ta tufe bayin ta koma gurin su Baffa, duk wanda a cikinsu taga zaiyi gurin sai tayi maza ta hanashi, hak'a rami sukayi mai zurfin gaske da tsaho, suka fara dibo gawarwakin suna turawa a ciki, saida suka gama tsaff ta Hardejo ta zama ta karshen sawa, fuskarnan tashi dauke da murmushi, wani kukan Baffa ya saki yana zuba kasa a kanshi yana rusa kuka, saida suka gama komai sannan hankalinshi ya dawo kan Atika da bai ganta ba, Ma'u in dai ba idona bane yake min gizo banga Atika ba,, kafin Ma'u ta bashi amsa sukaji kukan jariri da karfin gaske, runtse ido Ma'u tayi tace shikenan yazo duniyar, da sauri Baffa yabi ta inda yake jin kukan, kofar bayin ya tura da karfi, a durkushe ya sameta tana dada dafe cikin alamun akwai wani a ciki, daukar jinjirar yayi sannan ya taimaketa ta fito suka wuce dakin Aisha, bin su Ma'u tayi tace bari in taimaka mata, Kamar zautacciya ta dinga maimata yan biyu kyautar Allahn Hardejo, tsaye yayi akansu ya rufe ma jinjirar hannunshi jiki da zanin mai babban suna, saida ta kara awa daya sannan ta haifo Danta kato namiji, cike da yake Ma'u tace "tafi ka nemo abin da zamu yanke cibi, wani abu mai kaifi Atika ta sanya a hannun Ma'u, harararta tayi ta yanke cibiyar, kallon jinjirar hannunshi tayi tace "dame aka daure cibiyar, zanin jikinta ne ta yaga ta daure dashi, kallon ta ma'u tayi a zuciyarta tace duk a ina ta koyo wadannan abubuwan, wani tsumman ta kuma yaga ta katsewa ma'u tunanin da takeyi, amsa tayi ta daureshi sama sama, ta kuma dukunkuneshi ta hana Baffa ya daukeshi, saboda rashin imani Ma'u na ganin jini na ambaliyar fitowa daga jikin yaron tayi banza da alamarin, kuka sosai yaron keyi amma saboda kawaici Baffa yaki yunkurin karbarshi, a ganinshi ma'u ma uwa ce a gareshi, kuka Atika ta fara yi ta yafito Baffa da hannunta, tsugunawa yayi a gefenta shima cikin kuka yace "bana gane abinda kike cewa, cikin yaren fulani wanda ta fara fahimta kadan kadan tace " *SUWAIBA* Shine sunanta,, sunan ummuna,,, shi kuma *SAIFULLAH* in har ya kasance cikin rayayyu, Ka kularmin dasu, Amanarka ne su, Dan Allah ka Nemi *Ateek* da Abbuna dan Allah.. kuka Baffa ya cigaba da yi sosai yana fadin bazaki mutu ba, ki yafemin dan Allah, share mishi hawaye tayi tace "Inda zan tafi ya fiye min nan, son samu ma in tafi da 'yarana, Allah yayi bazan rayu dasu ba, Muryar samarin sukaji a waje suna fadin ku fito mu tafi Muhammadu gasu nan dawowa, da sauri ya mikawa ma'u jaririyar ya dauki Atika a kafadunshi suka bar gidan da sauri... Tun a hanya ma'u ta gane namijin ya cika, nan fa hankalinta ya kwanta sosai, suna shiga gidan yayi saurin shimfidar da Atika ya dauko ruwa yana shafa mata, salati ta farayi idonta ya fara kafewa, ta kara cigaba da kiran sunan Allah, ga jini har lokacin zuba yakeyi kamar famfo, cikin tashin hankali yace ma Ma'u ta taimaka ta kawo maganin da take sha idan ta haihu, kwantar da yaran tayi taje ta dauko MANDA mai tsinka jini ta jikata da yawa ta kawo mata, dago kanta tayi tasa a bakinta ta dure mata shi tasss, wani jinin ne ya kuma tsinkewa shaaaaaa, nan da nan ganin Atika ya dauke, hannuwanta suka saki gaba daya, babu abin da kake iya jiyowa sai sautin kukan jinjirar da maganar Atika, *SUWAIBA* Sunan da take ta maimaitawa kenan hade da kalmar shahada..... Mrs Tijjani Shattima..... [04/03 11:57 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 2⃣7⃣ By *Aysha Ya'u Kurah* *KADDARA* _Ba wanda ke shigowa cikin rayuwarmu ba tare da wani dalili ba, tun daga ranar da aka haifemu har izuwa ranar mutuwar mu, da kowa muka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156