Skip to content

Chapter 125

Chapter 125

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

da tayi ne, ta dinga fankama nan da sati zaizo ya maida Mummy dakinta.... Gidan Anni suka yada zango nan suka ci suka sha sannan suka bararraje anata hira har bayan la'asar, Anni hana matan tafiya tayi tace saida mazan su tafi, haka kuwa akayi su Mami suka zauna a gidan suka raba dare suna hira ana fassarawa Anni da ummi.... Kuďi masu yawa Anty Reemah taba Mummy sannan ta je gidan Raliya tayi mata faďa sosai akan rashin taimakama su Mummy, a sannan ne Raliya take faďa mata Daddy ne ya hanata yace in tayi sai ya saba mata, dafe kai Reemah tayi tace "Daddy yayi fushi da yawa, wallahi ko maganar Mummy baya son ayi mishi, "Addu'a kawai zamu cigaba dayi danni ita kadai ke bani tausayi ba su Anty ba, dey deserve it... Raliya ta faďi rai a bace... sun dade suna hira suna nemawa mahaifiyarsu mafita.... Kwanansu Sheik Uku suka shirya komawa gida da yan uwa dan suje suga inda yake, kyautar ban girma yayi ma su Mummy wacce zata mantar dasu talauci na wucin gadi, tayi murna sosai da wannan kyauta dan saida tayi kamar zata mishi sujjada, har suka tafi baisan cewa Mummy matar Daddy bace, ya dauka kawai a gidan take zaune, ya dai san yayar su Papy ce.... *Cyprus...* Da yake mansion din Sheik yana da matukar girma hakan yasa ya kwashe dukkansu, harda Husna da suka taho da ita dan ta haihu, dadin duniya babu wanda bai jiyar dasu ba, duk companies dinshi saida ya nuna musu harda na wasu kasashen, Saboda murna ya cire wani babban companynshi dake Holland ya mallakawa Papy a matsayin gadon mahaifiyarshi, sannan ya bawa Hafeez wani abun shima, gaba ďaya ya kasa controlling kanshi akan zuri'ar yayarshi.... Kwanansu biyar a garin akayi ma Husna tiyata aka ciro mata baby girl saboda haihuwar tazo da Matsala, lokacin su Daddy sun koma Nigeria, murna a gurinsu ba'a magana saboda dama cikin na yawan bata wahala, Papy da kanshi ya shiryawa Mummy tafiya dan taje gurin yarta taga jikarta, Ita dai a kullum haushin kanta takeji na biyewa zuciya tayi wa Suwaiba abubuwa marasa dadi kafin mutuwarta, gashi yanzu danshin su take raba taji dadi, lallai da ta hana auren Hafeez da Husna da sai takaici ya kusa ajalinta, kullum bata da addu'ar da ta wuce Allah ya dawo da Nadeeya cikin koshin lafiya dan danta ya samu farin cikin rayuwa, a yanzu ko ita bata samu farin ciki ba 'yayanta su samu, ta fahimci farin cikinsu shine nata, ďan zaman da tayi da su Radiya ta fahimci cewa ba kowani ďa bane ke sadaukar da farin cikin sa akan iyayenshi, a nan ta koyi basu farin ciki, in ta gansu cikinsa tasan itama zata kasance a ciki... Ranar Suna Daddy ya sanya wa yar suna Suwaiba, sosai dangi suka nunawa yar gata dan ta samu kaya na gani na faďa, Mummy ta sake tsorata da ikon Allah da tazo taga daular duniyar da dangin Atika ke ciki, inama Suwaiba na raye tazo ta dandani arziki, wayyo, ita nata dadin a lahira ta ďeboshi..... Na fa lura da wani abu Anty, Raliya ta faďi tana sanyawa Nour ďiyar Husna pampers, "Me fa? Anty Reemah ta tambaya haďe da gyara zama, "Na kusa yin siriki, Raliya ta faďi tana murmushi.. "Wa kenan?? "Dadina dake ganewa Anty Raly, Husna ta faďi tana ajiye kofin shayi, ni ai tun tuni na sani, Jamal ya hanani faďi, "Kaii nifa ban gane ba, wai me kuke nufi? Anty Reemah ta tambaya cike da mamaki, "Y'ata ta wajenki tayi kasuwa, soyayya sukeyi da Jamal, Mikewa Anty Reemah tayi tace "to ai ba sai kun faďa min ba, kuma iyaye ne, in akwai alheri Allah ya tabbatar... Dariya sukayi haďe da tafawa suka ce Ameen Ameen, ashe zamu sha biki... Hinad da ta doso dakin ta juya da sauri ta nufi waje cike da murna, tasan tunda Anty Raly tasa baki Allah ya kusa cika mata burinta, soyayyar Jamal ta zame mata tamkar jini da hanta, bata jin akwai abin da zai cire mata sonshi cikin ranta, kamar shima yadda Jamal din keji game da ita saboda kyawawan dabi'unta, zuwanshi kasar yasake sanya shakuwa mai karfi a tsakaninsu, wacce har ta sa aka fara diga ayar tambaya akansu..... Zaune suke a katafaren parlon sama suna duba ayyukan da gwamnati tayi approving, Zanen da Hilal yayi wannan karan na musamman ne, cike da yabawa sheik ya kalli zanen karshe yace "Bravoo alaika ya Hilal, Allah ya albarkaci hannunka, yanzu kaga sai dai kawai mu fidda kudi a hau aiki, Murmushi Hilal yayi zaiyi magana Irfan ya faďo parlon babu ko sallama, kusa da Sheik yaje ya zauna haďe da faďin "Masa'ul khair Aby, kallonshi yayi sama da kasa yace "uhummm, kudin naka sun kare kenan, sosa keya yayi yana hararar Hilal yace "Eh, akwai wani business da nasa kudi na, inaso inyi clearing ne bani da cikon kudin, 20mill ne kawai, "I struggle to get 5 thousands aday nd u are calling 20mil only, it's well dear, zanyi maka addu'a Allah ya baka, Lokacin da na kiraka ina farin cikin ganin yan uwana kaima kazo su ganka kazo? Kayi ignoring dina so yanzu ni bani da abun yi maka, yana kaiwa nan ya kalli Hilal yace "My dear gobe ka sameni a office sai mu fara shirye shirye ko? Cike da girmamawa Hilal yace "Okay sir, Allah ya kaimu... A tare suka mike Sheik ya raka Hilal har kasa sannan ya wuce dakin da Husna take dan duba lafiyarsu... Rike gaban rigarshi yayi saboda jin shakun da akayi mishi ta baya, yana da tabbacin Irfan ne dan irin kamshin turarenshi ne ya cika gurin, ganin yana daďa tamke shakan yasa Hilal yanka rigarshi ta gaba saboda ta kama wuyanshi sosai, iya karfinshi ya sanya ya cire hannun Irfan haďe da hankaďa shi baya. Taba wuyanshi yayi yana tari kaďan, saurin rike hannunshi yayi dan kare kanshi murya a kausashe yace "Wai menene? Fisge hannun Irfan yayi ya nuna shi da yatsa.. warning mai karfi ya karta mishi na kar ya sake taka kafarshi cikin gidannan in ba haka ba wallahi sai yayi ajalinsa, Dariya Hilal yayi yana gyara singlet dinshi zaiyi magana yaji muryar Maleekah a bayanshi, "Hey akan ka yake? In yazo gidan nan gurinka yazo? Kayi aikin gabanka ka bar kowa yayi nashi tunda gidan ba naka bane kai kaďai! Cikin zafin nama ya shako wuyanta dama yana da cikinta na yadda yake ganin an barta tana facaka da kuďi ba tare da an sa mata ido ba, sakin keyn motarta tayi saboda azaba tasa hannu tana kakari, Hannu Hilal yasa ya banbareshi a jikinta haďe da shake mishi nashi wuyan da karfi, naushi mai karfi Irfan ya sakarwa Hilal a ciki da gwiwar hannunshi, da sauri ya sakeshi ya durkushe rike da cikin saboda azaba, gaba daya jikinshi ya dau rawa dan jin ciwon yake har tsakiyar kanshi, ihuu Maleekah ta saki tayo kanshi ta hankaďe Irfan dake kara tattaka cikin Hilal, girman gidan baisa kowa yaji ihun ba sai maigadi, lokacin da ya iso har Hilal ya gama fita hayyacinshi, cikin kuka tace ma mai gadin ya kira Abbu, a ruďe ya

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156