Chapter 62
Chapter 62
Ya Musaddiq.. Daddy yana kiranka, Husnah ta fadi tana ajiye wayar da Daddy yayi kiranta, maida kan Nadeeyah kan pillo yayi, ya sauka suka fita a dakin tare da Anty Raly domin kaiwa baki abin ci da sha... "Baki da karfi dama kika fara *Soyayya* dagowa tayi ta kalleshi, tsareta yayi da ido kamar bashi yayi maganar ba, "ni bana soyayya, ta fadi hade da rufe fuskarta da hijab dinta, faduwar gabanta ya karu sosai, nade belt din hannunshi yayi yace "in ma kinada niyyar farawa gara in tuna miki, kije ki koyi fada, dan in baki da karfi zaki cutu a soyayya, ko tsoron maza bakya ji kin wani tsaya gab dashi, to da bamu zo gurin ba me zai faru kenan? Shi--- runtse idonshi yayi maganar ta makale a makoshinshi, a zuciyarshi yana neman tsari da shedan dake kawata mishi abubuwa marasa kyau, canza maganar yayi da cewa "wuyan baya miki zafi, in yana miki zafi kiyi magana a kaiki asibiti, "Murya can kasan makoshi tace "zai daina in shaa Allah, yana yi kadan kadan, Dauko waya yayi a aljihunshi ya danna number Hinad, tayi ringing sau biyu, a na uku ta dauka, "ina Zee,? jin ya ambaci sunan Zainab yasa ta mikewa zaune, "bata nan ya Hilal, sun fita da *Anty Mee*, kashe wayar yayi ya kira Meerah taki dagawa, wayar na katsewa tata ta shigo, video call, tsaki yaja ya dauka, "Hi dear, ta fadi tana daga mishi hannu, "Hello Meerah kina lafiya? Kamar yadda ka gani am very ok, but am missing yha, ta fadi a shagwabe, kauda zancen yayi ta hanyar tambayarta "where is Zee? Juya wayar tayi zuwa gurin Su Adeel cikin muryarta mai dadi tace "say Hi to Ya Hilal, fitowa tayi a cikin motar wasan yara ta bude hannu hade da cewa "oyoyo! Murmushi yayi yace "yawo, kika fita yawo baki fada min ba, nt good baby, karbar wayar tayi ta bata fuska tace "wayau zaka min ko, dan kaga na hakura bana kuka har yanzu, ka gudu ka barni baka kaini gurin Adda na ba, Tun Nadeeyah na rike murnarta najin muryar gudan jininta, har ta kasa tayi saurin zuwa gurinshi zata karbi wayar, hada ido sukayi tayi saurin maida hannunta, dariyar da bata fito fili ba yayi, sannan ya mika mata wayar, da sauri ta karba sukayi ido da ido da abar kaunarta, safa da marwa ta shiga yi suna hira cikin farin ciki harda yar kwallarsu, murnar ganin yadda zainab ta koma ya hanata sukuni ta dinga yi mata tambayoyi, sun fi minti bakwai suna hira sannan tace "ga Anty Mee ku gaisa, tana kula damu sosai ni da Ya Hilal, kallon juna suka yi na seconds kafin Nadeeyah ta saki murmushi tace "ina wuni, amsawa tayi itama tana mata musayar murmushi, yadda take jin sunan Nadeeyah a bakin Hilal ya tabbatar mata da lallai ganin da tayi mata yafi jinta, domin duk kushen mai kushe bai isa ya nemo aibun Nadeeyah ba, kyawunta na musamman ne, gashin da yayi kwance a gefen farar fuskarta su sukara kara kawata kyawunta, gashi in tayi murmushi ko dariya gefen kumatunta daya ke lotsawa can ciki, haka nan Meerah taji wani abu ya darsu a cikin zuciyarta, ita kanta Nadeeyah da bata cika lura da abu ko sanyashi a ranta ba taji wani abu kadan game da Meerah, kallon farko da sukayi wa juna dukkansu suka fahimci jininsu yayi nisa gurin haduwa, shurun da sukayi suna kallon juna ya sanya Zainab karbar wayar suka cigaba da hira, Tunanin inda ta taba ganin Nadeeyah meerah ta shiga yi, dakyar ta iya tunano sketch din da yayi a school as assignment, duk da wancan da dan yarinta sosai amma ta gane ita ce, lokacin duk wanda ya tambayeshi sai ya amsa cikin shakiyanci yace "My dream girl, a mafarki na na hadu da ita shine kamanninta suka mannu a zuciyata, nan da nan kamannin Meerah suka canza, zufa ta fara karyo mata tace "Zee bani wayar nan, mika mata tayi ta zauna kusa da ita, "Bani Hilal pls, tace ma Nadeeyah fuskar ta babu yabo babu fallasa, sai a lokacin Nadeeyah ta waigo ta kalleshi dan ta manta ma yana dakin, juyar da wayar tayi inda ake iya ganinshi ba tare da ta sani ba ta sunkui da kanta kasa, wani irin kallo Meerah ta hangoshi yana yi ma Nadeeyah wanda bata taba sanin ya iyashi ba, lokacin da ta mika mishi wayar bai kalleta ba ya fara kokarin kasheta, da sauri Meerah tace "Kangiwa kana ji na? "Yes Meerah Turaki ina jinki, yadda ya kirata ya tabbatar mata yana cikin shauki, "ina kabar Musaddiq, ta fada tana jin wani mugun kishi a cikin zuciyarta, sai a lokacin ma ya tuna da Musaddiq yace "auchh yana daki may be, ko Daddy ya aikeshi, bari in dubo shi will call u, ya katse wayar kafin ma ta sake magana, Yana kashe wayar Husnah ta shigo dakin da gudu tana kiran Sunan Nadeeyah, Hijab ta mika mata tace "yi sauri kisa, kallon Hilal tayi tace "my PP, zo muje kaga wani abun al'ajabi, Maida wayarshi cikin aljihu yayi ya bi bayansu dan ganin abun da zata nuna mishi... Ga Nadeeyahn nan.... Daddy ya fadi yana murmushin jin dadi, Allah kadai yasan irin farin cikin da yake ciki, gani yakeyi kamar da ita kanta Suwaibar yake zaune, gefe Nadeeyah ta tsuguna tace "ina wuni, Hannu Papy ya bude mata alamar ta iso gareshi, kalle kalle ta shiga yi suka hada ido da Hafeez ya gyada mata kai yana murmushi, mikewa tayi ta isa gabanshi tana mai mamakin kamannin, tsugunawa tazo yi yayi saurin dagota ya rungumeta, kukan da yake kokarin boyewa yaki boyuwa saida ya zubda su, Damke Hannun Hilal dake yunkurin zuwa gurin Husnah tayi tace "Babanta ne fa, twins din Mama Suwaiba, cikin rashin fahimta yace "what, ba Baffa yace ya mutu ba, Baffa dake zaune ya jiyo Hilal yace "muma duk haka muka dauka Muntari, ashe yana nan da ranshi, kaddarar da ta boye mana shi ita ta sake hadamu dashi, kallon Nadeeyah da ta kasa sakin jiki har lokacin Baffa yayi yace "saki jikinki, wannan uwa yake a gurinki, haka uba, domin tare suka zo duniya da Mahaifiyarki, kallonshi tayi sosai dan ta gasgata maganarshi, tun daga hannayenshi har kafarshi saida ta kare musu kallon, kyawawan yatsun kafarshi da ya zamto irin na Mamma da nata shi ya tabbatar mata da maganar Baffa, wata irin runguma ta sake yi mishi tana kuka sosai a zuciyarta tana jero alhamdulillah, ta kusa minti uku a jikinshi tana tunano rayuwar da sukayi da Mamma, ji takeyi kamar dawo da ita Allah yayi cikin wata suffar, saukowa a jikin Mami Ruwaidah tayi ta kama hijab din Nadeeyah tace "let my Papy be, karki bata mishi kaya da hawayenki, Papy na baya son kuka, dagashi tayi ta fara shafa fuskar Ruwaidah hade da rungumeta, duk rashin son mutanen Ruwaidah ta kasa nuna shi ga Nadeeyah, sai ma ce mata da tayi, "ki daina kuka mana, na fada miki Papy baya son kuka, ko so kikeyi yasa Yaya Jamal ya daura ki a bayan *OBENIZA* Dariya Hafeez da Jamal suka saki dan sunsan ta da mugun tsoron obeniza,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156