Skip to content

Chapter 18

Chapter 18

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

shige bayi, Husnah ta turnube fuska tace "wani Hafeez din, Anty Raudha tace "Hafeez din mama Suwaiba mana, kaff ta kwashe labarin abinda ya faru ta fadawa Husna suka karashe da dariya dukkaninsu, Badariyya tayi tsaki mai karfi tace "da an hadasu din, da zaifi mana alkhairi walhy, domin zuwansu nan din gaskiya akwai matsala, bama mai yiwuwa bane zamansu anan!! ta karasa fadi a gadarance, "Saboda kece mai gidan ko, Raliya da shigowarta kenan ta fadi tana harararta, Raudha tayi tsaki tace "nima zamansu anan din walhy bana sanshi, ni fa Allah ya sani na tsani talaka, ko sunan talauci banasan ji, Radiya daga bayi ta dago murya tace "ai talauci masifa ne, ni na rasa laifin me talaka yayiwa Allah, subhanallahi!!! Raliya tayi saurin cewa, ya salam, ku kuwa kuji tsoron Allah, talaucin nan fa wadanda suke cikinsa basu suka sawa kansu ba, kuma basu isa su cireshi ba sai Allah yaso, haka zalika arzikin da kuke ciki baku kuka bawa kanku ba, babu banbanci tsakaninmu, tunda duk abinda da talaka zaiyi mai kudi ma zaiyi, wadatar zuci tafi komai a rayuwa, suma Allah bai mance dasu ba, kuyi fatan kar Allah ya jarbceku da dandana rayuwar talauc----- "" eeeeeeh eeeh wait hang it, Radiya tayi saurin katseta, " har abada bazamu taba dandanawa ba "idiotic being, saboda muna sharhi kan talauci shine zaki rabashi jikinmu, to we reject it walhy, sakarai kawai,, uhmmm kawai Raliya tace ta fita tana mamakinsu, har ta kure dakin bata daina jiyo muryoyinsu ba.... Har karfe biyar na yamma Nadeeyah na zaune a inda take, da himilin kayansu, anan taci abincin da me aikinsu ta zubo mata, tana kallon dukkan ahalin mummy a cikin parlon ana hira, Anty Reemah ce kawai bata cikinsu, dan ita tun zuwansu suka wuce can gidansu ita dasu Hinad, ba yadda Hinad batayi tazo su tafi ba taki, kwanciyar hankalinta daya zainab ta bisu shiyasa ma zaman bai gundureta ba, gyangyadi ta farayi a zaune ta jiyo muryar Badariyya tana zuba rashin kunya tana fadin "wallahi mummy indai yarinyar can zata zauna a gidan nan ni bazan zauna ba, saidai ku zabi daya, janyota mummy tayi jikinta tace "haba baby, kiyi hakuri mana, dalili ne yasa zata zauna, kiyi hakuri pls na lokaci ne, kuma kinga makaranta zata koma, ba ganinta zaki dinga yi kullum ba, Keyn mota Raliya ta dauka a kan center table, ta dauki danta tace "Mummy sai anjimanku, tayi hanyar waje ba tare da ta jira amsarsu ba, badan a karkashin wani take ba, wallhy babu abinda zai hanata tafiya da Nadeeyah, mutuwa mai tonan asiri, duk talaucinsu basa zuwa gurinsu maula, rikon na Nadeeyah nawa yake? abinci ne fa kadai sai gurin kwanciya, sai dan kyautatawar yau da kullum, share kwallar idonta tayi ta shiga motar tana fadin, "ya Allah ka raya mu cikin ya'yanmu.... Dakyar mummy ta shawo kan Badar ta yarda, da sharadin a dakin mai aikinsu Nadeeyah zata zauna, dan ita sam bazata iya hada daki da Nadeeyah ba, dan a samu kwanciyar hankali mummy ta yarda amma can cikin ranta badan taso ba, Husna ma abin ya mata zafi sosai, Raudha da Radiya kuwa tsaff suka goyi bayan Badar... Dakin mai aikin nasu ma da d'an kyanshi, kayanta kawai ta shigar ciki ta fada bayi, sai da tayi kuka mai isarta sannan tayi wanka ta daura alwala ta fito... A inda ta idar da sallar ishaa bacci yayi gaba da ita, sai ajiyar zuciya take cikin baccinta, mai aikin nasu yar dattijuwa ce, taji tausayinta matuka, ta kuma yi tirr da hali irin nasu mummy, masu yin watsi da jininsu saboda talauci, tashinta tayi ta maida ita kan gado taja mata abun rufa...... Mrs Tijjani Shattima........! [07/03 6:31 AM] fareedah: ●ZUMUNCINMU A YAU● 1⃣8⃣ By Aysha Ya'u Kurah Tsakurar abincin dake gabanta takeyi tana juya cokalin, ta rasa menene asalin abinda take ji cikin ranta, farin cikin sanin halin da Nadeeyah ke ciki na rashin iyayenta takeyi ko kuwa bakin cikin tarewar da kowa yayi a gidansu Nadeeyan, Mutuwar mamma na iskarta tayi murmushin farin ciki, tasan Nadeeyah na can cikin radadin da ta sanya ta, saidai takaicinta daya musaddiq sam baya yarda su hadu, duk wata kafa da zata sadasu ya tosheta, dan sam baya son jin ko muryarta, wani irin tsanarta yakeji a zuciyarshi na rashin imaninta, babu wanda bai ziyarci gidan mutuwar ba sai ita, kullum tana zaune a gida daga kallo sai cin abinci sai game, babu yadda mummy batayi ba akan tazo gidan mutuwar tun farkon yin ta, amma sam taki zuwa, gashi wata mutuwar ta sake bullo kai... Tura abincin gefe tayi ta mike ta wuce daki dan ta watsa ruwa, ita kadai ta kwana a gidan, sai daddy da taji tashin motarshi da asuba tasan shima a gidan ya kwana, ko gezau bata ji ba a zuciyarta bare ta karaya ta shirya zuwa gidan su Nadeeyan, ita sam bata san zafin mutuwa ba, a ganinta kuncin da Nadeeyah ta sanyata yafi zafi akan radadin mutuwa, tsaki taja hade da wurgi da kayan jikinta ta fada bayi...... *********** Bayan doguwar addu'ar da aka gabatar a kofar gidan malam Adamu na sadakar ukun mamma Suwaiba, sadakar abinci akayi sosai, duk wanda yake gurin saida ya wadatu da abinci saboda yawanshi, cikin kankanin lokaci jama'a suka watse ya rage saura makusanta kawai, Baffa da shock din mutuwar bai sakeshi ba har lokacin ya mike kamar ba laka a jikinshi ya shige cikin gidan, Saida ya zauna yana maida numfashi sannan ya dubi gurin da mummy da Goggo ke magana, fada mummy keyi akan rashin zuwan Badariyya, ita kuwa goggo goyon bayan Badariyya take hade da fadin "kinsan yarinya ce kuma bata san hayaniya, duk mu da muka zauna a gidan har kwana uku bamu wakilceta ba, Baffa dai kallonsu yakeyi zuciyarshi na tafasa amma bakinshi yayi nauyi ya gaza furta koda kalma daya ce, Hinad dake zaune can gefe kusa da Nadeeyah ya yafito da hannu alamar tazo, da sauri ta karaso gabanshi tace gani Baffa, cikin murya mai rauni yace, taje ta kira Hafeezu da Daddy a waje, sai a sannan mummy tasan da shigowarshi, karasowa tayi ta zauna kusa dashi tace "Baffa yaushe ka shigo, murmushin yake yayi yace "yanzun nan, tafi ki kirawo min dukkan ya'yanki akwai maganar da nake so muyi daku, kai ta gyada tace "to Baffa, ta mike ta fita tsakar gidan, Zama Goggo tayi tana matsa mishi hannu hade da cewa duk kwana ukun nan baka da wani kuzari, mutuwar nan fa ba a kanta aka fara yi maka ba, ka rasa uwa, uba, mata, da ya'ya, saidai wannan mutuwar na lura tafi razana ka, wanda ni bansan dalili ba, mutuwa daya ce, in mutum yayi ta baya dawowa, inda ana dawowa sai ince ka cigaba da damuwar, watakil damuwar taka na iya dawo da ita, ya kamata ka sanya wa kanka nutsuwa kayi tawakkali, Hawayen da ya zubo a gefen idonshi ya share zuciyarshi na rawa yace "Asama'u! duk mutuwar da akemin ta Suwaiba tafi tsaya min, kinfi kowa sanin hal---- da sauri ya dauke idonshi cikin nata, ya kauda kanshi ya canza maganar da cewa "ina matukar tausayin halin da yaran nan zasu shiga ne,

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156