Skip to content

Chapter 21

Chapter 21

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

suna ta maganganu cikin fushin rashin ganinta, muryar shaho ya jiyo daga can yana fadin "babu abinda zai hanashi kasheta in ya ganta, da yaso ya sameta yayi yadda yake so da ita amma yanzu kasheta zaiyi dan in ya barta zata iya zama barazana ga rayuwarshi, jin haka yasa Baffa cikin tashin hankali yayi saurin komawa cikin gidan, A kofar sakarkari ya samu ma'u zaune tana damun fura da nono, ganin da tayi ya shigo a firgice yasa ta mikewa ta nufo shi, "lafiya?, ta tambaya tana kallon yadda jikinshi yake rawa, daki ya jata yace "ina bakuwar balarabiyar nan, maza fito da ita mu nemi wani gurin mu korata dan walhy rayuwarmu tana cikin hatsari, ya kwashe duk abin da yaji shaho ya fadi ya gaya mata, cikin dakiya irin tata da jarumta tace babu inda zaka kaita in ba iyayenta ne suka zo neman ta ba, ya zama dole a samu me tsawatarwa shaho, abubuwan da yakeyi a cikin garin nan ya isa haka, kallonta yayi galala yace "wa kike ganin zai tsawatar mishi?, ki fada min wake da wannan zarrar? kwaryar damunta ta dauko tace "nidai na fada maka babu inda zata, ta wuce daki tana tsuma tana fadin babu wanda ya isa ya taba makka, "sunan da ta rada mata kenan tun kafin taji sunanta, ita zuciyarta ta tafi can tunanin in iyayenta suka zo to fa zasu musu alherin ganin sun taimaki yarsu, kuma zata kafa tarihin ita ta fara taba jikin balarabiya a duk fadin tsirarun musulman da suka musulunta a kauyen, cire kayan tayi ta dago yayin ta fito da ita tace "sannu hai yar budurwa, fito muje ki sha fura sai kiyi wanka, raba dara daran idanuwanta ta fara yi dan ko kalma daya bata dauka cikin kalaman ma'u ba, hannunta ta riko suka fito waje ta shimfida mata sabuwar tabarma ta nuna mata tace "zauna, bata fahimta ba haka ta kuma kama hannunta ta zaunar da ita, furar ta mika mata ta dauka ta fara sha hawaye na zirarowa daga cikin idanuwanta, tunanin kaninta takeyi dan shekara 6 a duniya wanda ta zamo gata a gareshi gaba da baya, ko a wani hali yake yanzu Allah masani, ludayi uku tayi ta miko ma ma'u.. Amsar kwaryar tayi tana fadin "hai har kin koshi, da kin kara kadan ta fadi tana miko mata, Girgiza kai tayi saboda ta fahimci nufinta tace "Alhamdillah, Jazakumullah khairan" yashe hakori Ma'u tayi tana dariya har can cikinta tana kyakyato shi, dariyar murnan jin yaren larabci, da kuma ganin ita kanta balarabiyar makkan a gidanta takeyi, saida ta gama dariyarta tace "hai Baffan Boddo an je gidan kawu suwidi in fadowa su inna wuro munyi bakuwa mai tsarki yar Makkah, takalmin robarta ta janyo me ruwan bula tasa a kafarta, ta yayo dankwalin saka ta rufe kanta ta fara tafiya, ta kusa taba kofar Baffa yayi saurin tareta yace "A wala hakkilo na" ("baki da hankali ne?) Kinsan irin halin da zaki samu a ciki in kika gayyato mana mutanen gidan Kawu Suwidi?, kince bazata bar gidan nan ba na hakura ta zauna amma ki sani babu me shigo min gida bare ya ganta ya jaza min masifa, tana nan zaune nasan za'a zo cigiyarta a lokacin sai in mikata gurin iyayenta,, kalonshi ma'u tayi fuskar nan cike da gamsuwa tayi kamar ta yarda din da gaske, yaye dankwalin kanta tayi tace "Haka ne, na manta ne ina ta zumudin kai rahoto dan kawai in burge su inna wuro, yanzu bari inje in sata tayi wanka sai ta canza kaya a wanke na jikinta, gyada kai Baffa yayi cikin jin dadi ya koma daki kusa da yaranshi ya zauna yana shafa kan karamar dake kokarin tashi.. Murdaddiyar sarkar murjanin gwal din da ta cire kafin ta shiga wanka ma'u tayi ta juyawa a hannunta tana dariyar farin ciki, "Aiya Ya Allahn Hard'ejo, (sunan yayan mijinta kenan malamin da ya fara kawo musu musulunci kauyen), ji wani "kuje ndade' (sarka) kamar ba hannun mutum bane ya kerashi, sashi tayi a wuyanta tace "wannan ko matar Ardo Laminu bata da irinshi, kaii ya zame min dole in je gidan su inna wuro dan bazan bar wannan daddadan labari ya wuce ban basu shi ba, ai ni ko da wannan maka wuyar aka barni na tsira, daki tayi da sauri tana magana kamar zararra, kayanta dake cikin wani akwatin katako ta dauko sababbi na fulani tace " Baffa zan bata wannan kayan nawa tasa saboda a wanke wadancan, gyada mata kai kawai yayi dan mamakinta bai barshi ya bude baki yayi magana ba, ma'u da ko dankwalinta bata iya bawa wani aro shine har ta dauko kayanta da bata taba sasu ba zata bawa wata tasa, lallai yar makkah ta ciri tuta.. Sosai kayan fulanin suka mata kyau a jiki saboda tsabar kyawunta, lallausan gashinta ma'u ta shiga kitsashi da kyar tana yi yana warwarewa, haka dai tayi mata irin nasu na fulani ta dauko mata su sarka da abun hannu duk dan ta mantar da ita sarkar gwal dinta... Mrs Tijjani Shattima... [07/03 6:31 AM] fareedah: •• ZUMUNCINMU A YAU •• 2⃣1⃣ By Aysha Ya'u Kurah Hanyar sama Badariyya tayi da gudu tana shashshekar kuka kamar ranta zai fita, kofar dakin Daddy ta shiga bugawa kamar zata ballata, da gudu mummy ta fito daga bayi jiki na rawa ta bude kofar, Daddy kuwa zaune yayi yana jiran ganin me mishi irin wannan bugun kofar da safiyyar nan, jikin mummy Badar ta fado ta sake kecewa da wani kukan, waigawa tayi ta kalli Daddy da ya rike kanshi yana tsaki, waje ta jata ta rufo mishi kofar, ta kama hannunta sukayi dakin ta, zaunar da ita tayi a kan gado ta shiga rarrashinta, saida ta tabbatar ta fara samun nutusuwa sannan ta tambayeta abinda ya faru, karya ta shiga rerowa mummy cikin wani sabon kukan, "Ya Hilal ne yayi min dukan tsiya, wai saboda Nadeeyah taje tana wanke wanke kunama ta harbeta, shine yaje ya taso ni ina bacci wai tace mishi ni nasa ta, kuma tace mishi wai na hana a bata abinci jiya har tayi bacci, sannan a gabana Ya Musaddiq ya dauketa ya sata a mota suka kaita asibiti wai kafin su dawo in tabbatar na gama wanke wanken da ya rage------- , Wani irin kunci da tukuki mummy taji a ranta, "Hilal din ne ya dake ki? gyada kai Badar tayi wasu zafafan hawaye na sake bin kuncin ta, 'irin kallon da Musaddiq ke ma Nadeeyah shi ya fi komai taba zuciyarta, kwanciya tayi jikin mummy ta runtse idanuwanta saboda ganin hanun Musaddiq da takeyi cikin na Nadeeyah, "Hello Reemah, daga daya bangaren Anty Reemah ta bude idonta hankali tashe cikin muryar bacci tace "Na'am, ina kwana Mummy, ''lfy kadai mummý tace, ta cigaba, "kizo gida yanzu ina nemanki, bata jira amsarta ba ta kashe wayar.. Mikewa Anty Reemah tayi jiki a sanyaye, tasan akan matsalar Hilal akayi kiranta da safen nan, cikin zafi tace "wai wannan wani irin yaro ne da yakeson kashe ni tun lokaci na baiyi ba, wallhy yau, ko gobe zamu bar kasar nan kar ya jaza min bala'i, ina kokarin gamawa da mahaifiyata lafiya yana neman janyo min tsinuwa, Papa

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156