Chapter 78
Chapter 78
kuka kai min kayan daki? Tabdijam, wallahi hukuma ce kadai zata rabani daku, ashariyya ta fara kundumo musu babu kakkautawa, Muryar Papy tajiyo daga tsakar gidan yana sallama, fitowa tayi da sauri har tana tuntunbe, tana fitowa Baffa ya murda kofa ya fito yana amsa sallama, baki ta saki tana kallon yadda muhammadunta ya canza a cikin yan satittikan da ta tafi ta barshi, gaba daya an aske farin gashin dake gemunshi da kanshi, tsufanshi ya boye sai wani annurin kyau da yake fitarwa, Bugaggiyar shadda blue ce a jikinshi sai hula da takalmi masu matukar kyau, ga wani uban kamshin turare da yake fitarwa, duk su biyun ta kalla taga kayan nasu iri daya har dinkin ma, bata kara shan mamaki ba sai da jiyo sallamar Daddy, kallon hanyar shigowar tayi taga ya shigo da danyar gezna ash, bayanshi Musaddiq, Hafeez da Jamal ne suma sunyi kyau sosai, *Zuri'ar Atika* ta fadi a hankali, wata juya ta fara ji wacce ta sanyata yin zaman dirshan, Papy ne ya fara isa gareta yana fadin "subhannallah, Inna lafiya? ina kika tafi har wannan lokacin kika barmu da jimami, bata iya yin magana ba sai kukan takaicin da ya kufce mata, taruwa sukayi akanta harda Baffa suna mata sannu, dan yanayinta na marasa lafiya ne, dakin waje suka shiga da ita Baffa ya tsaya a kanta yana mata tambayoyin inda ta shiga, kureshi da ido tayi alamar tuhuma, ga mamakinta murmushi yayi kamar yaro karami, haibarshi ta lokacin samartaka ta tariyo kanta, shi ma ita din yake kallo amma fa a tsorace yake dan yana tsoron abun da zai canza ra'ayinshi akan auren nan, dan kwanakin da ya jera yana haduwa da Anni yaji tayi matukar kwanta mishi a rai, yana fatan suyi zaman tare har mai rabawa ta raba, "Biki akeyi na ganka da sababbin kaya? yadda ta jefo tambayar sai ta bawa mai kallonta tausayi, "Gyada kai yayi yace "eh bikin Muhammadu da Hanne, agogon bango ya kalla yace "goma daidai za'a daura, yanzu tara da rabi, bari muyi saurin zuwa gurin, akwai kayan abinci a cikin drawer can kiyi kokari kici kafin mu dawo, sai ki fada min inda kika je kuma da izinin wa, *IZINI* Goggo ta maimaita kamar me koyon magana, yana gab da fita tayi karfi da jikinta ta damki babbar rigarshi hade da fadin "wallahi babu inda zaka, kai baka isa ka wulakanta ni ba Muhammadu, ko kunya bakaji, banda jika har tattaba kunni gareka amma dan budurwar zuciya irin taka harda yin anko kai a dole zaka angance, to wallhi saidai in ka kasheni ka ka fita, saboda rashin kuzarin da take ciki yasa shi kwace rigar yace "Raya sunnar ne abin kunya, bazan kasheki ba, kuma aure babu fashi mutuwa ka raba, yana kaiwa nan yasa kai ya fice, "aiko zaku mutu, wallahi tallahi kaji rantsuwar da bata da kaff------ ido cikin idon da sukayi da Daddy ne ya hanata karasa mummunan furucinta, ciki ta juya hawayen ido suka kafe sai na zuci da suka dinga kara kaini, kasa zaune tayi tanata safa da marwa tana tunanin ta inda ta kuskuro har wadannan abubuwan suka cakude mata haka, ga kayan dakinta duk an fitar dasu bare ta samo wasu cikin surkullenta tayi amfani dashi, dakyar ta zauna tana maida numfashi kamar zata mutu...... Foiling naman walima Nadeeyah da Husnah sukeyi a cikin tray suna hira, Mummy na bayansu tana hada coleslaw na dole dan ba yadda zatayi Daddy ya dauki nauyin walimar a gidanshi, suna gamawa suka jere komai a inda ya dace, rissinawa Nadeeyah tayi tace "Mummy akwai wani abun ne? gyada tayi kawai alamar a'a kamar me ciwon baki, Daki suka wuce dan yin wanka, kaya kala daya Papy ya dinka musu harda su Anty Raly, lace ne dark purple mai ratsin manyan pattern pink flower, dinkin riga da skirt mai matukar kyau, ko ina an sanya farin stones wanda ya kara kayata lace din, *Bismid cream* Husna ta dauko tana shafawa tana dariya, wayaga Baffa ango, wallahi ni abun kunya ma yake bani, su Daddy kuma harda wani daurewa karya ...... wai harda walima, dariya Nadeeyah tayi hade da jan zip din rigarta tace "ni kaina abun jinshi nake wani iri, saidai ba yadda za'ayi da hukuncin Allah, Badar sarkin nukufurci tana kwance cikin bargo tana latsa waya bata ma san suna shiri ba, light make up sukayi wanda ya dace da fatarsu, sunyi kyau sosai saboda lace din kalar farare ne, dauri sukayi mai matukar kyau iri daya suka feshe jikinsu da turaruka masu kamshi da saukin karfi, kara wayar Nadeeyah tayi alamar shigowar sako, da sauri ta dauka dan tasan wanda yayi text din, "baya kiranta a waya, amma text duk minti biyar yinsa yakeyi, ko ya rasa abin cewa sai ya nemo write up na yaudarar maza, ko yadda zata kula da kanta, ko adduoi ya tura mata, reply dinta koda kalma daya ce means the world to him, *Yunwaaaaaaaa, plss ku kawo min abinci kar in mutu*..... Dariya sosai tayi dan ganin mai sakon, ta mikawa Husna wayar, itama dariyar tayi tace acici, kinsan yau ya tashi da wuri to fa kowa ya bani a gidannan, flat shoe suka saka suka wuce kitchen, flask Nadeeyah ta dauka da hot chocolate da ta san yafi san karyawa dashi, ita kuma Husnah ta dibi naman kaza cikin pepper din da sukayi foiling, wani sakon ne ya sake shigowa.. *Nadeeyah so kikeyi in mutu ko, ba komai... ya sanyo alamar kuka* Reply tayi mishi tana murmushi tace *Sorry, kana ina ne* Yana ganin reply din yayi saurin kiranta "ina BQ, yanzu muka dawo, plss kiyi sauri cikina na ta kiran sunanki, yasan ke kadai zaki taimaka, kashe wayar tayi tana dariya suka wuce BQ din, Murda kofar Husna tayi saboda ita ke da rangwamen kaya a hannu, karo tayi da mutum shima ya sako kai zai fito, subhanallah ta fadi hade ja baya tana kallon tray din da ya fadi kasa, kallon shi tayi taga shaddarshi ta baci da source "Ya salam.. Ya Hafeez dan Allah kayi hakuri, wallhy bansan zaka fito ba, Murmushi yayi yace "haba karki damu, da kinsani bazaki shigo ba nasani, ke da gaisuwa ma sai na roka, yaushe zakiso kiyi karo dani, dariya tayi sosai tace "kiji sharri Nadeeyah, bari in duba maka kayan Ya Musaddiq ka canza, "inyi yawo dai a ciki ya fadi yana goge jikinshi hade da kallon Musaddiq da yayi fuskar tausayi, dariya yayi ya kalli Nadeeyah yace "saura kiris a zare ran fa, maza kije ki bashi break fast.. Da sauri ta zare takalmin kafarta ta shiga da sallama tana fadin "sorry pls, rike cikin yayi ya kara bata fuska yace "naki sorryn na koshi, bude flask din tayi ta zuba ruwan zafi ta hada mishi tace "gashi kayi hakuri dan Allah kar a zare ran, in aka zare bamu san inda zamu sa kanmu ba, "Dadi zakuji mana ku huta da acici, sosai sukayi dariya Nadeeyah ta gimtse tata dariyar tace "ai ci dole ne yayana, kowa ma acici ne, gashi kaji, plssssss, ta fadi tana karkace kai gefe, "badan ni zansha ba sai dan tausayin hanjin cikina, Saboda dariya saida Nadeeyah ta durkushe a gurin, "dan Allah
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156