Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

kuma babu Mai hanasu, daukar zainab tayi ta bi bayan mamma suka fita hade da rufe gidan... Gidan cike yake da 'yayan kawayen mummy da iyayensu da ita kanta, suna can ciki anata wasa da ciye ciye, iyayen kuma suna hira hade da Shewa, can gefe kuwa su Reemah ne ita kannenta sunata hira babu Wanda ya lura da zuwansu, hakan ya ba Nadiya daman zama can nesa dasu tana kallon yaran dake dakin 'ya'yan hutu kawayen su badariyya, zainab da hankalinta ya gama tashi da tulin kayan wasan yara sa'aninta ta mike a jikin Nadiya tace anty zanyi wasa, Nadiya ta zaunar da ita tace ki bari su gama kema sai kiyi kinji, gyada kanta tayi tanata binsu da ido suna wasa babu kakkautawa, Mamma kuwa tana can gurin su goggo da mummy da kawayenta sunata hira, tunda ta gaishesu ta nemi guri ta zauna a kasa itama, babu Wanda yace musu ga abinci haka in za'a ba yara barka da sallah babu wanda ke kallonsu, sallah kadai ke tada iyayen Sannan su dawo su cigaba da hira, "Suwaiba tashi ki tattara gidan nan tunda baki San abinda ya kamata ba sai an fada, muryar goggo ta dakin kunnen daukacin mutanen dake cikin parlorn, da sauri mamma ta mike tana murmushi ta fara tattare kwanukan da suka ci abinci, kwala Kiran Nadiya tayi tace taho ki fitar min da kwanukan nan, zaunar da zainab tayi ta mike sum sum ta karbi kwanukan hannun mamma tayi waje dasu, Badariyya dake kwance tana game a iPad dinta ta bita da ido cike da rainin wayau, tsaki taja ta cigaba da danna iPad dinta, ta rasa dalilin dayasa ta tsani Nadiya, bata jin ko digon kwayar Santa a cikin zuciyarta, tasan tafi Nadiya dukkan gatan rayuwa, haka kyau karyarta ta nuna mata, can kasan zuciyarta ta jiyo yayi amsar kuwwar "KYAWUN JIKIN FA" tsaki taja tace saidai jikin Shima dan bamu gama girma bane amma Nadiya babu abin da ta fini dashi, Husna da Laila yar kawar mummy suka bita da kallon mamaki sukace to waye ya ce Nadiya tafi ki wani abu, gimtse fuska tayi hade da runtsa ido dan bata San maganar zuci ta fito fili ba, A ranar babu wani abu da ya shiga tsakaninta da badariyya saboda Hilal da yayi kaka gida a parlorn, Kasa katabus tayi saboda tsoron Kar ya sake marin kyakykyawar fuskarta, ta tsani abin da zai taba fatarta koda kuwa kuda ne,, Yaji mamma tayi ma Reemah da yawa na tafiya sannan tayi ma musaddiq dambun kifi da nama, murna sosai sukayi sunata godiya, sai bayan Isha mamma ta fara shirin tafiya, dakin Baffa ta shiga Wanda yake cike da 'ya'yan mummy da ita kanta suna meeting ana ciye ciye, durkusawa tayi tace Baffa mu zamu tafi sai da safe, to madalla sai da safe suwaiba, yaki taho zainabu ki karbi kudin mota, nokewa zainab tayi saboda rashin Sabo, mamma tayi murmushi tace "quiwa gareta, , toooo... to ta rike kanta ta cinye, sai Allah ya tashe mu ki gaida Adamun, to zaiji Baffa, ta waiga tace masu sai da safenku, to sai da safe duk sukace suna masu kai nama bakinsu.. Reemah dai kai kawai take girgizawa cike da takaici, yafito Hilal tayi da hannu tace maza yaje ya sauke su a gida, kunkuni ya fara yi yana buga kafa, musaddiq ya mike yace bani mukullin, da sauri ya wurga masa ya koma ya zauna ya cigaba da latsa wayarshi, a can bakin gate ya tarar dasu suna kokarin fita, Mota ya bude yayi musu hon yaja ya isa gaban su, bude musu yayi yace mamma muje in kaiku,, ayi haka.... mamma ta fadi tana rike baki, bakomai ku shiga muje, baya suka shiga ya ja motar suka wuce.... ******** Tun daren suka gama shirye shiryen komai na tafiya, ba kananan kudade daddyn shi ya turo na siyayyar tafiyarshi ba, mummy da kanta ta shirya mishi kaya suna ta hira cikin farin ciki, Yaya wata nawa zakayi? Husna ta tambayeshi tana bude ledar dambun naman da mamma tayi mishi, mummy tayi dariya tace shekara nawa dai, ai sai kin ganshi kawai, Husna tace "tabdi har shekara anya mummy zai iya zama kuwa, shi da baya ko iya kwana a wani gari, shafa kanshi mummy tayi tace "can ma ai gida ne ko little? , gyada kai yayi ya kwanta kan cinyarta yace but I will miss you so much mummy, i will miss u more my baby, ka kwantar da hankalinka zan dinga zuwa ganin ka a kai kai kaji, um kawai yace yana kallon Badariyya dake mishi kallon shi din baida wayau, tsaki yaja ya mike ya nufi dakinshi, rainin Badariyya a gareshi yayi yawa, lallai taga gadon barcinshi amma babu komai with time Shima zai zama jajirtacce marar daukar raini in shaa Allah ya fadi yana mai karfafa zuciyarshi..... Mrs Tijjani Shattima.... [04/12 09:46] Meela Adeel: 9⃣ °ZUMUNCINMU A YAU ° By Aysha Ya'u Kurah HAPPY NEW YEAR, Allah yasa mun shigeta a sa'a AMEEN.... 2017 is unforgettable... Allah yayi Maka Rahama Babana... "Kilode sis"... Husna ta fadi tana zungurar Badariyya da tayi tagumi tana kallon Kasa, tsaki Badar ta ja tace "nothing bacci kawai nake ji, Husna ta tabe baki hade da kwanciya tace "to ai sai ki kwanta, Badar ta dan kashingida ta runtse ido kamar mai bacci, har cikin ranta bata son tafiyar Musaddiq, duk da yawan samun sabanin da sukeyi tafi son kasancewarshi kullum a gida tana mishi koda kallon raini da wulakancin da ta saba ne, to in ya tafi wa zata dinga gani, Husna tayi mata kadan a cewarta, duk da sa'oin juna ne amma a koda yaushe Badar gani takeyi ta girme ma Husna nesa ba kusa ba saboda tsantsar sangarta da d'agawa, tunanin hanyar da zata bi ta hanashi tafiya ta shiga yi, ta dade tana tufka da warwara kafin daga karshe ta samo mafita,.. a hankali ta Mike ta murda kofa ta fita , dakin mummy ta nufa dan tasan bata ciki tana can gurin musaddiq, drawers ta fara janyowa ta shiga binciken visan musaddiq da aka kawo mishi jiya, da kyar ta gano inda take cikin wata karamar jaka, dariyar farin ciki ta shiga yi a ranta tace zanga yadda za'ayi ya tafi ba wannan, hannu tasa zata fara yagawa taji an Fisge visan a hannunta, saurin waigawa tayi dan ganin ko waye, Husna ta gani tsaye tana kallonta cikin ido, "haba Badar yanzu muguntar taki har ta kai haka, meye amfanin yaga mishi visa,? tun fitar ki na biyo ki dan nasan ba fitar alkhairi kikayi ba, akwai abin da kike shirin kulawa da shurun da naga kinyi,, mtswwwwwwwww Badar taja dogon tsaki tace "dalla malama bani, ni nace miki yagawa zanyi, to me zakiyi dashi? husna ta tambaya fuskarta dauke da mamaki, ban sani ba Badar ta fadi tana mik'a hannu zata kwace, kaucewa husna tayi tace wallahi bazan baki ba, sai dai ki kwata ta karfin tsiya, nan suka fara kokawar da ya janyo hankalin su mummy, Kaiiii, kaiiii, lafiya menene haka, mummy ta fadi da karfi tana shiga tsakaninsu, Husna tasaki wahalalliyar ajiyar zuciya hade da haki tace mummy visar Yaya zata yaga, Visa kuma, to me

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156