Chapter 134
Chapter 134
da yaron, Cike da azama Musaddiq ya taro yaron da har lokacin bai farka daga baccin da yakeyi ba, rawa jikin saurayin ya fara yi cike da tsoro dan da yaron ya faďi ba karamin buguwa zaiyi ba, waya ma kenan da take bata da karfi ta tarwatse inaga rai, Kallon Musaddiq yayi wanda ya zubawa yaron ido suna kallon juna dan yana zuwa hannun Musaddiq ya buďe idonshi tangaran, dariya jinjirin yayi wa Musaddiq wanda ya sanya duka kumatunshi lotsawa, cike da kasala Musaddiq ya maida mishi dariyar haďe da taba kumatunshi, haka nan yaji son yaron na yawo cikin jininshi, matsowa saurayin yayi yana ma Musaddiq godiya haďe da sa hannu ya karbi jinjirin, kuka sosai jinjirin ya fashe dashi wanda a iya saninsu bai taba yin irinshi ba tun haihuwarshi, a ruďe saurayin ya fara jijjigashi yana hangen wani guri alamar neman mahaifiyar yaron, kuka sosai jinjirin yakeyi har yana shakewa, hawaye shabe shabe a rufaffen idonshi, har cikin rai Musaddiq ke jin kukan jinjirin, ganin yadda saurayin ke jijjigashi cikin rashin iyawa yasashi matsowa kusa ya mika hannu ya karbeshi, sanyashi yayi a kafaďa nan take gurin yayi tsitt sai alamar shakuwa da ajiyar zuciyar jinjirin, cike da mamaki dan saurayin yace "Lallai junior, wato nayi maka yaro da raino ko? Dariya Musaddiq yayi yace "Abun mamaki, ban sanshi ba amma ganin farko ya shiga raina, ya sunanshi? *Mukhtar amma Hi*------- "Amaaan.. da sauri ya katse maganar ya amshi junior yace "Sorry.. uncle dina na kirana, inaga zamu wuce ne, thanks alot, bin bayansu Musaddiq yayi dan keyn motarshi ya makale jikin showel din, tsayawa Aman yayi cike da mamaki yace "Any problem? Nuna mishi keyn yayi lokacin ya cireshi haďe da jan kumatun junior, "Bye Daddy, ka daina rigima kaji ko? yadda ya kaďa mishi keyn yasanya yaron sake yin dariyar da ta tsaya a ran Musaddiq, saida suka kurewa ganinshi sannan ne yayi ajiyar zuciya haďe da kokarin cire tunanin yaron a cikin zuciyarshi... Faďuwar da gabanshi yayi ne ya sanyashi faďin "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun... kamar an sake hura faďuwar gaban domin kuwa da sauri da sauri take harbawa kamar ana lugude, runtse idonshi yayi haďe da dafe kirjinshi, tunanin da yake kwana yi shi ya dawo mishi sabo fil kamar yau aka halitta shi a cikin zuciyarshi, Karar wucewar takalma ta bayanshi ya sanyashi buďe idon a hankali, kafin ya juyar da fuskarshi duk sun bi ta kofar sun shige sai Aman da shima ya bi bayansu, kamshin turarukansu da ya biye gurin shi ya sanya Musaddiq sake jingina da kujerar yana mai tsintar kanshi cikin shaukin da ya daďe bai shiga irinshi ba.... Saida jirgin yakai 45mins sannan ya sauka a wani kebabben guri saboda dama private ne, A gajiye likiss suka sauko kowa yana mika saboda zaman guri daya, Anty Reemah Musaddiq ya fara gani yayi saurin karasawa kusa da ita yana mata sannu da zuwa, Sakkowar Sheik ba karamin gigita Musaddiq tayi ba, bai dawo daga wannan shock din ba ya shiga wacce ta fishi, Maleekah ya hango kanta dauke da hular Hilal wacce ta cire suna gab da fitowa, "Kaga Nadeeyarka ko? Kunci ya kare, Papa ya faďi yana murmushi... Hmmm ya faďi cike da mamaki, "Mai kama da ita dai, Nadeeyah ba haka take ba, amma a ina kuka samo mai kama da ita, in ma kunyi haka ne dan hankalina ya kwanta in sake wani auren to ku sani ni da aure sai dai a lahira, yadda Nadeeyah ta gama aure ta tafi ta barni nima hakan zan je in sameta yadda ta barni.. Hannun Papa Anty Reemah ta kama haďe da girgiza mishi kai suka tsaya a gefe, cike da murna Hilal ya sauko ya rungume Musaddiq haďe da tambayarshi bayan rabuwa, Murmushin da dole uwar naki ta koya mishi shi ya sakar mishi haďe da tambayarshi su waye wadannan masu kama da su Mamma? "Hello broo, Ayyam Atika Ateek, a.k.a Maleekah, tsaki Hilal yayi haďe da cire hular kanta yayi gaba, "Salamu alaikum, nyc meeting u Atika, i am Musaddiq Kyari, Maida hannunta baya tayi dan yadda ya amsa mata sallamar ya burgeta, har kasa ya tsuguna ya gaida su Sheik, dagoshi Sheik yayi ya rungumeshi haďe da amsa gaisuwar, saida suka gaisa sosai sannan suka fita suka isa motar Musaddiq da wata da aka basu a airport din dan zurga zurga, har suka isa gida Musaddiq bai bar tambayarsu daga ina suka nemo dangin Mama suwaiba ba.... Cike da al'ajabi Daddy ya ke duban Sheik, "Ikon Allah kenan, to meyasa babu wanda ya nemeta? Murmushi sheik yayi yace "Kaddarar Zuri'a, a lokacin da labarin yazo mana ina da shekara shida a duniya, amma nakan tuna wasu abubuwan, Lokacin da labarin mutuwarta ya riski ummul bata tsaya tayi binciken komai ba, kamar jira takeyi ta tattara 'yayanta suka fita daga gidan da niyyar in ta koma tace harda ni aka kashe, wani yaron da muke wasa dashi *Husaimin* shi ya shigo ya tasheni yace "inyi sauri gashi can za'a gudu a barni, a lokacin ne yake faďa min cewa an kashe Habeebullah da yayata, da gudu nabi bayansu lokacin har sun hau amalanke sun fara tafiya, takalmina da ya cire na waiga zan dauko Husaimin yajani da tayar hannunshi mukayi gudu muka kamo su, dakyar na iya hawa saboda tsayin abun, ina hawa ummul ta fara yi min masifar borin kunya tana tambayata inda naje, ban bata amsa ba na tsugunar da kaina inata kukan rashin gatan da zan tarar, har muka isa inda zamu tsallaka ruwa ban daina kuka ba, muna zuwa muka samu wadanda zasu tsallaka zuwa Egypt, nan aka loda mu ciki muka fara tafiyar da ta kaimu washe gari cikin ruwa... Karya da gaskiya Ummul ta fadawa mahaifina har ta ce mishi an sallaceta a gabanta domin tasan bazai yarda da ita ba sai yasa an je an dubo ta, saboda tsabar bakin cikin rashin Atika mahaifina ya kamu da mummunan ciwon stroke wanda ya daukeshi shekara biyu yana yi kafin Allah ya dauki ranshi, gaba daya dukiyarshi ummul ta tattareta ita da yayanta ta maidani dan aikinsu, son zuciya yasa ta manta matsayina a gurinta, ta mance cewa inda mahaifiyarmu ta tafi itama zata je komi daren dadewa, gidan Sheik Al' Mannar abokin babana nan nake zuwa daukar karatu, ganin hazakata yasashi ya sanya ni a makarantar boko, daga can sai in wuce gurin da suke aikin gini in dinga koya ina samun na abinci, gaba daya kwanan gidanmu ya gagareni domin kwana nakeyi aiki bani da wani hutu, abinci ma ummul sai taga dama take bani a cewarta itama ba kudi gareta ba, duk wasu kadarori na mahaifinmu ta haďe ta siyar sun cinye kudin da 'yayanta... Muna da shekara sha takwass 'yaranta biyu sukayi wa wata yarinya fyaďe wanda hakan yayi sanadiyyar yi musu hukuncin da yayi ajalinsu, a lokacin ummul hauka ne kawai batayi ba domin saida tayi wata biyu a asibiti, ni nayi jinyarta saboda dayan yaronta an nemeshi an rasa ya gudu da ragowar kudin da ta ajiye, ashe shima smuggling din kwaya yakeyi, ranar da dubunshi ta cika aka kamashi ita ma a ranar rayuwarta tazo karshe saboda shock din fille mishi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156