Chapter 3
Chapter 3
na manta inda kika aikeni dashi, karki damu gobe in shaa Allah da wuri zan kai mata, kika ce gidanta na kusa da gidan mama suwaiba ko? Wani mugun kallo ta bishi dashi had'e da taune leb'enta, matsawa baya ya fara yi dan yasan in mummy ta fara taune leb'e to abin da zai biyo baya bazaiyi kyau ba, dai dai kofa ya tsaya kamar zaiyi kuka "yace mummy kiyi hakuri dan Allah, cike da takaici tace "Musaddiq Anya rayuwar da ka daukarwa kanka Mai b'illewa ce, ka zama almubazzari Wanda baisan darajar kudi ba, in ba iskanci ba me suwaiba zatayi da dubu dari biyu harda d'oriya, wallhy tun muna mu biyu da kai gobe kafin goma na safe kaje ka amso min kudi na, kuma ka tabbatar ka kaima Hadiza kanwar Hajiya Nafeesa kana ji na ko, gyad'a kanshi yayi fuskarshi da bata cika nuna fushi ba ta canza launi saboda tsananin b'acin rai, Takalmin kafarshi ya cire ya kwanta yayi ruf da ciki yana tunanin yadda zaiyi ya samu dubu d'ari biyu gobe ba tare da yaje gidan mama suwaiba ba, Sai karfe daya ya yanke shawarar Kiran yayyenshi mata ya fad'a musu komai yasan a cikinsu bazai rasa Mai bashi ba..... Mrs Tijjani shattima.... [04/12 09:43] Meela Adeel: 4⃣ °ZUMUNCINMU A YAU ° By Aysha Ya'u Kurah Kamar a mafarki yaji ana bugun kofar dakinshi, mikewa yayi akan dardumar da bacci ya dauke shi bayan sallar asuba, mik'a ya fara yi hade da addu'ar tashi daga bacci, kara buga kofar da akayi ne ya sashi kallon agogo, goma saura kwata ya fadi da karfi yana mai karasawa kofar dakin, murda kofar yayi a hankali ya ja da baya hade da runtse idanuwanshi saboda tsoron irin kallon da zaiyi Karo dashi... *HAPPY 17TH BIRTHDAY BROO* Muryoyin su ya daki dodon kunnenshi, bude idonshi yayi da sauri ya bisu da kallo daya bayan daya, wani murmushi ya saki mai matukar kyau, take ya manta da damuwar da ta hanashi bacci ya fara rungumarsu yana fadin "thank u so much sweeries,, " Happy womb escape uncle" ya jiyo cikin siririyar murya, ''omg HINAD!! ya fadi da karfi, murmushi tayi mishi hade da yi mishi nuni da hanyar shigowa dakinshi da idanuwanta,, Ta madubin console din dake kallon dakinshi ya hangota tsaye cikin shigar jallabiya ta alfarma kanta yane da jan mayafi ta nade hannayenta a kirjinta tana murmushi, ihu ya saki hade da kwasawa a guje ya nufi gurinta, bude hannuwanta tayi ya fada kirjinta, "Best birthday gift eva luvly sis, I love u so much, dago fuskarshi tayi ta cire farin glass din Idonta tace ''Happy birthday little Diku nah, love you more,, karasowa suka yi cike da mamaki suka ce ''saukar yaushe ANTY REEMA, ''yanzun nan!, ko gida banje ba, ta fadi tana maida glass dinta, waigawa musaddiq yayi gurin Hinad ya lakace hancinta yace ''cutie pie ina handsome? yamutsa fuska tayi tace yana mota wai bazai shigo ba, dalili? Musaddiq ya tambaya yana kallon Anty Reema, ''don't ask me kasan halin d'an naka, kallon Sauran kannenta tayi tace mummy fa?, RADIYA ce ta fara magana, ''muma zuwan mu gidan kenan, ina ga bata tashi ba, hannun RAUDHA ta kama tace ''ina kika baro WALEED,? ''yana gidan Anty RALLY can yayi sallah, nasan suna hanya yanzu,, Raudha ta bata amsa cike da girmamawa, falo suka koma dukkansu banda musaddiq da tuni ya fita gurin HILAL.... Maganata ta karshe kenan babu wanda ya isa ya sake dawo da ita farko, bazan mishi party ba wannan shekarar FAKAT!!! mummy ta karashe fadi tana hararar musaddiq dake zaune kanshi a sunkuye, but mummy why,? RALIYA da shigowarta kenan ta tambaya tana karasowa parlon, tsaki mummy taja ta tashi ta wuce kitchen, Radiya da Raudha kuwa mamaki ne ya hanasu magana dan a iya rayuwarsu sunsan babu abin da mahaifiyarsu ke so sai bidi'a, haka nan ma kirkirar party takeyi in kudi yayi mata yawa, babu d'a, ko jikan da shekara ta taba wucewa ba ayi mishi kwarya kwarya ba, barin ma danta d'aya namiji tilo wanda partynshi ke banbanta da na kowa, shiyasa sukayi sammako dan ayi komai dasu, ''wow MIRACLE ya sakko kenan, yau mummy ce da kanta take cewa bazata yi ma little birthday ba, iko sai Allah Anty Reemah ta fadi tana mai mikewa, Raliya tace ''kedai bari anty na Kasa ajiye jaka saboda mamaki,, '''Ba abun mamaki bane laifi yayi ma mummy''' waigowa sukayi suna kallon ta inda maganar ta fito, karasowa tayi rike da cup a hannunta tace ''kwarai kuwa, almubazzaranci yayi da kudin mummy, ta aikeshi ya kaiwa Baffa shine ya kai gidansu Nadiya Roba Roba, kuma kudin da yawa har 200k, mikewa musaddiq yayi a fusace yayi kanta, rikeshi Anty Reemah tayi da sauri ta girgiza mishi kai alamar ya kyaleta, Badariyya ta rike kugu tace da kin kyaleshi anty, karya akayi maka, mtswww wanda bais----''shut up'' Anty Reemah ta katseta da karfi,, ''yaushe yarinyar nan ta fitsare haka, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, duka nawa kike Badar?, Musaddiq sa'an ki, ''Ba sa'a na bane amma abin da zaiyi ni bazanyi ba, dan Sam bashi da hanka----- wucewar walkiya da tsayuwar ji na wucin gadi ne ya hanata karasa maganar, rike kuncinta tayi ta Sanya kara mai firgitarwa, cike da firgici su Radiya suka karaso gurin, kallo anty Reemah ta bishi dashi yana huci hade da zazzaro ido, cikin zafi yace ''I usually give people more chances dan dey deserve, but once am done am done,! waye sa'an ki anan, tun dazu kina ta zuba rashin kunya an kyaleki shine kike kokarin wuce limit dinki, ya kalli musaddiq cikin kunan rai yace ''kanwar kanwarka ta tsaya tana fada maka magana kai kuma kana tsaye kamar gunki, u'r pathetic wallhi mtswwwwwwwww, yaja tsaki hade da daukar wayarshi yace ''wannan dalilin ya hanani shigowa gidan nan, kallon Anty Reemah yayi yace ''plss lets go Mum,, faduwa kasa Badariyya tayi tana ihu tana shureshure tana fadin ''Allah ya isa mugu azzalumi, wayyo Allah na mummy ya tsinka min kunne, da gudu mummy ta karaso ciki dan duk budurin da akeyi bata sani ba tana can bayan kitchen tana duba masu yi mata hidima..... Mrs Tijjani Shattima.... [04/12 09:43] Meela Adeel: 5⃣ °ZUMUNCINMU A YAU ° By Aysha Ya'u Kurah Ya ya, me yake faruwa? kukan wa nakeji kamar Badar, da gudu ta ruga jikin mummy, Hilal ya bita a guje ya daga hannu zai kai mata duka mummy ta daka mishi tsawa, ''kulll karka sake ka taba ta, rasa kunya berar danga, ko girgiza baiyi ba bare ya saurari abinda ta ce ya sauke hannunshi a bayanta, wani ihun Badar ta sake saki kamar wacce ake yankawa, kallon gurin da suke mummy tayi cikin bacin rai tace' ''Reemah dan iskanci kina tsaye danki zai raunata min 'ya, babu Wanda yayi yunkurin hanashi, kuma saboda rashin ta ido ya iya Zuwa har gabana ya narka mata gudumar hannunshi a baya, to wallhy bazan dauka ba, ko ki rama mata ko kuma ni in rama mata da kaina, Raliya tace ' ''haba mummy, ya za'ayi mu shiga fadan yara, Badar ce fa bata da gaskiya, rashin kunyarta kullum dad'a k'aburi yakeyi, babu Wanda ya isa ya fada mata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156