Chapter 53
Chapter 53
muyi, bata motsa daga inda take ba tana tsaye har seconds sittin, Murmushi yayi ya kara takowa yazo har inda take, kamar me rada yace "matsayinki ya kai in biyoki inda kike, kamar zatayi kuka ta juyo tace "um um dan Allah uncle kayi hakuri, zan dauko dankwali na ne, "Ya riga ya gama fahimtar yanayinta na tsoro yayi murmushi mai kashe zuciya yace "naki wayan, hular kanshi ya cire ya mika mata yace "ki rufe kanki dashi, saurin maida hannunta baya tayi tace "Dan All-- "karki hada ni da Allah, yayi saurin katse ta a kasalance, hannu yasa ya dago habarta ya sanya idanuwanshi cikin nata, kokarin sauke idonta tayi jiki na rawa, yayi girgiza mata kai alamar a'a, karkatar da kanshi gefe yayi, gaba daya soyayyarta tana neman maidashi zautacce, ya mance matsayin malami yake a gareta, suffofinshi na shagwababben Momma suka bayyana, a hankali yace "plssss!!! bata bari yayi magana ba tayi saurin runtse idonta hade girgiza kai, bata taba shiga yanayin da yake kokarin sanya ta a ciki ba, rufe idonshi yayi shima yace "karki hana ni plss, akwai abun da ya ke kokarin karya duk wani lago nawa, *Soyayya* ita gayyaceni zuwa gareki ba tare da shirya ma zuwanta ba, tell me,!! kina son in barta ta sanya ni na rankwafa, bani da wani sauran sukuni tun ranar da na fara ganinki, kiyi min agaji, ki tausaya min, ki tallafe ni, ki amince dani a cikin zuciyarki, sonki ya gama shiga cikin jinin jikina, Shuru ne ya dan ratsa gurin na minti daya, bugun zuciyoyinsu kadai suke jiyowa sai numfashinsu dake gauraya da juna, A hankali ta bude idonta wanda ya zamo kamar hadin baki shima ya bude nashi, da sauri ta dauke kanta hade da rugawa ciki da gudu, saida ta isa daki sannan ta fara maida numfashi.. jin karar ruwa a bayi ne ya bata tabbacin Husnah na ciki tana wanke jikin ta har lokacin, a gefen gado ta zauna ta runtse idonta, ta kasa fassara yanayin da take ciki, wani abu ne yake ta mata yawo a cikin kwanyarta.. karar wayar Husna ta ji tayi saurin mikewa ta dauko ta a gaban madubi, sunan da ta gani ne ya sanyata dauka, tun kafin tayi magana yace "kina lafiya, bata amsa ba tace "ina wuni Ya Hilal ba ita ce, "i knw ya fadi yana dada jinjinawa zuciyarshi da take saurin daukar haske akan kusancinta da Nadeeyah, tana dauka jikinshi ya bashi ita ce, "ya school, hope kina kokari ko,? cikin nutsuwa tace "umm ina yi, lumshe ido yayi ya bude yana kallon kasan office din da yakewa aikin zane yace "Good, babu ruwanki da kowa kamar yadda nake fada miki kullum, karatunki shine gatanki, bana san wani abu ya shiga rayuwarki yanzu, i want u to be successful kin gane ko, gyada kai tayi kamar tana gabanshi tace "in shaa Allah, in yana waya da ita ya kan manta duk wata zuciyarshi da bata san raini, yakan manta ko shi waye duk da har yanzu bai taba nuna mata alamar soyayya ba, so yakeyi ta zama macen da ko ina a duniya za'ayi alfahari da ita, "Zeemarh na gaishe ki, yau dakyar taje makarantar islamiyya wai ni zata bi, murmushi Nadeeyah tayi tace "Allah kuna lalata ta ne, anjima zan kira Anty ince ta dinga zane ta, "u are on ur own ya fadi hade da cewa kema musa a zaneki kuwa, sai ayi 50-50, dariya sosai tayi wacce ta sanya Hilal nishadi, zatayi magana kenan taji Anty Raly na kwala mata kira, sallama tayi mishi ta kashe wayar ta fita da sauri, kallo ta bita dashi fuskarta dauke da Murmushi, tace "Nadeeyah daga hannu sama mu godewa Allah, da sauri ta daga dan bata san me zasuyi ma adduar ba, bayan sun gama adduar tace "Allah ya kawo miki taimako, yanzu Taheer ya fita a gidannan, kaii yau saboda farin ciki bansan yadda zanyi ba, kin gama dacewa duniya, lahira kadai zaki nema, Nadeeyarmu ce zata zama matar Taheer surukar Anty Saude, wannan dadin ina zan kaishi yau, rufe fuska Nadeeyah tayi ta kasa gane ainihin yanayin da take ciki, na farin ciki ne ko akasinshi, kalaman Hilal ke mata yawo a zuciyarta, wanda sabonsu ke bata mamaki duk da har yanzu tana shayin shi, ga kuma zazzafar kaunar da ta gani a idon Taheer, rungumota Anty Raly tayi tace "saura 3 to months ki gama school, lokacin ne zamu fasa maganar nan, wallahi dadi yau kamar zai kasheni, daki Nadeeyah ta wuce da sauri tana nazarin abubuwan da suka gifta tsakaninta da Tahir...... ********___******* Turjiya takeyi a kasa tana ihu tana fadin "indai yaya Jamal zaije itama sai taje, dariya Hafeez yayi yace "Haba autar mami, yaya jamal fa ba bin mu zaiyi ba, ni da Papy kawai zamu tafi, kiyi hakuri kinji, fitowa yayi yana gyara button din rigarshi yace "fada mata gaskiya mister, dani za'a, dan Allah kafin mu dawo ki mutu tunda ni sa'anki ne, wani ihun ta saka wanda ya sanya Anni da sauki ya samuwa fitowa tana fadin Jamal zan ci maka mutunci akan yarinyar nan, turo baki yayi yace "haba Anni, kina ganin yarinya ta rainani, da nayi aure da wuri da na dire wacce ta fita ya karashe hade da rankwashinta, jikinshi ta shige tana ihu tana yakushinshi tana fadin "babu inda zakaje walhy, ni sai dai mu tafi tare, tureta yayi yana dariya yace "zan gani yau, ji min rigima fa, fitowar Papy ne ya sanyata zuwa gurinshi tana kuka, daukarta yayi yace "haba mamana, kaduna fa zani ba nan kusa ba, zo kiji a kunne, mika mishi kunnen tayi yayi mata rada, dariya tayi ta kalli Jamal tana mishi gwallo, har suka shiga motar tana tsalle tana ma Jamal gwalo tana cewa "an mishi wayau wooo, dariya sukayi dukkansu a motar, ta window ya leko yayi mata nashi gwalon shima kamar yaro karami, janta Mami tayi suka wuce daki dan kar Jamal ya sake ballo mata august... Karfe Hudu da minti ashirin suka shiga garin Kaduna, tunda suka shigo cikin garin Papy yaji jikinshi ya mutu, shidai yasan meeting yazo yi a Kaduna state university, amma yanzu ji yakeyi kamar wani abu mai muhimmaci akasin haka ne ya shigo dashi, Hotel din da aka kama musu Hafeez ya kaisu sannan ya yi musu sallama ya wuce da niyyar dawowa da safe... Washe gari bayan sun gama komai karfe biyu Hafeez yazo ya daukeshi, suna Hira Hafeez yace "mishi daga gidan kakanshi yake, baiji dadi ba jiya kwana yayi yana gudawa, da gangan ya fadi haka dan hakar shi ta cimma ruwa, in ma suna da dangantaka to suna ganin juna a yau zasu gane su kuma warware mishi komai, gidan Baffa ya wuce direct kamar yadda Papy ya bukaci zuwa gaisheshi,, A daidai kofar gidan yayi parking, cike da girmamawa ya bude mishi kofa yayi mishi iso har cikin gidan, fuskar Ma'u ke fuskantar hanyar shigowa, kamar an manne ganinta a fuskar papy, kallon Baffa tayi ta dago ta kara kallon Papy, Da sallama ya shigo ciki ya karaso ya tsuguna ya gaida Goggo, motsi kawai bakinta keyi amma ta gaza furta ko kalma daya, kamar ance Baffa ya dago nan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156