Chapter 91
Chapter 91
mutumin dake gabanta yana tambayarta ko tana san danshi, ta ina zata iya butulce mishi, a cikin jerin da ta lissafo babu wanda bai taka rawar gani cikin rayuwarta ba, kuma Daddy ne ya samar dasu, dago kai tayi suka hada ido da Mummy ta harareta hade girgiza mata kai, dauke kanta tayi da sauri ta kalli Daddy dake sake jefo mata tambayar, gyada kanta tayi a hankali alamar eh, wanene shi? Dan Musaddiq yazo min da zancenki, in wani kike so shikenan sai sawun giwa ya taka na rakumi, wani irin girma ya kara a idonta ta kasa bashi amsa, "Ko Musaddiq din kike so? Hannun Husnah ta rike sosai ta kasa dago ido ta kalleshi bare ta bashi amsa, sau uku yana tambayarta tana yin shuru, dariya yayi yace su tashi tafi, Nadeeyah har tana tuntube da kofa tayi saurin fita, Maida kallonshi gurin Musaddiq yayi yace "To Malam ka shirya ma aure? nawa ka tara daga albashinka, nidai kasan ba ruwana nima da kaina na auri matata ya karashe cikin zolayar dukkansu biyun, Ganin ya saki fuska yasa Mummy zama a kasan kafarshi, "Dan Allah Daddy ka rufa min asiri, bai kalleta ba yace "Allah ne mai rufawa Zainabu, me ya faru? Hawayen bakin ciki ta fara yi tace "Yanzu kai farin cikinka ne danka guda daya tiloo ya kare anan, tsakani da Allah duk yadda manyan abokanka ke miko ya'yansu mata gurinka domin shi, sai kuma suga ya kare a gurin yar Mai gadi, yadda ta fadi abun ya soki Daddy Matuka, nan da nan fuskarshi ta sauya yace "akan Nadeeyah zan iya bata miki rai wallahi, idan kika sake kiranta da yar mai gadi a matsayinta na jininki wallahi hukuncin da zan miki ba mai dadi bane, cikin bacin rai ta mike tace "ba jinina bace, uwarta ce kadai jinina, kai kasan asalinsu ne, wa yasani ma ko ubanta barawo ne ya shigo cikinmu aka bashi aure, wallahi bazan yarda in hada jini da marasa asali in samu bara gurbi cikin zuri'ata da zanyi tunkaho da ita ba, "wallahi bazata sabu ba, ai nima ina da hakki akan shi, saboda haka wallahi indai ni na haifeshi bai isa ya auri Nadeeyah ba, Sam Daddy bashi da saurin hannu amma tabbas a lokacin yayi niyyar dauke fuskar Mummy da mari, a hankali yace "ke kika haifeshi, ke kuma nike iko dake, wallahi tallahi in har kikayi abun da auren nan yaki yiwuwa sai kin bar min gidana, kinga sai kowa ya nuna ikonshi, Asali kuma Nadeeyah bata da wanda ya fini, a yanzu na zama asalin Nadeeyah, ni ne ubanta, ni ne danginta da komai nata, sai ki je maiduguri ki binciki Asalin Alh Garba kyari mai fata, kallon Musaddiq yayi yace ka tashi kaje ka fara shiri daga bangarenka, ni a bangarena bani da matsala... jiki a sanyaye Musaddiq ya mike ya fita daga dakin, bai taba tunanin zai samu wannan matsalar ba, gashi kuma har ga Allah yana son Nadeeyah bazai iya rabuwa da ita ba, ga kuma Mummy zata yi mishi karan tsaye cikin rayuwarshi, tunane tunane ya dinga yi ya rasa mafita ya dauki wayarshi dan kiran Hilal, a kashe wayar take dan haka ya kwanta yanata sakar da bata da karshe.... Mummy kuwa tana fita dakinta ta wuce cike da bakin ciki ta daga waya ta kira Radiya da Raudha da ta dawo gida weekend tace su kira Raliya suzo su sameta a gidan Goggo, jin yadda muryarta ke rawa suka san ba lafiya ba, ko wacce hankali tashe ta shirya tafiya gidan Goggo... "Radiya ina zaki da sassafe?, ko abun karyawa bakiyi ma su Umma ba kuma kinsan ba ita kadai bace, shekeke ta kalleshi tace "ni ma uwata ke nema na, ko bani da ikon amsa kiran, su tashi su daura da kansu tunda dai suna da hannu, shikenan ni bani da sukuni saboda umma tazo, a'a wallahi bazai yiwu ba, Raees babban danta ne ya shigo yace "Mama wai inji Umma tace ki kawo mata ruwan zafi zata sha magani, wani dogon tsaki taja tace "maza jeka gurin Gyatum kace ta kai mata, hijab ta dauko tasa tana kunkunin da tun zuwansu gidan takeyinshi, Mikewa mijinta yayi ya kira kanwarshi Haleesah yace "tazo tayi ma Su umma abinci, sam baya jin dadin abin da Radiya kema yan uwanshi dashi kanshi, hakuri kawai yakeyi saboda darajar mahaifinta, yana shiga kitchen ya tarar da wata yar budurwa wacce shekarunta bai wuce sha tara ba. tana tsaye tana taya gyatum aiki, Da sauri gyatum ta gaisheshi ya amsa yana kallon yarinyar, itama tsugunawa tayi har kasa ta gaisheshi, kamanninta da gyatum shi ya tabbatar mishi yarta ce, saidai wannan din bak'inta mai kyau ne, da dara daran ido farare tass ga kyawun diri, har zai fita yace "Gyatum wannan yarki ce? Murmushi tayi tace "eh Alhj, auta ta ce, a gurin kanwata take a jos, a can take karatu, yanzu ma tazo hutu ne tazo tayani aiki, gyada kanshi yayi yace "Dan Allah ku taimakeni ku hada ma su Umma abun karyawa, in san samu ne ma su samu tuwon laushi, da sauri gyatum ta mike tace "har sai ka roka, Bar wanke wanken nan Fatima ki fara hada kayan karyawa, Cike da jin dadi ya fita dan ko abincin baiyi dadi ba yasan zai fita kunyar mahaifiyarshi da kannenta... Cikin kwarewa Fatima tayi miyar kukar da taji daddawa da dagargajajjen naman kaza, sannan ta tafasa kifi kadan ta sa citta da karumfani da tafarnuwa ta dakesu tsaf ta juye a cikin miyar, nan gida ya kaure da kamshi, tana gamawa suka shirya komai cikin cooler gyatum ta dama musu kunun gyada ta fito da garin kosai ta kwaba tasa kwai da albasa ta soyashi gunin dadi, manyan Coolers gyatum ta zuba abincin aka kai musu sannan ta zuba a kananan coolers ta ajiye wa mai gidan a dining, saboda farin cikin ganin tuwon malmala biyu Umma ta cinye, cike da jin dadi Haleesa ta kalleta tace "yau Umma taci abinda take so, san samu kullum da safe da dare a dunga miki tuwo, to hakan bazai yiwu ba, hidimar Maman Raees tafi karfinta, harara Indo kanwar Umma ta jefawa Haleesa tace "yau da tayi kasheta aikin yayi, Dariya Haleesa tayi tace "waya fada miki ita tayi, ita bata gidan ma, mai aikin gidan ce tayi, a daidai lokacin fatima ta shigo kwashe kayan abincin, albarka suka shiga sa mata har ta gama ta fita, umma dai da ido ta bita, a kullum tana ma danta adduar samun mace ta gari ba mai kyale kyale irin Radiya ba, yanzu din ma bazata fasa ba, ganin da tayi wa Fatima na farko taji ta shiga ranta, saidai bazata tilasta shi ya nemeta ba, za dai ta cigaba da addua, dan tabbas danta bashi da mace a gidanshi...... *Wai ina Hajiya Goggo Ma'u ne* Bangaren Goggo kuwa tunda Anni ta tare kullum cikin kunan zuci take, tayi asirin, tayi tsafin duk a banza saboda yin auren Baffa ma kadai karyewar alkadari ne, ga yawan abinci sadaka da Anni keyi kusan kullum domin nema musu tsira ranar Gobe kiyama, Tunda Goggo taga asirin nata yaki aiki saidai suyi ta cin kudinta sai ta hakura
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156