Chapter 43
Chapter 43
tayi tace "maza matso ki tayata ku jera kayan, ke kuma Badar, bana son tashin hankali, Nadeeyah yar uwarki ce, kaddara ce ta sanya kukayi nesa da juna, yanzu kuma Allah ya hada ku, kuma kinsan baki da yadda zakiyi da hadin Allah... Ajiyar zuciya Hilal yayi a ranshi yace "Allah yasa Mummy ta daure a haka, yanzu ne zai tafi hankalinshi a kwance, yafi son yayi nesa da ita ta samu damar yin karatunta ta zama cikakkiyar mace, yasan in har yana ganinta kullum bazai iya controlling kanshi ba, dole yayi abin da zata gane halin da yake ciki, shi kuma ba yanzu yake son furta mata ba, yana matukar tattalin kalmar har sai ta cimma lokacin ta..... Karfe 5pm suka dawo gida hannunsu rike da ledoji, kalolin jallabiya guda shida Hilal ya siyo ma Nadeeyah, sai flat shoes guda biyu milk nd brown, dayar ledar kuma jallabiya ce guda biyu, kwala kiran Husna yayi, da sauri ta fito daga kitchen tana tsane hannunta tace "ya Hilal gani, "ledar ya mika mata yace "wannan naki ne, kinsan yanzu mun fara dasawa, tsalle tayi tana ihu tace "Thank u *bro Son* , bai damu da sunan da ta kirashi ba yace "wannan ki kaima Nadeeyah, kinga kayanta duk sun kode, zan ma Anty Rally magana sai kuje kasuwa a samo mata yan atamfofi, karbar ledar tayi tace "ummm ya Hilal ashe dai kana da kirki, gaskiya thank u, kamar kasan in tasa kaya abin na dan taba ni, wasu ma sun mata kadan, Murmushi jin dadi yayi yace "yauwa gaskiya i love u, u will be my personal person daga yanzu, dariya tayi tace "godiya nake, gashi gobe zaka tafi, gaskiya zanyi missing dinka, bari naje na kai mata, nasan zata ji dadi.... Bude kayan Husna tayi ta dinga yaba kyawunsu tana gwadawa a jikinta, tana cikin gwada wata ja a cikin na Nadeeyah Badar ta shigo dakin, zama tayi a gefen gado ta dauki daya a ciki tace "waye ya kawo mana jallabiya, shine har kika fara zaba baki jirani ba ko ta fadi a gadarance, kwacewa Husna tayi tace "to Mummy kiyi hakuri, ya Hilal ne siyan ma Nadeeyah, ta dauko nata tace 'kinga nawa nima, wayyo, ai kamar Husna ta watsa mata ruwan zafi haka taji, dama duk yau cikin kunci ta wuni saboda yadda Mummy tayi wata wuzu wuzu akan Nadeeyah, mikewa tayi idonta ya ciko da kwalla zata bar dakin, tausayi taba Husnah tace "sis zo wasa nake miki, guda biyu ya kawo mana ni da ke fa, sauran ne na Nadeeyah saboda bata a kaya, bata saurareta ba ta fita daga dakin dan tasan Hilal bazai taba yi mata kyauta ba, ninke kayan Husna tayi ta maidasu cikin ledar ta wuce kitchen ta kira Nadeeya, A tsorace Nadeeya ke daga kayan tace "duka nawa ne? gyada mata kai Husna tayi tace "u are very lucky, yaya Hilal bai taba kyautar ko da naira dari biyar ba, yaushe ma kaga fuska a gurinshi bare ya baka, sai gashi yau har ni ya hada, dark blue din ta dauko a ciki tace "gwada wannan nasan zata miki kyau, bayi taje ta sa a jikinta, fadin rigar yayi mata cibb saboda tana da dan jiki, sai dai tsawon ya so yayi mata yawa, madubin bayin ta kalla hade da gyara gashin da ya kwanto a goshinta, ita kanta ta yarda a zuciyarta rigar ta mata kyau, dakyar ta iya fitowa daga bayin saboda kunyar Husna, wooooww.. Husnah ta fadi a fili, a cikin ranta kuma tace "see beauty, oh Gosh, Allah baya bawa mai wuka nama, "kinga yadda yayi miki kyau kuwa, kunya ce ta ishi Nadeeyah tace " nagode, bari inje in cire, tareta Husna tayi tace "godiya dai zamu je kiyi ma "ya Hilal, daburcewa Nadeeyah tayi tace "a'a dan Allah bari in canza kaya sai muje, dagewa Husna tayi tace lallai sai dai suje a haka, dakyar ta yarda ta yafa gyalen a kanta, murda kofar dakin suka ji anyi, a tare suka waigo, daburcewa Nadeeyah tayi ganin Musaddiq da Hilal tsaye a bakin kofar, karasowa ciki Musaddiq yayi cikin zolaya yace "a'a iyye, kaga kanwata, ashe dai kina da kyau haka, to juyo ki nuna mana kwalliyar mana, janyo hijab tayi ta cukwikwiye kanta tace "ba kwalliya nayi ba, Husna ce tace in gwada ko zai min daidai, dariya yayi yace "kuma ya miki kyau, ashe dai mun iya zabe, to babu ko yar godiya, kara rufe fuskarta tayi tace "yanzu dama zamu je muyi, kuyi hakuri, Nagode Allah ya saka da mafificin alkhairi, Ameen Ameen, muma mun gode da addu'ar da muka roka, gurin Hilal Husna ta matsa tace "ya Hilal kaga yadda kayan suka karbemu, thank u once again, murmushi yayi yace "never mind, kinga mukullin motata cikin kayan nan, zazzage kayan ta koma tayi, babu komai a cikin su, dago kai tayi tace "baya ciki, ko ka barshi a jikin motar? Tunani ya fara yi yace "eh to bari inje in duba, ta gefen ido yake satar kallonta tun shigowarshi dakin, sai da zai fita ne ya kalli yadda ta matse kanta, murmushin shauki yayi ya fita zuciyarshi wasai saboda yadda yaga ta fara samun sakewa a gidan..... Jirgin karfe shida na yamma zasu bi, tun safe Hinad da Zainab suka tafi saloon suka wanke kansu akayi musu kitso, daga can gidan Mummy aka wuce dasu, nan suka yini har bayan la'asar sannan suka soma shirin tafiya, har bakin mota ta rakasu tana dada yi ma zainab nasiha, saida taga sun shiga motar sun zauna ta kalli Zainab da idonta ya ciko da kwalla tace "kuka kuma zakiyi, to bari in tafi in barki tunda kuka zakiyi, hannunta Zainab ta rike tace "Adda zan tafi in barki a gidan mummy su dinga saki kuka, meyasa bazaki zo mu tafi ba, share mata hawaye Nadeeyah tayi cikin dakiya tace "inji wa yace miki zasu sani kuka, bana nuna miki kayana da mummy ta kawo min ba, yau ma tace zata kuma kawo min wani, kar kiyi kuka kinji dukkan mu zamuji dadi, gyada kai Zainab tayi tace "Haka mumyn Hinad tace min, sake matse hannunta tayi tace "banda rashin ji kinji, in kikayi rashin ji zasu fada min, ni kuma sai inyi ta kuka anan, kinaso inyi kuka, girgiza kai tayi da sauri tace "a'a bana so, bazan kuma yi rashin ji ba, kumatunta Nadeeyah taja tace "good girl, hira suka cigaba dayi suna jiran drivern yazo suka hango motar Hafeez ta shigo gidan, da murna Nadeeyah taje gurin shi tana mishi barka da zuwa, rungumeta yayi suka wuce gurin su Zainab, ta window zainab ta fito ta dane wuyanshi tana murna, komawa mota yayi ya dauko katuwar leda yace "wannan sweets dinku ne ke da Hinad, kuma saura inji labarin kin mayar da shi abincinki, kara kankameshi tayi tace mun gode yaya, amma zaka dinga zuwa gurina ko? "Kullum zaki ganni, kedai kiyi karatu, banda rashin ji, banda takurawa mutane akan abin da babu kina ji na ko, gyada kai tayi tace "duk na sani Adda Nadeeya ta fada min, motar ya mayar da ita yace "to Allah ya kiyaye hanya, Hinad ki gaida Anty Reemah kinji, "in shaa Allah
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156