Chapter 79
Chapter 79
karka kashe ni, bari in kawo maka wani abinci me nauyi, kallon Husnah yayi dake kara jaddaddawa Hafeez suje ta bashi kayan shi ya saka, "in kinje ki bashi riga kadai ta isheshi, kinga sai kuji dadin zagin halitta ta, ya karashe yana kai kofin bakinshi, dariyar ma kin fitowa Husnah tayi suka fita tare da Nadeeyah, Dariya Hafeez yayi yace "manta da ita kaji, gida zan koma in canza kaya, bari in kira Jamal ya kawo min mota, ciro key Musaddiq yayi yace "ga tawa kaje ka dawo kafin a fara walimar, karbar keyn yayi yace "ka dai ajiye min nawa abincin kar ka cinye kai kadai, "Haaahaha... zan daina cin abinci kwata kwata a idon mutane, gara in rage wannan kibar, da zan iya ma harda tsawo zan rage, "dariyar Shirmen Musaddiq Hafeez yayi ya fita yana jin dadin yadda al'amura suke kasancewa kamar yadda Mamma take so, Allah sarki Mamma, ina ma ana mutuwa a dawo kiga yadda wuya take neman rikide mana ta zamto dadi, kiga yadda dan uwan da baki sani ba yake gatata mu kamar shi ya tsuguna ya haifemu, Allah yayi miki Rahama ya fadi ya shiga motar zuciyarshi a dagule saboda tuno iyayenshi da yayi....... Ana idar da sallar isha'i su Nadeeyah suka fara shirin barin gurin su Anni, hankalin Nadeeyah a kwance ta gama shiri dan tasan yanzu su Anty Radiya sun bar gidan, "kallon banza da habaicin talauci hade da rashin asali da suke mata yana sosa ranta matuka, kalmar da Anty Raudah ta fadi na "anyi clean fata ta murje da abinci akan kari sai kace wata yar shugaban kasa, a dai dinga tuno asali dan kar garin iyawa a wuce gona da iri!! Wadannan kalamai sun matukar tsaya mata, dan ma Musaddiq dake bayanta wanda dan shi Anty Raudah tayi mata habaicin yace "Haba Anty, sai kace sa'arki, dani take magana bada ke ba, ku ke jawa kanku raini wallahi, yayi tsaki a hankali hade da cewa Nadeeyah ta kira Husnah su tafi... Hannu ya kyasta mata a kusa da idonta, a firgice ta dawo daga tunanin abubuwan da suka gifta dazu a gidan, rage Murya yayi yace "Tunanin su Anty ko? Abin da ya kamata ki saba dashi ne tunda saidai in basu zo gidan ba, in kika kula mutum a kullum burin shi ya bata miki rai to sai kiyi fatali da duk abin da yace, domin shi kadai zaiyi dakon bacin ransa, "Zuciya is very special my sister, fill it with love, karki bari bacin rai ya samu kofar shiga cikinta, dan bacin rai na destroying duk abin da aka tanadarwa zuciya, dan haka bana san ganin tunani ko bacin rai nan a tare dake, kinji ko? gyada kai tayi hade da murmushinta mai kyau, "Thats my lovely sis, oya kira mana Husnah mu tafi, kafin ta kai ga amsawa suka hango Husnah sun fito tare da Hafeez da Ruwaidah a tsakiya, gefe kuma Jamal ne sanye da kayan bacci shima yana dosar inda suke, "Badai bacci zakayi ba, Musaddiq ya tambayeshi yana mishi kallon mamaki, jingina jikin motar yayi yace "in banyi bacci ba ai sai in kasa moruwa, yau ko tamola bata kaini garuwa ba, wahalar da Baffa ya bani yau ba kadan bace, "duk wani abokinshi da yazo gurin daurin aure wanda baida mota saida na maidashi gida, just imagine kaine, hmmm thank Goodness akwai ruwan zafi, da yau sai na tashi aiki, ya karashe yana danna bayanshi, "Lazy youth!! Ruwaidah ta fadi tana boyewa a bayan Hafeez, dariya ta basu dukkansu Nadeeyah tace "duk kokarin nan da yayi ki kirashi lazy, murya cakwai tace "Allah Adda he is very lazy and he can exaggerate, yanzu haka gida uku yaje, haka Mami ke fama dashi baya san a moreshi, Rai a bace Jamal yayi inda take yana fadin "ni sa'anki, wani irin ihu ta saki hade da rugawa ciki, bayanta yabi da gudu dan yaci alwashin ko a gaban Papy ne sai ya gurji bakinta, Dariya Hafeez yayi yace ku shiga mota ku tafi dare nayi, indai su Jamal ne kullum sai sunyi sau ba adadi, ya kasa gane dadin tsokanarshi takeyi, saboda bata da abokin wasa shiyasa ta maidashi abokin wasanta, shi kuma san girma yasa baya wasa da ita, " haushin hakan yasa ta rainashi sosai, motar suka bude suka shiga suna dariyar Ruwaidah da Jamal, Sallama sukayi ma Hafeez da kunya ta hanashi katabus saboda irin kallon da Husnah take mishi, dalilin da yasa ya sanya Ruwaida a tsakaninsu kenan da ya fito yi musu rakiya, ko a da lokacin da yayi wauta da rudin kudi mata ke kawo kansu, ita kuwa Husnah ganin irin gidan da ta fito ya sanyashi jin kunyarta da taka tsantsan, dan yasan tafi karfinshi, shi da bashi da cikakken asali kamar yadda Goggo ke yawan fada, wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, gara ya nemi saffa saffa dai dai shi.... Mrs Tijjani Shattimah...... [01/04 3:08 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣0⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Kasa tabuka komai Nadeeyah tayi ta dauki wayarta ta latsa number Hilal, sai tayi kamar zata shiga sai tayi saurin kashewà, tun daren jiya take abu daya, tasan yadda ya saba da yi mata text haka nan bazai ki turowa ba sai da dalili, Abin da bata sani ba shine, duk latsin da zatayi ma numbershi tana shiga kadan sai ta katse, da haka ya fahimci ta damu da rashin tura mata sakon wanda yayi shi domin fahimtar wani abu daga gareta, Yana gama shiryawa ya dauki wayar ya latso ta, ajiye kwan da take kadawa tayi da sauri ta dauka ringing na farko, "ajiyar Zuciya yayi a hankali, ita din ma hakan tayi amma nata ya dan fito kadan, shuru ne ya ratsa wayar na yan sakwanni, shi ya fara katse shurun ta hanyar cewa "ina kwana Anty, saura kiris wayar ta fado a hannunta tayi saurin riketa tace "kayi Hakuri, ina kwana, "a'a ai ni ya kamata in fara gaisuwar, kina nan lafiya? bata amsa ba ta sake cewa "ina kwana, yasu Anty? dariya yayi mara sauti yace "kowa lafiya, "harda k--- shuru tayi ta kasa karasawa, "Harda ni Nadeeyah, lafiyata kalau, alhamdulillah ta fadi a zuciyarta, a fili kuma tace "to Masha Allah, gyara tsayuwarshi yayi yace "jiya kuma bakiga sakona ba, ke kuma baki damu ki turo ba, shikenan da mutuwa nayi haka zaki manta dani bare har in sa ran addu'a, cikin rawar Muryar da take nuni da alamun tayi matukar missing sakonnin shi tace "Dan Allah kayi hakuri, na rubuta sai na kasa turowa, "ehen me kika rubuta? fada min da baki, toshe bakin tayi da hannu taki sakinshi dan bata san abun da zata ce mishi ba, tana jiyo Muryar Hinad na cewa "Papa na kiranka, muryarshi taji bayan fitar Hinad yace "ina jiran ganin sakon irin na jiya sakk, zan gane rubutun na jiya da na yau, sai na jiki ya karashe hade da kashe wayar ya sauka kasa gurin Papa.... ******* Karfe goma na dare Mummy ta shigo dakin su Nadeeyah bayan ta gama kashe kayan kallon parlon, kallon Nadeeyah tayi wacce ke zaune da blue riga da wando na bacci, tasan Nadeeyah ce kadai a gidan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156