Skip to content

Chapter 61

Chapter 61

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

yayi rai a bace yace "hey bata bukatar garkuwarka, live ur life nd let her live hers, Hannunta ya kama ya cigaba da cewa "ba sa'arka bace, kamar yadda kace, so ka barta tayi abun da takeso, ka nemi sa'oinka ka zame musu garkuwa, yana kaiwa nan yaja ta zuwa dakinsu, Hilal kamar zai mutu saboda takaicin zuciyarshi da furucinshi, To ya zaiyi, shi kanshi baisan ya fadi wasu abubuwan ba saboda tsananin kishin da ya nemi zautashi, Kalaman Taheer sun matukar hassala shi, ledar da yayi wurgi da ita ya dauka ya mikawa Anty Raly yace "ki mayar mishi da abunshi, babu wanda a gidannan waya ta gagareshi, wallahi in kika ce baza ki mayar ba yanzu zan kira Daddy in fada mishi yadda kike son lalata rayuwar marainyar Allah, Yana kaiwa nan ya fara tafiya zuwa dakin Musaddiq, "In ka fasa Hilal, in ka fasa ka fada ka raina kanka, bazan mayar da wayar ba dan Allah in kana iyawa kazo ka zaneni, mara kunyan banza da wofi, Bayan Hilal Husna tabi tana fadin "sorry my PP, rabu da Anty gobe zan mayar mishi da wayar school, wani irin miyau ya hadiye mai daci a hankali yace " laifi ne dan inason gyara rayuwarta, girgiza kai tayi tace "a'a ya Hilal, in akwai irinka cikin rayuwarmu bazamu taba tagayyara ba, amma pls ka dinga danne zuciyarka, in kayi fushi kai kanka tsoron kanka kakeji, bana son ganin fushin.. gyada mata kai yayi ya murda dakin ya shiga hade cewa ta tafi ta barshi shi kadai.... A can daki kuwa Musaddiq keta rarrashin Nadeeyah wacce keta kuka sosai harda shashsheka tana fadin "walhi ban taba mishi magana ba, kuma ni bance ina sonshi ba, nima buri na inyi karatu mai zurfi, dan Allah Ya Musaddiq ka bashi hakuri, wallahi bazan kara ba.. Zaunar da ita yayi a gefen gadonsu, ya tsuguna a gabanta ya sa hannu yana share mata hawaye yace "karki damu, ranshi ne ya baci, duk tausayinki ne yaja hakan, Yasha fada min in dinga sa ido a kanki saboda maraicinki, Hilal na matukar son kiyi karatun da zai sa ki dogara da kanki, A iya sanina ban taba ganin abun da Hilal ya damu dashi ba bayan iyayenshi, sai ni, sai ke yanzu da kike son kwace min mishi, nidai bazan yarda ba, kawai kinsa ya daina damuwa dani, ko waya mukeyi ya dinga tambayata ke kenan, Dariya tayi sosai, yadda yayi maganar a shagwabe ya sanya ta manta duk wani kuncin da ya tokare zuciyarta, Murmushi yayi shima ya mike yaja kumatunta yace "haka nake so kanwata, karki kara zubda hawaye kinji? kai ta gyada mishi ya kashe mata ido daya ya juya zai fita a dakin, Ganin Badariyya yayi tsaye a bayanshi tana huci, wani irin kallo yayi mata hade da cewa "lafiya? Bata iya bashi amsa ba sai hawaye ya ga suna sauka a idanuwanta, mtswwwww.... dogon tsaki yaja ya bi ta gefenta ya bude kofar dakin ya fita, wani kololon bakin ciki ne ya turnuke Badariyya tayi ma Nadeeyah wani irin kallo hawaye na cigaba da ambaliya a idonta, Mikewa Nadeeyah zata wuce Badar ta janyo ta ta hankada ta baya, "uban me kukeyi a dakin nan ta fadi murya kausashe, Husnah da shigowarta dakin kenan tace "me ko sukeyi, *Soyayya* mana, baki san suna soyayya ba dama? ta fadi hakan ne dan ta tunzura ta, dan ta gane take takenta da dadewa.... aiko ta tunzuru, dan hauka ta fara yi, ta cakumi wuyan Nadeeyah iya karfinta tana fadin "wallahi saina kasheki, shakar da tayi mata ita ta hana ta ihu mai karfi, sai hawayen azaba da take fitarwa, Da Husnah taga ta kasa kwace Nadeeyah a hannunta kuma tana ganin take taken zata iya kashetan da gaske tace "na shiga uku, wallahi karya nakeyi, ki saketa Badar, inaa kesashshiyar zuciyar Badariyya bata ji bata gani wen it comes to Musaddiq, Da sauri Husnah ta fita tana ihu tana fadin "Zata kasheta, wayyo Allah Anty Raly kizo zata kashe ta, Wa za'a kashe? Daddy da ya shigo a lokacin ya tambaya a gigice, Husnah da kuka ya kufce mata ta nuna dakinsu tace Badariyya zata kashe Nadee---- kafin ta karasa fadi Hilal ya murda kofar da karfi har yana cire handle din kofar, lokacin da ya shiga kiriss ya rage Nadeeyah ta suma, dan idonta da ya jike da hawaye ya fara lumshewa, ita kanta Badar din kukan takeyi, amma zuciyarta ta ki bari ta saketa, dama wannan damar take jira, tsanar da tayi ma Nadeeyah mara misaltuwa ce, gara ta kasheta kowa ya huta, tasan hukuncinta kadan ne tunda bata kai 18yrs ba "a karancin iliminta na addini", Iya karfinshi ya sa ya janye Badar, yayi wurgi da ita jikin drawer dakin har saida mudubin drawer ya fashe, da gudu Musaddiq yayi kan Nadeeyah da ta durkushe tana tari dakyar, rungumota yayi jikinshi yana jijjigata, yana kiran sunanta da karfi saboda firgici...... Mrs Tijjani Shattimah...... [24/03 9:36 PM] Ummu Abdul 2: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣2⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Ganin yadda take lumshe ido ya sa Daddy cewa "kawo ruwa da sauri Husnah, rige rigen dauko ruwa sukayi ita da Anty Raly, A kidime Musaddiq ya bude bakinta yana hura mata iskar bakinshi saboda yadda jikinta ya fara saki, babu wanda a cikinsu ya ji, ko ya saurari irin dukan da Hilal yakewa Badariyya kamar Allah ya aikoshi, Tun tana ihu anaji har muryarta ta dashe, da gudu ta rarrafa ta rike kafar Daddy tace "dan Allah Daddy kace yayi hakuri bazan kara ba wallahi, finciko Hilal yayi yace "kin san Allah dama, belt din hannunshi har ya tattare saboda azabar duka, Badan tausayi ba, sai dan saboda muryarta ta ishi Daddy yasashi cewa "kyaleta Muktar! Badan yaso ba ya kyaleta yana yi mata kallon ban gama dake ba, a guje ta bar dakin tana ihun azabar haurin da yayi mata a baya, a kofar shigowa palon taci karo da Su Mummy, rungumarta tayi a tsorace tace "ke lafiya, meya faru? Kankameta Badar tayi tace "zasu kasheni Mummy, wayyo Allah bayana, kallon su Mami da Anni tayi tace "ku shigo ciki ku zauna, shigowa sukayi suka zauna, Mummy taja hannun Badar suka shiga dakin, Tsaye ta samesu dukkansu akan Nadeeyah da ta bude idonta tana maida numfashi, Belt din hannun Hilal ta kalla rai a bace tace "uban me tayi maka kayi mata dukan ficewar hayyaci, abin da ya kawoka gidan nan kenan, ya ilahi kayi min maganin yaron nan da duk in yazo gidana sai ya tayar min da husuma, wannan wace irin mas---- dakata min!! Daddy ya katseta fuskarshi a murtuke babu alamun wasa, Naji alamar zuwan baki, muje in samesu, da kaina zanyi maganin matsalar gidana, naji duk abin da ke faruwa tun zuwan Nadeeyah gidannan har kawo yau da idona ya gane min, "Nadeeyah, Mummy ta fadi a hankali, ta kalli Nadeeyar dake kwance har lokacin a jikin Musaddiq, Saida Daddy ya bar dakin ta tambayi Husnah abun da ya faru, yadda abin ya faru ta fada mata, ta sakaya mata ainihin abun da ya tunzura Badar, jiki a sanyaye ta fita a daki dan bata da mafita sai jiran hukuncin da Daddy zai yanke....

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156