Chapter 114
Chapter 114
ya nufi gida zuciyarshi kamar ana soyata saboda gashin kumar da yakeji a cikinta...... Kashe motar Zubair yayi yace "Muje dai tunda ka matsa, dama amarya tamin gorin ban taba cin abincinta ba.. Dariya Hilal yayi ya saba jakarshi a baya suka wuce cikin gidan, Tun kafin su karasa suke jiyo muryoyi ana maida magana kamar karnuka, kalmar da ta da ta doki kunnen Hilal ita ta sashi yar da jakar hannunshi haďe da murďa kofar parlon... *Da ya saketa ai ku kuka koreta, ku kuka ce zaku koreta kuma kuka ce mata kar ta sake shigowa cikin rayuwarku, saboda haka ku zaku nemota ko in tona muku asiri wallahi...* Cikin rashin sani yake kallon wacce tayi maganar dan bai santa ba, shakar da Raudha ta kai mata ita tasata sakin ihu sosai tana neman ceto, dukkansu basu san Hilal da Zubair sun shigo parlon ba.. "Dan ubanki saboda wa mukayi? Saboda ki aureshi muka sanyashi ya saketa kuma muka koreta a gidan, Fisgewa Faida tayi tace "Saboda kwaďayi dai, kwadayin abin duniya da kuma kuna ganin Nadeeyah babu wani nata zai zame muku gata, ni kuma kunsan waye mahaifina, in banda son abun duniya waye zai ki Nadeeyah ya daukeni, ta fini komai na dan adam, ciki harda halin kwarai, ranar da muka kwashe naman miya muka boye batayi yunkurin kare kanta ba saboda girmamawa kuma tasan ku kuka dauke dan ta ganshi daga baya, hakan baisa tayi yunkurin tonaku ba, ku kukayi ma kanku dan ni ko Musaddiq kadai ya rage namiji a duniya bazan aureshi ba, banason zama da mijin da baya sona, gara in nemi wanda zai soni in soshi... "Dan bakya son Musaddiq yanzu shine zaki faďa mishi duk abun da mukayi dan ki haďa ni da ďana? Mummy ce tayi maganar cikin kunan rai da nadama, "Gara in faďa mishi yasan lallai fa uwar da ta haifeshi bata kaunar farin cikinsa, domin da kina kaunarsa bazaki rabashi da matar da ko sati biyu batayi a gidanshi ba, kuma kinsan irin son da yake mata, uhmm ni am out of this trash ku karata can, gida zan wuce, tana kaiwa nan tayi gaba abinta, Bin bayanta Radiya tayi ta janyota haďe da ďaga hannu zata kwaďa mata mari, kammm... taji hannunta alamun an rikeshi, waigawa tayi dan ganin wanda ya rike hannun tayi tozali da Hilal wanda idanuwanshi suka zama kamar jini saboda tsabar jaa da sukayi, wurgi yayi da hannunta wanda ya sanyata yin baya tagaga zata faďi, Buďe fuska Faida tayi saboda rashin jin saukar marin a fuskarta, ganin Hilal ya nufota yasata yin baya da sauri, kamo hannunta yayi da karfi har ta kusa missing step zata faďi, parlon ya dawo da ita ya zaunar da ita dabass kamar wanda yayi wurgi da kaya, nan idanuwanta suka firfito waje tayi saurin cewa "Waye kai? In kaji min ciwo fa? Akan me zak---- Shut up.... ya faďi da karfi har saida kirjin Mummy ya buga, Zama yayi yana facing dinta haďe da daukar waya dan kiran Musaddiq yaji inda yake, karar wayar yaji a parlor haďe da sakkowarshi daga sama a hankali kamar wanda aka zarewa laka... Maida kallonshi gurin Faida yayi yace "Bance ki rage min ko kalma daya ba, bance ki mance komai ba dan in kin mance u will be in for it, komai da ya faru nakeson ji nd lastly... ina Nadeeyah? Kamar jira takeyi ya rufe baki tace "cikin sauki ya kamata ka tambayeni ba sai ka kusa yi min lahani ba, in dai wannan ne zan baka labarinshi, harda shirin gaba da mukayi.... "Ba kai ba, uwarka ma bata isa ta shigo gidannan a yanzu tasan abun da ke faruwa ba, Musaddiq ďana ne, ni ke da ikon zaba mishi abin da nasan zai fi dacewa da rayuwarshi, kai waye da kake tunanin zaka iya interfering cikin rayuwarshi a koda yaushe... Runste ido Hilal yayi dan bashi da wani kuzarin da zai iya amsata, sake duban Faida yayi zaiyi magana yaji sautin Muryar Musaddiq "Ni ba danki bane, karki sake taba ni, babu uwar da zatayi ma ďanta haka, a da ina ganin babu wata mace da ta kaiki son 'ya'yanta, ashe ke din mace ce mai son zuciya, i hate you, i hate u.. hakan yayi ta maimaitawa haďe da durkushe a gurin.... Share hawayen da ya ďigo mata tayi tace "Taimakonka nayi, bazaka gane hakan ba sai nan gaba, yanzu nasan fushi ne da kuma shaukin dafin son da ta ďiga maka, da sannu zata fita a ranka ka gane gatan da nayi maka, kai kanka ka faďi "bata da asali, kasan kenan bata dace da mai cikakken asali irinka ba... Hannayenshi duk biyun ya daura akanshi yana girgiza kanshi hawaye na bin idonshi, kalmar *bata da asali* ita ta dinga yawo akanshi, rarrafawa yayi ya isa kusa da Musaddiq, "Nadeeyah bata da asali Musaddiq? Kai da bakinka ka fadi cewa bata da asali? To ina take? Ina Nadeeyah take.... ya faďi da karfi haďe da shake wuyan Musaddiq.. Da sauri Zubair da tunda ya shigo yake tsaye cike da mamaki ya fara kokarin banbare Musaddiq daga hannun Hilal, dukkansu hawaye ne ke zuba a idonsu, ture zubair yayi da karfi yace "He promised to take care of her, ina ya korata? Ina ya tura marainiyar Allah, just 9days of their marriage, Meyasa bai kyaleta ba tunda yasan bazai iya ba? meyasa ya zabi ruguza rayuwarta at this early age? he shud have lv her for me in yasan shi bazai iya ba, shi kaďai ne wanda zan iya sadaukarwa da abinda na dade ina dakon so, why did u do dis to her, Why Musaddiq? Ya karashe cikin ficewar hankali haďe da kwantar da kanshi a gurin.... Nan kallo ya koma gurin Hilal wanda ke kuka mai ban tausayi, Share hawaye Musaddiq yayi jikinshi na rawa ya durkusa gaban Hilal yace "Hilal---- Don't ask me anything Musaddiq, u are very useless, baka da amfani a rayuwarka bare ka amfani wani, you are a Coward... Irresponsible human bei--- Toshe mishi baki Zubair yayi da sauri yace "wannan abun da kukeyi bazai taimaka ba, gara mu fita mu nemo ta kafin ta shiga wani hali... Babu inda ďana zashi Mummy ta faďi tana rike hannun Musaddiq, A hankali ya zame hannunshi yace "Sau biyu kenan zan maimaita, ni ba danki bane, kin daina amsa sunan Mahaifiyata, yana kaiwa nan yabi bayan su Zubair zuciyarshi cike da tunanin maganganun Hilal, A kofar da zasu fita sukaci karo da Abbati, da sauri ya nufesu yace "yauwa Musaddiq tun dazu nake kiranka, fito da wayar Raudha yayi ya nuna mishi text din da sukayi tayi da Radiya a daren jiya, sannan ya kare da cewa kar kayi gangancin yarda da duk da zasu ce maka... Is too late Musaddiq ya faďi yana mai share hawayen da yaki tsayawa a idonshi, yana hango Hilal na matsama Zubair ya tada motar yayi saurin cewa "Kayi hakuri zamuyi waya, yanzu zamu je nemo Nadeeyah ne.. bayanshi Abbati yabi da kallo cike da tausayawa yace "Allah sarki, Allah ya haďaka da matarka, Cikin parlon ya karasa kanshi tsaye haďe da sallama dan ba mutunci bane ya kawo shi....... Kamar yadda su Musaddiq sukayi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156