Chapter 15
Chapter 15
matukar tausaya musu, duk da irin wadatar abincin da suke samu baisa su walwala ba bare har su kai ga cinshi cikin jin dadi, A cikin kwanakin Mummy tayi bajinta matuka, ta manta duk wani girman kai nata, sai ma tsananin tausayin yar uwarta, A wannan lokacin ne Daddy da Musaddiq da duk wasu makusantansu suka san lallai jini daya ya wuce wasa, yaran mummy ma sunyi bajinta matuka daga su har mazajensu, sam mummy bata ba kowa kofar da zaiyi complain ba.. A cikin kwanakin kullum ta koma gida a tsorace take, Jikinta na bata kamar zata iya rasa wani makusancinta lokaci daya, ( Nidai nace Allah yasa wannan canjin ya daure).. Bayan an watse adduar bakwai kowa na shirin tafiya gida, mummy ce ta shigo daki ta zauna gefen gadon da mama suwaiba take, cikin Nasiha tace "suwaiba ki kwantar da Hankalinki, kiyi tawakkali, Allah ya fiki san Adamu, kuma ya karbi abinshi, dan Allah kar kiyi abin da zai sa ya'yanki su cutu, domin yanzu ke kadai kika rage musu, dan Allah suwaiba ki rage tunani, ga kayan abinci nan na hadesu guri daya, na bawa Nadeeyah mukullin, gyada kai mamma tayi idon nan yayi ciki ciki, tace "Mun gode mummy Allah ya bada lada, Allah ya biyaku da gidan aljann----- bata karashe ba kuka mai karfi ya kwace mata, Hakuri su mummy da sauran matan dakin suka shiga bata suna tayata sharar kwalla, nan fa kuka ya rikide ya zama tari mai karfi, tun tana tarin da sauran karfinta har takai ga ta fara tarin jini, a gigice mummy ta fito tana kiran sunan Hafeez.. Hafeez na kofar gida yana sallamar baki shi da musaddiq suka jiyo ihun mummy, suka ruga cikin gidan a guje, a rude mummy tace "maza ka fito da mota Hafeezu mu tafi asibiti Suwaiba Aman jini takeyi, fito da ido waje Hafeez yayi cikin firgici yace "aman jini? eh mummy ta fadi tana turashi cikin dakin, Daukota yayi cakk ya fito da ita waje yana fadin dan Allah mamma kiyi hakuri, karki tafi ki barmu, gurin motarshi ya nufa da ita musaddiq ya bude baya aka shimfideta, gefe Nadeeyah ta shiga idon nan a kafe babu ko digon hawaye, zafin da kirjinta yakeyi ba mai kwatantuwa bane a wannan lokacin, motar Hafeez yaja da karfi suka nufi Asibiti mafi kusa. Da isarsu Hafeez ya sauka ko key bai cire ba ya fara kiran nurses, gadon emergency aka gunguro aka shimfideta a kai, gungurashi ciki suka fara yi da sauri sauri, da kyar kalmar salati ke fita a bakin mamma, babu wani sauran karfi a tattare da ita, komai nata ya riga ya gama sakewa, da karfi ta cakumo hannun Nadeeyah wacce take tayata salati ta hada da na Hafeez, idanuwan nan nata dakyar take iya budesu, "Ka rike min su Amana Hafeez, dan Allah ka rikesu, nasani kai me rauni ne Hafizu, abu kadan ke juya kwakwalwarka, na rokeka kar ka barsu suyi kukan rashin mu, na yafe maka, kuma mahaifinka ma ya yafe maka, ta juyo da kallanta gurin Nadeeyah da idonta ya kada sosai tace "Nasani Zainab nada nagartacciyar uwa, basai nace komai ba! Allah ya albarkaci rayuwarki, kiyi Hakuri da rayuwa Nadeeyah, ina matukar alfahari dake tun daga haihuwarki har kawo yau, Allah ya cigaba da taimakonki a duk halin da kika tsinci kanki, hannu Nadeeya tasa ta rufe mata baki tace "mamma babu abin da zai sameki in shaa Allah.. Dakin emergency aka shiga da ita aka ce su jira a nan likita zai shiga ya duba ta, kuka sosai Hafeez da Musaddiq keyi, Nadeeyah ce kadai tayi karfin halin yin addu'a, minti talatin da shigar doctor su mummy suka shigo, kafin su karaso doctor ya fito fuskar nan cike da damuwa, Kallon Hafeez yayi nan take zuciyarshi ta karye yace "am sorry, she is no more!! zuciyarta ta kai awa daya da yin collapse, yanzu ta daina aiki kwata kwata.. wani irin ihu Mummy ta saka wanda ya razanar da daukacin mutanen asibitin... Juyayi kwakwalwar Nadeeya ta shiga yi, a can cikin kanta take jin kalmar "she is no more, baya ta fara ja tana ganin mutane biyu biyu, kukansu sai juya kwakwalwarta yakeyi, batayi aune ba sai jinta tayi jikinta ya saki bata da wani sauran karfin da jikinta zai dauketa, sulalewa tayi saura kadan ta kai kasa, Cikin zafin nama ya karaso gurin ya riketa, babu wanda hankalinshi yake kanta, kowa kuka yakeyi babu kakkautawa, suma shigowarsu gurin kenan don daga airport asibitin suka wuto saboda Raliya ta fada musu halin da ake ciki.. Sunan Doctor HILAL ya fara kira da karfi hade da dagata ya rike a jikinshi, nan take hankalin masu kukan ya dawo kansu, wani daki aka shigar da Nadeeyah aka kwantar da ita a kan gado, hannunta Hilal ya rike yana murzashi da karfi yana kiran sunanta, koda doctor ya shigo Hilal na zaune a gefen gadon yanata bubbuga hannun, magana doctor yayi mishi yace ya tashi ya dubata, mikewa Hilal yayi ya koma kusa da su Papa ya harde hannunshi hade da jingine kanshi a bango, zuciyarshi ta karye matuka, da ya iya yi ma damuwa kuka da irin kukan da zaiyi ba mai misaltuwa bane, sai dai shi sam kuka baya daga cikin jerin abinda ya dauka me yaye damuwa, dan in yaga mutum na kuka har mamaki abun yake bashi. Minti kalilan doctor yayi a kan Nadeeyah ya fita bayan ya sanar musu shock ne yasa ta faduwa, amma in shaa Allah nan da awa daya zuwa biyu zata farka... Dakin gawar suka koma, kuka ya dawo musu sabo, Zuwan Daddy ne ya sanyasu cikin hankalinsu da nasihar da yayi musu, sannan yasa aka dauki gawar a ambulance suka wuce dan yi mata sutura.... ( *ALLAHU AKBAAR* Haka rayuwar ta gada, mutuwa na daya daga cikin abubuwan da muka debo na daga rayuwarmu, akwai masu rasa biyar lokaci daya, kuma badan Allah baya sansu bane, sai dai dan musan mutuwa ta zama dole, dukkanmu zamu dandanata komin daren dadewa, Allah ya kara mana hakurin rashin da mukayi dukkaninmu, kuma yasa mu cika da kyau da imani) Ameen ya Allah Mrs Tijjani shattima... [04/12 09:50] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU By Aysha Ya'u Kurah 1⃣7⃣ Ba gidan mutuwar ba, har unguwar su Nadeeyah sai da ta sake hargitsewa da koke koke, duk rashin imanin mutum sai ya zubar da hawaye saboda tausayin rai... ana sauke gawar, kofar gidan ya sake dinkewa da mutane.. A sanyaye Zainab ta shigo gidan, dama dakyar taje islamiyya a ranar, Hafeezu da kanshi ya kaita saboda tirjiyar da tayi, sai da ya sai mata sweets sanan ta yarda suka tafi.. mummy ta tarar a zaune tana kuka kamar ranta zai fita, duk sauran yaran na kanta suma suna sharar kwalla, dakin mamma tazo shiga da sauri, bin bayanta Husna tayi dan ta hana ta shiga, kafin Husna ta karasa zainab ta isa cikin dakin, kwance ta samu Mamma a rufe cikin likkafani, a gigice ta karasa jikinta, girgizata ta shiga yi tana fadin Mamma me ya sameki? meyasa naga suna ta kuka a waje, duk da karancin shekarunta tasan menene mutuwa domin tun rasuwar mahaifinta tasan mecece kalmar, kuma ta fahimci in mutum
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156