Chapter 2
Chapter 2
sallah, karar da wayarshi keyi ne ya dawo dashi cikin duniyar tunanin da ya tafi, hannu ya zira cikin aljihunshi ba tare da ya d'ago ba ya danna ya Kara a kunnenshi, Assalamu alai-- "hello Ya Hafiz ta katse shi cikin kaguwa, dago kanshi yayi cikin firgici yace "Nadiya Lafiya,? fizge wayar mamma tayi tace "Hafizu kana Ina ne, duk abunda kakeyi ka barshi ka dawo gida, mikewa yayi da sauri ya Sanya silifas dinshi, ya kalli abokin aikinshi yace "Haladu dan Allah ka Mik'a min baron nan gidan oga lukman in har ban dawo da wuri ba, Haladu yace "lafiya dai ko, "walhy ban sani ba mamma ke kira na, ya karasa fadi yana tafiya da sauri , "Allah yasa lafiya haladu ya fadi da karfi dan Hafiz ya kusa karya kwana, zuciyarshi cike take da fargabar abinda zai je ya tarar a gida... Hello Baffah, an yini lafiya, baki har kunne baffah "yace lafiya lau ya sallar, "sallah alhamdulillah, "Dan Allah Baffa kace ma su Husnah su biyo MUSADDIQ na aiki Haruna driver, to bakomai daga ya karaso zansa su taho saboda dare, "kana nufin har yanzu bai zo ba baffah, baffah yace "eh to sunce min sun ganshi d'azu amma ni har yanzu bansa shi a idona ba, ikon Allah ta fadi hade da gyara zama, ya rigasu fita gida fa, kuma saida na mishi kashedi akan yawo, Yanzu haka yana can gurin abokan banza, amma dai ya basu sak'onka ko? , "ko kusa bai basu ba, baffah ya fadi had'e da yak'e wanda yafi kuka ciwo dan ya kosa yaji makwafin kudin da ya ba jikokinshi da Karin wasu a aljihunshi, "karka damu baffah bari in kirashi inji inda ya tsaya, "too bakomai Kar dai ki matsa mishi kin San yaran yanzu saida lallami, haka ne baffah nagode a gaida Goggo,"to zata ji Nima na gode,.... Kiran Musaddiq ta shiga yi, abin ya d'aure mata kai da taji wayoyin shi a kashe, lallai yau zan bala'in sab'a ma Yaron nan, duk fadan da na mishi akan shirman partyn nan baiji ba ko, Allah ya kawo shi gida wallhy Mai rabani dashi sai Allah ta wurga wayar cikin jaka ta d'auki gyale da mukullin mota ta fita... "ji nake kamar a mafarki mamma, shafar kudin ya sake yi yace "ban taba tunanin zan rike irin wadannan kudin ba a rayuwata, Mamma da farin ciki ya mantar da ita damuwa da yunwa tace "kaidai bari, Allah kenan maji rokon bawa, duk yadda mutum ya kasance cikin kunci da bakin ciki to in ya dogara da Allah sai ya samar mishi mafita,, Hafiz yace "haka ne mamma, to yanzu ya zamuyi da kudinnan, "shi nake tunani hafizu, mu jira babanku ya dawo sai musan abin yi dashi, dubu biyu ta ciro cikin kudin tace je kayo mana cefane da wannan muyi abinci kafin ya dawo, Zainab da ke kwance Kan cinyar Nadiya tace "anty Madara ta, Nadiya tayi dariya tace "kiyi hakuri yanzu za'ayi abinci muci, mamma na jinsu tayi kamar bata ji ba tace, "au Hafizu na manta ka siyo ma auta Madara kaji, Nadiya tayi murmushi tace kamar kinsan maganar da takeyi kenan, Mamma tace au haba, taho auta ta kinsan ni namiki alkawari kuma bazan manta ba,, haka suka kasance cikin farin ciki a ranar, ji sukeyi kamar babu kamar su a doron duniyar Allah SWT, Allah sarki, kud'in da bai wuce kudin naman wani gida ba shi ya Sanya bayin Allahn nan murna har suke Jin babu kamarsu...... Mrs Tijjani Shattima... [04/12 09:42] Meela Adeel: 3⃣ °ZUMUNCINMU A YAU ° BY Aysha Ya'u Kurah *******10:56pm****** Zaune yake cikin motarshi kafafunshi duk biyun na waje yana latsa wayarshi da ko minti uku baiyi da kunnata ba, text din mummy ya karanta yayi d'an murmushi had'e da shafa kwantaccen sajenshi, rufe wayar yayi ya sake duba agogo,… gyara zamanshi yayi ya rufe motar yace "na tabbata yanzu mummy ta isa k'asar Singapore ita da k'awanta cikin mafarki, tada motar yayi ya karaso kofar gida, kiran mai gadin su yayi a waya dan ya bud'e mishi gate, yana tsoron latsa hon ya dawo da mummy cikin kasar Nigeria, da sauri Mai gadin ya bud'e mishi, ya shiga yayi parking a gurin da aka tanada dan ajiye Motoci, Kiran waya ya shiga yi kafin ya karasa kofar parlon.. Badariyya na zaune tana buga game taji land line din dakinsu na Kara, pause ta danna ta Mik'e tana tsaki, "hello.. ta fadi cikin muryarta Mai cike da izza da isgili, "hey Badar zo ki bude min kofa kuma kiyi a hankali Kar mummy ta jiki kin gane ko, katse wayar tayi ba tare da ta amsa shi ba ta juya ta fita daga d'akin, d'akin mummy ta nufa, bud'e kofar tayi ta shiga ba tare da tayi sallama ba, dan a ganin Badariyya sallama ta talakawa ce,, hasken da ya gauraye d'akin ne ya farkar da mummy daga bacci, Mikewa tayi hade da mik'a tace "BADAR lafiya, yaya Musaddiq ne ya kira ni wai in bud'e mishi kofa.... Bawan Allah yana waje yana jiran Badariyya ta bud'e mishi kofa, ganin da yayi har minti 5 ta wuce bata bude ba ya fara mita cikin zuciyarshi, d'aga wayar yayi da niyyar sake kira yaji ana tab'a kofar, tura wayar yayi cikin aljihu ya k'arasa kusa da kofar fuskarshi d'auke da murmushi, "ina kika tsaya ne haka, har hakuri na ya fa---- maganar ta makale mishi a mak'oshi sakamakon ido hud'u da sukayi da mummy, zaro ido yayi ya had'iye wani mugun miyau, dariya ya fara yi yana fad'in mummy baki kwanta ba, tun d'azu Ina nan k'ofar gida a zaune ni da Tinau Mai gadi yana bani Labarin k'auye, sannan malam--- juyawa tayi ta barshi a tsaye, shigowa yayi ya rufe kofar ya bi bayanta da gudu, can gefe ya hango Badariyya tsaye tana mishi kallon raini, harara ya jefe ta dashi yace "tun kina yar ficiciya kin iya munafurci da makirci Ina ga in kin girma, wallhy kinji haushin rayuwar ki idiot,, tsaki taja ta wuce d'akinsu,, Kofar dakin mummy ya karasa, a hankali ya murd'a kofar ya shiga had'e da sallama, kusa da ita yaje yayi kneel down ya kamo hannunta yace "kiyi hakuri mummy, wallahi ba party na je ba, ina gidan su Mahmud tun da na fita daga gida, sai dare na bar gidansu na dawo kofar gida na zauna, Dan Allah kiyi hakuri banason wannan fushin please ya karashe a shagwabe,, bata tanka mishi ba ta zame hannunta cikin nashi tace "bani,, zuciyarshi na dukan uku uku yace "me zan baki?, K'ara tamke fuskarta tayi tace kud'in Baffa da na aike ka dashi, dakewa yayi yace "ni gidan mama suwaiba kika aikeni saidai ko driver kika aika gidan Baffa, "karka raina min hankali Musaddiq, kalleni da kyau banyi girman da zan fara mantuwa ba, dubu biyar na baka ka kaima "SUWAIBA" dubu d'ari biyu na Baffa, sai dubu Hamsin na k'anwar k'awata "Hajiya Nafeesa dake layin su suwaiba, bud'e baki yayi yace "Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, mummy ai banji duk lissafin da kika min ba, ni dai sunan mama suwaiba kad'ai naji, na bata dubu dari biyu da biyar, ga dubu hamsin nan a aljihuna
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156