Chapter 26
Chapter 26
wa aka kashe? Ke ko Ma'u baki bani gurin zama, duk irin gajiyar nan da na kwaso ki barni a tsaye, Tsaff ma'u ta gano manufarta, taja hannunta tayi hanyar sakarkari da ita, saboda tsaho irin na ma'u tsaff ta hana haire damar waigowa, Labarin abin da ya faru ta fada mata hade da cewa "yanzu Hardejo yasa a dauke gawar yaron ayi mata sallah, dan ance saurayin musulmi ne, kuma ya wakilta wani yaje can tsaunin ya nemo inda yan uwanshi suke a fada musu, cike da damuwa Haire tace "ni yanzu yar buduwar nake tausayi, dan shaho na can ya tashi hankalin gari, kuma yace duk wanda ya dauketa ya boyeta in dai ya samu labari sai ya hallaka shi, kinsan shaho, a wala hore na,, duk dakiya irin ta ma'u saida cikinta ya dauki kugi saboda yadda take jin labarin shi tun zuwanta garin da aure ya kawota,, magana ta fara yi jiki a sanyaye tace "Haire am kinsan babu abinda zan boye miki, gyada kai Haire tayi tace "nasani ma'u, yauwa tace tana mai gyara tsayuwa, ta kwashe yadda akayi Baffa ya kawo yar makka gidan da kuma amfanin da take ganin yar makkan zata yi mata, ta karashe da fadin duk irin kokarin da zanyi in ga na samu wani abu a gurin iyayenta da ita zanyi, sannan kema bazan barki a baya ba, rabawa zamuyi daidai in kin yarda zaki rufa mana asiri, Ajiye kwarya Haire tayi ta zauna tana washe baki tace "wannan ai karuwar mu ce duka, ke ni har na fara hango ni a kasa mai tsarki, yadda su Hardejo suke fadin kasar ace muma gamu a cikinta, shewa sukayi dukkansu Ma'u tace "ai kaff kauyen nan sai sun dawo yi mana bauta, ke dai ki bani hadin kai mu samu abinda muke so, yanzu bari kiga sarkar da na dauke mata na hadata da tarkacen tawa, "aiko dakko ta mu gani, kin gani, ashe dai dama gaskiyar Hardejo da yace musulunci dadi gareshi, gashi nan cikin kwanaki kadan da karbarshi mun sami damin arziki, dariyar murna ma'u tayi ta wuce daki inda take jiyo kukan boddo, rashin ganin Baffa a dakin baisa ta kawo komai a ranta ba, ta dauki Boddo Halima ta duba gurin da ta ajiye sarkar taga wayam ba komai, dube dube ta farayi a gefen da tayi ajiyar, nan ma bata ga komai ba, a kidime ta fito da sauri tana kiran sunan Baffa, Rashin ganin bakuwar a inda ta barta ne ya kara daga hankalinta matuka, bayin gidan ta duba ko tana ciki, nan ma taga wayam babu kowa, gurin Haire ta koma jiki a sanyaye tace "Baffa ya dauketa a gidannan, dama yace zai koreta na hanashi, shine ya faki idona ya aiwatar, shi tsoro gareshi, daya barni da shaho ni nasan yadda zanyi inyi maganinshi, yanzu gashi ya janyo min asarar sarkar gwal da kyautar da iyayenta zasu mana in sunzo daukarta, Cike da kunan rai Haire da ta gama hango kanta a wata duniyar tace "amma Baffan Bingel bai kyauta mana ba, badan sunan annabin Hardejo gareshi ba da sai inyi kokwanton amsar musuluncin shi, tunda ai addinin Hardejo yace mu sowa dan uwanmu abin da muke sowa kanmu, jugum dai ma'u tayi tana bawa Boddo nono, tunanin ko ina mijinta zai kai yar Makkah ne ya cikata ya hanata magana..... Shi kuwa Baffa jin hirar da sukeyi da Haire ne ya sashi dauko sarkar da rigarta ya rufe mata fuska hade da kamo hanunta suka fita a gidan, Hanyar gidan yayanshi Hardejo yayi, duk wanda ya gansu a hanya sai yayi tunanin Ma'u ce, wasu a ganinsu wani abu ne ya faru ta rufe fuskarta take kuka, babu wanda ya ganeta kasancewar ma'u ma fara ce sosai, saidai farin nasu ba iri daya bane.. A kofar gida ya samu Hardejo yana koyar da samari karatun Allo, can ciki ya shige gurin matan shi, aiki ya samesu sunayi dukkan su a tsakar gidan, dakin uwar gidan ya shige kai tsaye tare da ita, ganin su a haka ya sa uwar gidan cire hannu a aikin ta wankesu tabi bayansu dan jin ko lafiya taga Ma'u haka, A tsaye ta sameshi yana safa da marwah a cikin dakin, yana ganinta yace "yauwa me babban suna, dama ke nake jira, taimakona nazo kiyi, zama tayi kusa da budurwar da take tunanin ma'u ce, tace "me ya sameki ma'u? Zama yayi daidai kafarta ya bude fuskar budurwar yace ba ma'u bace, bakuwa ce wacce rayuwarta ke cikin hatsari, labarin abinda ya faru kaff ya kwashe ya fada mata har dalilin da yasa ya kawota gurinsu, ya cigaba da fadin "nasan Shaho bashi da karfin da zaizo gidan nan yace zai dauke ta ko ya mata illah, gata nan zan bar miki ita, domin Allahn Hardejo ki kula da ita har iyayenta suzo daukarta,,, A tsorace Aisha (mai babban suna) ta kalli budurwar tace "a wani gari take? Inafa zan san daga inda take, Baffa ya fadi cike da zullumi, gyara zama tayi tace "to babu matsala, na samu labarin abinda ya faru sama sama dazu, Kuma naji ance malam ya tura aje a dauko gawarshi mutanen shaho sun hana sun zauna jiran dawowar budurwar ko wanda zai dauki gawar, cike da tausayawa ta kalli budurwar tace "ya sunanki, Baffa yayi dariya yace "ai bata jin komai, larabcin kadai na lura take ji, da yake Aisha ta dade cikin musulunci, babanta babban malami ne a jalingo, kuma sanadiyyarsu Hardejo ya musulunta har aka bashi aure, tace "maa ismuki ya ukhtee... cike da jin dadi budurwar tace "ATIKA " *ATIKA SHEIK SAHEEB SAIFUDDEEN* Juya sunan Baffa yayi tayi yace "kai ilimi akwai dadi, yanzu kinga sai musan labarinta ta dalilinki mai babban suna.... Mikewa Aisha tayi tace "bari in kawo mata abinci taci sai tayi sallah, kaga magariba ta kusa.... Bayan sallar isha'i kowa ya nutsu a gida, kuka da karai kainin shanaye kadai ke tashi a cikin gidan, matasa da yaran gidan duk suna zaure suna daukar karatun dare, yayin da wasu daga cikin malaman hardejo suka wanke gawar Habeeb da suka samu daukowa da kyar, hade da suturceta kamar yadda hardejo ya koya musu... Zaune yake cike da damuwa ya zurawa abincin gabanshi ido, "mutanen kauyen nan har yanzu imani bai gama ratsasu ba, duk irin fatawar nan da ake badawa bazai sa su hankalta su saduda ba, Hannu yasa a sama yace " *YA ALLAH DUK WANDA ZUCIYARSHI TAKE A KESASHE BATA DA NIYYAR RUSSUNAWA KUMA BA MAI SHIRYUWA BACE YA ALLAH KAYI MANA MAGANINSU DA GAGGAWA* AMEEN suka amsa dashi dukkansu, Adduoi yayi sosai akan duk abinda zai zamto barazana akan alummar musulmi Allah ya kauda shi.... ****** Cikin Harshen larabci take bawa Aisha da Hardejo labarinta... Sheik Saheeb Saifuddeen shine sunan mahaifina, dan asalin kasar cairo ne, babban malami ne kuma dan kasuwa wanda ake ji dashi a egypt.. Ummuna ta rasu shekara shida da suka wuce gurin haihuwar kanina, ummuna mahaifinta dan cameroon ne, mahaifiyarta ce yar cairo, kasancewata babba gurin mahaifina yasa yake ji dani fiye da kowa,, Tun bayan rasuwar mahaifiyata aka aura mishi kanwarta Ummul khair saboda ta kula da kanina, tun daga lokacin rayuwa ta fara sauya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156