Chapter 38
Chapter 38
da babu mai zuwa gurin, kuka takeyi sosai hade da karatun qurani, tasan in har ba'a ganta ba to tabbas baza'a daura mata auren ba... Zufa Baffa ke sharewa yana fadin "ina tace miki zata, kukan munafurci Ma'u ta kirkiro tace "bata fada min ba, nidai naji Leemah na cewa Suwaiba tace "in aka mata aure saita kashe kanta, salati Baffa ya saki yana fadin yarinyar nan so takeyi ta kunyata ni, duk irin mutanen da muka tara a kofar gidannan so takeyi lallai sai na kunyata, Matsowa kusa dashi ma'u tayi tace "tunda tace bata sanshi a hakura mana, Wani kallo baffa yayi mata yace "so kikeyi in zama karamin mutum, kinsan adadin manyan masu kudin dake zaune a kofar gidannan suna jiran a daura auren nan, kawai kuma sai inje ince musu amarya ta gudu, Sake matsowa tayi tace "to ya zakayi, saidai ko dan mu fita kunya a hada auren da Zainabu, kaga shikenan asirinka a rufe, ita kuma tunda rayuwar da ta zabarwa kanta kenan shikenan sai taje can tayi, dan taga tana da farin jinin ne, in kayi tafiya itace wannan saurayi itace wancan, cike da bacin rai Baffa ya hau kan zancen Ma'u ya zauna, ya fita yanata sababi cikin zuciyarshi.. bai nemi shawarar mukhtar ba dan baisan samm ya rasa shi a matsayin siriki saboda tarin hidimar da yakeyi mishi, gurin daurin auren yaje ya zauna aka fara gudanar da auren kamar yadda addini ya tanada, saida aka daura aure akayi komai sannan maroki ya fara fadin, "Tuwon girma miyarsa nama, yau naga auren da ban taba ganin irinsa ba, jama'a ku shaida an daura auren *ZAINAB* DA *MUNTARI* akan sadaki naira na gugan naira har naira Dubu Uku.... Ba Mukhtar bane kadai ya girgiza, hatta Mahaifinshi saida ya tafi tunanin Zainab ko Suwaiba...... Mrs Tijjani Shattima..... [07/03 2:02 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣0⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Alhaji ku yafe ni!, na yanke hukunci ba tare da neman yardarku ba, dan Allah ku gafarce ni, nayi hakan ne dan in fitar damu daga kunyar jama'ar da muka gayyata, Baffa ne ke jero musu bayanan ban baki lokacin da suka kebe da Alhaji Garba yayi mishi tambayar dalilin sauya akalar daurin auren, share hawaye yayi ya cigaba da cewa, "yarinyar nan taso ta wulakanta ni, sai Allah yasa ina da 'ya'ya matan da basuyi aure ba, kuma bana son mutum kamili kamar Muntari ya subuce min, da zainab da Suwaiba duk daya ne, uwa daya uba daya suke, dan haka kaga wanda yazo daukar suwaiba kuma ya samu zainab ai duk daya ne tunda tsatso daya suka fito, kasa Magana Mukhtar da zuciyarshi ta kai kololuwa gurin bacin rai yayi, har lokacin baiji ko daya daga kwatan son da yake ma Suwaiba ya fita a ranshi ba, da yaji Babanshi na kokarin amincewa da batun yayi saurin cewa "Abba, dan Allah kuyi hakuri, ni suwaiba kadai nakeso, in aka daura mana aure da ita nasan zata hakura ta zauna dani! "Naso yin hakan,amma abin yaci tura saboda guduwa tayi tabar gidan, Baffa ya karashe cike da damuwa, wani abu Muntarin yaji ya soki kahon zuciyarshi, har kiyayyar ta kai haka, ta ina ya gaza da ya samu macen da ta nuna mishi irin wannan kiyayyar, me ya rasa, babu abinda bai mallaka ba na daga dangin kyau, ilimi, gayu, uwa uba arziki na jama'a da kuma na dukiya, me yasa Suwaiba zata rusa tanadin da yayi wa rayuwarsu, yanzu kenan dukkan mafarkinshi zai zamto cikakken mafarki, kenan babu ko daya a cikin mafarkinshi da zai zamto gaskiya, baisan Hawaye ya fito a cikin idanuwanshi ba saida yaji duminsu a kuncinshi, mikewa yayi ya fita zauren hade da share hawayen fuskarshi, motar da suka zo shi da abokanshi ya shiga hade rufe fuskarsa dan hawayen sunki daina zuba, Allah ya sani ba karamin so yake yi ma Suwaiba ba.... Godiya sosai Baffa yayi wa Baban muntari saboda fahimtarshi da yayi,da Kuma alkawarin da yayi mishi na yarshi bazata wulakanta a cikin zuri'arshi ba, ko yana so ko baya so dole ya karbeta hannu bibbiyu a matsayin matarshi, dan zuri'armu kaff babu me wulakanta mace... Sai dare suwaiba ta dawo gida lokacin Ma'u na buduri da makota ana shirin kai Zainab dakin miji, kallo ne ya dawo kanta, daga mai yi mata habaici, sai mai yi mata kallon marar hankali, dakin Baffa ta shige a darare, zaune ta sameshi yayi tagumi yana tunanin ta inda zai fara neman suwaiba, jin muryarta ne ya sanyashi waigowa da sauri, sanyi yaji a zuciyarshi da ya ganta lafiya kalau, a fili kuwa fada ya rufeta dashi, saida yayi mata cin mutunci sannan a karshe yace "Wallahi, wallahi, kinga rantsuwar nan, bata da kaffara, bazaki kara daga kafarki kije makaranta ba, kina cikin gidannan har sai na samu wanda zan bawa ke sadaka, ke ba takamarki kinada farin jinin samari ba, kin daukesu kamar rigar canji, to ki sani kin jawa kanki a gurina, fita ko nan da kofar gida ne ban yarda kiyi ta ba, sai ki zauna a gidan tunda kin zabi butulcewa Allah da ni'imar da yayi miki, tashi ki fita ki bani guri mutuniyar banza mutuniyar hofi, tashi tayi ta fita da gudu tana rusa kuka, a kofar dakin tayi karo da masu kai Amarya ana wakar "Ayye mama", ta gefensu tabi ta shige dakinsu ta kara bude wani sabon babin kukan.... (oyoyo talauci inji Meela) Rayuwar auren Zainab da Muntari kadaran kadaham, sam baya wulakanta ta saboda ya karanci hakkin mace akan miji, kuma mahaifinshi ya sake tunasar dashi, Da fari ta dan samu matsala da mahaifiyarshi domin sam bata san zainab, gani takeyi an lika mishi ita ne dan a cuceshi, saida "Abba" yayi mata nasihar cewa matar mutum kabarinsa, kuma wata bata auren mijin wata, sannan ne ta dan sakko, amma duk da haka bata cika bata muhimmanci ba, biyayyar da zainab ke mishi ne ya sanya shi sake sakewa da ita, wani lokaci yakan tuna suwaiba wani shashin zuciyarshi yaji yayi mugun tsanarta, wani shashin kuma yaji ta ciki a killece, ya sha in zai ambaci sunan zainab yace suwaiba, in ko yayi tafiya to fa sai ya cirewa suwaiba tsaraba, kome zaiyi da ita yake hadawa yayi, wannan abu shi ya kara dungunzuma zuciyar Zainab taji gaba daya Suwaiba ta fice a ranta, kullum cikin kulli Goggo take dan dai kawai kar auren yarta ya mutu, a irin zaman da sukeyi Zainab ta samu ciki har ta haihu, haihuwarta ita ta kara daraja ta a idon iyayenshi da shi kanshi, sannu sannu ya fara fitar da Suwaiba a cikin ranshi, saboda samun zuri'a da ya farayi. Saida Zainab ta jera mishi 'ya'ya Mata uku a karancin tsakani (gwarne ) cikin shekara hudun aurensu, Reemah ce Babba, sai Radiya Sai Raudha, a lokacin da take da cikin na hudu ne Muntari ya saduda ya mika mata ragamar rayuwarshi, domin yasan yanzu indai za'a kirashi to itace ta biyun da za'a kira a rayuwarshi.... Ita kuwa suwaiba baiwar Allah ta zama baiwa ta gidi, komai na gidan ita takeyi, babu makarantar islamiyya, babu fita cikin gari, iyakarta shagon buzu Adamu mai gadin jikin gidansu, duk irin kyawun da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156