Chapter 52
Chapter 52
momma kice su tafi zan kawo shi, cike da mamakinshi ta kashe wayar tace "zai miko shi inaga yayi bacci ne, nagode sosai Raliya, a'a haba Anty babu godiya a tsakaninmu anty Raly ta fadi tana murmushi, sallama su Nadeeyah sukayi mata ta amsa cike da fara'a, bayan Nadeeyah tabi da kallo tana Nazarin wasu abubuwa, har saida ta kurewa ganinta sannan tayi ajiyar zuciya ta fara bude kulolin abincin.... Mrs Tijjani Shattima [15/03 12:04 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣7⃣ By *Aysha Ya'u kurah* *JIGON RAYUWA* Kallon Mamaki Anty Saude ta bishi dashi, kayan da ya shiga dasu sanye a jikinshi ba dasu ya fito ba, wannan karan Ash Shadda ce a jikinshi, yayi kyaun da shi kanshi ya yaba, babu ta inda Taheer bai hadu ba, ya hada komai da duk namiji zai yi tunkaho dashi, matsalarshi daya ido, ciwon idon da ya samo asali tun yana yaro gurin wasansu na yara, babu inda ba'a kaishi dan duba idon ba, saidai ya dan samu sauki amma bazai bar ciwon duka ba, a karshe har iyayenshi suka hakura suka dawo asibitocin ido na nigeria, a nan ne suka daurashi kan magunguna har idon yayi kyawu sosai, da taimakon Allah da taimakon glasses dinshi da suka kara fito da ainihin kyawunshi yake ganin abun da ke nesa.. Zaunar da Fadeel yayi akan kujera ya dauki nama daya cikin soyayyun naman da Anty Raly ta kawo, zama yayi kusa da Anty saude ya kai naman bakinshi yace "Momma zan fita, "Ina zuwa kuma? ta tambaya hade da ajiye plate din hannunta, Murmushi yayi mai matukar kyau yace "zan mika Fadeel gida, sannan zan je aiken da zuciyata take ta min kullum, "Hannunshi ta kama da sauri tace "Fara isar min da aiken TEE, fada min sakon in taya zuciyar taka adduar samun karbuwar sakon, nata hannun ya rike shima zuciyarshi na kai kawo, farin ciki ne cike a cikinta na ganin tana gab da samun abin da take so, lumshe idonshi yayi , kana hango yanda gashin idon ya kwanta ta cikin glass yace "i'm in love Momma, wani irin numfashi ta saki wanda zai tabbatarwa da mai kallonta tana cikin matsanancin farin ciki, "wacece Taheer? wacece wannan? ya Allah kayi mata albarka, share hawayen da ya zubo mata tayi, tace "bani labarin ta Tee, "murmushi yayi dan dama yasan yadda zatayi reacting kenan, yace "calm down Momma, with time zaki santa, kuma nasan zaki sota, ni dai addua'arki nake bukata, ina son ki dage da addu'ar samun nasara, inason zuciyata ta kasance da ita a duk bugun numfashina, tun ranar da fara ganinta har zuwa yau kaunarta ce ke kara tasiri a cikin ruhina, "rungumeshi tayi sosai tana fadin Alhamdulillah a jere har sau uku, jin kukan da takeyi yana neman yayi yawa ya sashi saurin raba jikinshi da nata, hannu yasa yana share mata hawayen hade da girgiza mata kai, a shagwabe yace "kina so in bata kwalliyata ne, sai ma na fasa in bawa zuciyata hakuri tunda aikenta nasa min ke kuka, dan mari takai ma fuskarshi tana dariya tace "tashi maza ka tafi, Allah ya baka dukkan sa'a my boy, daukar Fadeel yayi yace "Ameen Momma, kallon farin ciki ta bishi dashi hade da mikewa ta isa gaban hoton mahaifinshi, rau rau idonta yayi tayi saurin maida hawayen hade da fadin "tun bayan rasuwarka Taheer dinka bai sake yin farin ciki ba, yau!! a karo na biyu a rayuwarshi na ganshi cikin farin ciki, kasa controlling hawayenta tayi tace "we missed u alot Abba, Allah yayi maka rahama, adduoi ta shiga jerowa mijinta da danta, saida ta gama ta share hawayenta ta kira Abida mai mata hidima dan ta tattara parlon.... Sau biyu ya taba shiga gidan Anty Raly tun zuwanta unguwar, motar da ya dauko daga gida ma ta musamman ce kai kace garin zai bari ba kusa da gida ba, sai da yayi zaman minti uku a ciki sannan ya kashe ya dauki Fadeel, mai gadin na ganinshi ya tsuguna har kasa ya gaisheshi dan babu wanda baisan dan gidan Hajiya Saude ba a unguwar, bude mishi kofa yayi ya shiga, Baya yaja zai tsaya ya hango Husnah ta fito ta nufo gate din, tana ganinshi ta kara sauri tana fadin "uncle da kanka ka kawo shi, mika hannu tayi ta dauki Fadeel hade da ce mishi tana zuwa, mai gadin ta kira tace "ina lawalli, kace yaje ya siyowa Anty Gas, cikin girmamawa ya amsa ya fita da niyyar zuwa kiran lawali driver, Dawowa gurin Taheer tayi ta sake gaisheshi, tambayoyi ta fara jefo mishi, "uncle dama kai dan Anty saude ne? ai na santa, bansan kai danta ba, kasan last year ka fara teaching a school shiyasa bamu san kai danta bane, she is very nice, kasan akwai lo--- katseta yayi yana dariya yace "ashe haka kike da surutu, to tunda bazaki bani gurin zama ba bari in tafi, da sauri tace "laaa sorry uncle muje dan Allah, bai bata lokaci ba ya bita hade da addu'ar Allah ya bashi karfin gwiwar sanar da ita, parlon Baban Fadeel ta bude mishi tayi mishi iso har ciki ya zauna, har zata zauna sai tayi saurin mikewa tace "bari in kawo maka ruwa, murmushi yayi yace "na dauka zama zakiyi da sai ince ashe baki iya tarbar baki ba, dariya tayi ta wuce kitchen, Suna shiga kitchen Fadeel ya saki Kashin da ya fito daga pampers har rigar Husnah, wani irin ihu ta saki wanda ya sanya Nadeeyah da Anty Raly zuwa kitchen din, dariya Raliya tayi na yadda Husnah ta bata baki hade da tale riga da kafarta, da sauri ta dauki Fadeel da ya fara bata mata kitchen da kashi tayi daki dashi, kallon Nadeeyah Husna tayi tace "dan Allah ki kai mishi juice parlor, bata tsaya yi mata bayani ba ta wuce daki tana ware kafa, dariya Nadeeyah tayi ta shirya juice a tray, duk tunaninta Baban Fadeel aka shiryawa abinci a parlon kafin ya dawo, bata damu da yadda gashinta yake a bude ba saboda tasan bai dawo ba, gyara wanda ya dan zubo ta gefen idonta tayi ta wuce parlon, sam bata kula dashi ba saboda kujerar da yake zaune tana baya, duk wanda ya shigo parlon in ba ya lura dakyau ba bai kula da na zaune a kujerar, ganin babu abinci a parlon yasa ta dube dube, sai da ta razana saboda ganin bazata da tayi mishi, da sauri ta ajiye tray din jiki na rawa hade da bugawar kirji tace "ina wuni uncle, bai amsata ba ya tako har inda take tsaye shima kirjin nashi bugawa yake yi sosai, "murya can kasa yace "bakina ya kamata ya fara furta wannan, an yini lafiya *Umm Nadeeyah* Wani abun taji ya tsarga mata tun daga kwanyar kanta har tafin kafarta, yadda yayi kiran sunanta ta ya sake kashe mata jiki dan duk duniya banda Babanta babu mai kiranta da Umm Nadeeyah, bata amsa shi ba ta fara tafiya da niyyar barin parlon, *Nadeeyah* ya sake fadi a hankali yana kallonta, tsayawa tayi kamar zata saki fitsari saboda tsabar tsoron yanayin shi, bai karaso inda take ba yace "dawo ki zauna, akwai maganar da nake so
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156