Chapter 155
Chapter 155
zuciyarta, ko ba komai hankalinta ya kwanta tunda Junior ya saki jiki da mahaifinshi, ko a yanzu tasan Musaddiq zai samu saukin kaso 50 cikin ďari... Cikin sanďa ta isa gurin gadon dan gyarawa Junior hannu dan gab yake da famawa Musaddiq ciwon dake hannunshi wanda hakan zaiyi sanadiyyar katsewar baccin da ta tabbatar yana jin dadinsa, da dabara ta gyara mishi taji ya rikota yana sambatun "Daddy am very angry with u, i will nt talk to u ever again, Dariya tayi haďe da sumbatar kumatunshi ta zame hannunta cikin nashi, bargon dake jikinsu ta gyara musu ta shafa kan Junior ta dago da niyyar yin hanyar waje, kamar gizo haka taga idon Musaddiq a buďe, sake juyowa tayi ta kalleshi tagansu a rufe, ajiyar zuciya tayi ta fara tafiya dan zuwa kofar da zata sadata da waje, "Nadeeyah... Taji ya furta a hankali wanda ya sanya hantar cikinta kadawa, tsayawa tayi cakk a gurin ba tare da ta amsa ko ta waigo ta kalleshi ba.. jin har minti uku baiyi magana ba yasata juyawa dan ganin halin da yake ciki, wannan karan a juye yake idanuwan nan a rufe wani sabon bacci ne ma yayi gaba dashi wanda daga gani kasan yana cikin mayen magani ne, da sauri ta murďa kofar ta fita saboda kwalla da taji ta taru a idonta, wannan wacce iriyar zazzafar jarabawa ce, ya Allah ka kawo mana mafita baki dayanmu dan alfarmar annabi Muhammad s.a.w..... Gidan Alhaji Mukhtar ya zama tamkar gidan zaman makoki, kamar babu wata hidima da za'ayi a cikinsa nan da kwana biyu, Anty Reemah dasu Raudha sune kadai ke hidimarsu bisa ga umurnin Daddy, sai kuma Mummy da a yanzu takan samu shigowa duba jikin Musaddiq, duk da bata samun koda gaisawa da Daddy hakan yayi mata daďi tunda ya yafe mata kuma ya yafewa 'yayanshi yana sakar musu yanzu, a yanzu bata da burin da ya wuce taga rayuwar Musaddiq ta inganta, ta rasa kalmar da zata roki Nadeeyah dashi ta yarda da auren ďanta wanda ta zama sila a rabuwarsu, gashi abun da tayi yayi sanadiyyar sanya shi cikin tsakiyar rayuwa da mutuwa... A yau ma kamar kullum bayan ta gama gyara ďakin Goggo inda take kwana ta shirya tsaff dan tafiya dubo Musaddiq sannan ta zauna ayi kamun Nadeeyah da ita, tana rufe kofa ta jiyo muryar Badariyya wacce a yanzu Yareemah Suhail ke fitowa da ita ya kawo ta har gida tun dawowar Nadeeyah,, kwancen kayan da su Husna suka bata shi ta sanya tayi kyau abunta, sannan su suwidi suma sunyi kyansu dan a yanzu suna samun sake da kuma abinci wanda duk tazo sai yan uwa sun sai mata, "A'a Badariyyah kece a gidan, to juya muje ki duba jikin Musaddiq daga nan ki jira ayi kamun Nadeeyah dake, cike da damuwa ta juya suka fita suna tattauna damuwar da Musaddiq din ke ciki a sanadinsu, Badariyya a cikin ranta ta dau alwashin kebewa da Nadeeyah ta faďa mata abubuwan da tayi wanda ya rabasu, babu mamaki taji tausayinshi in tasan baya cikin hayyacinsa sanda yayi sakin.... Bayan ta gama sauraron kalaman Badariyya wanda takeyinsu cike da nadama tace "Badariyya abun da kukayi bai isa ya raba mu ba, tunda kika ga mun rabu to tabbas Allah ya rubuta rabuwar tamu ne a lokacin, sannan a yanzu in na ki uncle Taheer shi munsan halin da zai shiga, dan Allah ku fahimceni, ni kadai nasan halin da nake ciki, ku tayani addu'a nasan komai zai daidaita da yardar Allah... Share hawaye Badariyya tayi tace "Zamu tayaki, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.... Karfe huďu da yan mintuna Nadeeyah ta shirya cikin wani lace mai kyau da tsada cikin kayan da Taheer ya dinka mata, Anty Raly ke tsaye a kanta tana gyara mata kwalliyarta haďe da yi mata ďauri, wata farar alkyabba mai adon yellow ta dauko ta daura mata a kanta wanda hakan ya sake fitar da kayatuwar da amaryar tayi, jan lallen da akayi mata ya rinu sosai ya koma dark maroon hakan ba karamin sake fitar da suffar yatsunta yayi ba, zaunar da ita Anty Raly tayi tana jiyo sautin maganganu yan biki daga waje,, Cike da masifa take shirya su Nour tana daka musu tsawar su tsaya ko ta zanesu, a hankali Nadeeyah ta janyo hannun Abee tace "Kawo in shiryashi Husna, "Barshi.. kadai ta faďi haďe da janyo hannunshi ta sa mishi irin kayan dake jikin Hafeez, oya a je ayi wasa, banda barna da bata jiki, mikewa tayi da niyyar shiga bayi Nadeeyah ta riko hannunta, "Husnah nasan ni mai laif--- Lokaci na kurewa Nadeeyah, baki da laifin komai kaddararmu ce tazo a haka, na kasa dai jin saukin zuciyata ne shiyasa har yanzun kika ganni haka, with time in shaa Allah komai zai daidaita, Husnah ta katseta fuskar nan murtuke tamkar wacce akayi ma mutuwa.. ganin Nadeeyah na kokarin sake magana yasata zame hannunta daga cikin nata ta faďa bayi, wani irin kuka ne yazo musu a tare mai cin rai, saida sukaci suka koshi sannan Husnah tayi wanka ta fito ta shirya da sauri sauri tayi waje.... Sai biyar da kusan rabi dangin Taheer suka zo sa lallen amarya, sai da suka biya kawayen amarya wacce Amal ce kaďai sai Raliya da ta shiga cikin zancen, turaruka masu kamshin gaske suka karar a jikinta sauran yan uwansu na Agadez wadanda suka ji dadin ganin Nadeeyah da Hafeez suna rangaďa guďa, kwaryar nono wacce suka kawo gidan kanta ta kai hamsin, banda sauran gararrakin arziki da suka kawo, sunci sun sha a gidan sosai dan komai nasu daban aka ware musu, sai bayan Isha'i motocin da suka kawosu suka maida su.... A daddafe Musaddiq ya amsa gaisuwar Taheer wanda ke tsaye rike da danshi cikin tsadajjiyar shadda iri ďaya, lallaba Junior ya shiga yi bayan ya fuskanci irin fushin da yakeyi dashi, sannan kuma dan ya daukewa kanshi damuwar da ke cinshi tun kwana uku baya, wani mugun tari yaji Musaddiq nayi wanda ya sanyashi sakin hannun Junior ya isa gareshi haďe da dauko ruwa yana faďin sannu, ga ruwa kasha, runtse ido Musaddiq yayi haďe da kauda fuskarshi gefe, ya riga ya gama yanke duk wani hukuncin da ya dace, yasani a yanzu ganin gobe a gareshi nada matukar wahala, a yanzu ya sadaukar da komai yasan Nadeeyah da ďanshi bazasu taba yin kunci ba tunda suna tare da nagartaccen mutum irin Taheer wanda a haďuwarka dashi ta farko zata tabbatar da hakan komin kinka dashi, dafe kanshi yayi da hannayenshi biyu saboda hawayen dake zubo mishi babu kakkautawa, Mikewa Taheer yayi dukkan lakar jikinshi a sake ya kama hannun Junior suka sauka kasa, a hanyar da zai sadasu da kofar fita ya haďu da Hilal da ya dawo daga rakiyar abokansu, shima duk ya fukace ya fita hayyacinshi kamar shine mai ciwon, "A'a yallabai har kun fito, ya faďi yana mika mishi hannu, "Eh dare nayi, Allah ya bashi lafiya, "Ameen Hilal ya amsa haďe cewa sai da safe mun gode, "Allah ya tashemu lafiya Taheer yace yana mai saka kafarshi a waje, A gurin motarshi suka tsaya ya kira number Nadeeyah wacce ke kan dadduma tana zubda kwallar da ta zame mata jiki,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156