Chapter 64
Chapter 64
tace "bani hankalinki nan, aure ya haramta tsakaninki da Musaddiq, Dariyar takaici Badar tayi tace "Haramta? Menene ya haramta shi, naga we are cousins saidai in baki son farin ciki na, Buge bakinta Mummy tayi da karfi hade da cewa "bance karki kara min maganar nan ba, Zafin buge bakin da zafin ganin zata rasa masoyinta yasata sakin wani irin Kuka, Inda take Goggo tayo tana tambayar dalilin kukanta, bata amsa ta ba ta cigaba da kukanta, Mummy ce ta tsuguna a gabanta zata fara rarrashi, kafin tayi magana ta katseta... "Cikin kuka mai cin rai tace menene ya haramta aurena da Yaya Musaddiq Mummy, menene shi, a iya sanina bake kika haifeni ba, nasan babu abin da zai haramta aurena dashi saidai in kema so kikeyi ki min gori akan asalina kamar yadda Daddy yayi m---- tassss.. mummy ta dauke ta da mari, itama kukan ne ya subuce mata ta rungumota tace "Allah ne ya haramta shi Badar, Asalinki bazai taba zame min abin gori ba saboda ke din makwafi biyu gareki a gurina, na diya da kuma kanwa, ke kadai ce jinin yar uwata wacce nake gani inji dadi, ban damu da ya kikazo duniya ba nidai nasan ina ganinki a matsayin LEEMAH, Cike da shashsheka Badar tace "to mummy ki yarda ya aureni, walhy in na rasa shi zan iya mutuwa, *Badariyya* *NONO* daya kuka sha da Musaddiq, babu aure a tsakaninku...... Wani irin zaman dirshan Badariyya tayi wanda ya tafi da duk wani ganinta na dan lokaci kadan, " *NONO DAYA KUKA SHA* Kalmar ke ta mata yawo a kwakwalwarta, duk da bata zuwa islamiyya sosai tasan haramcin auren, wasu zafafan Hawaye ne suka dinga ambaliyar fitowa a idonta, "NA MUTU, BANI DA SAURAN AMFANI, kalaman da ta dinga fada kenan kamar zautacciya, rungumeta Goggo tayi tace "bazaki mutu ba indai ina raye, Musaddiq ne ki kwantar da hankalinki zan san yadda zakiyi ki aureshi, anjima zanje gurin liman BADARU ya nemo wani hadisin da ya halasta aurenku, tashi kije maza ki wanke fuskarki, Tashi tayi kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta wuce bayin Goggo, Tashin hankalin da ta tarar a ciki ya sanya ta fitowa da gudu tana haki, "lafiya Suka hada baki suka tambaya, ina fa Lafiya bayi yayi kaca kaca, haba Goggo, dan Allah bakya yin flushing ne? Tabe baki Goggo tayi ta mikawa Zulai mai tayata aikin gida farar shinkafar tuwo dan ta gyara, ta waigo ta kalli Badar tace "tunda kinzo sai ki gyara ai, da tsufa na zanyi ta hakilon wankin bayi, "ay da sai zulai ta wanke ta fadi kamar zatayi kuka, murmushi Goggo tayi tace "kin sani sarai Zulai bata shiga min dakin miji bare bayi, matse fitsarin mararta tayi tace "gaskiya Goggo bazan iya ba, bazan iya zama har wata daya a nan gidan ba, "to ya zakiyi, haka nan zaki hakura, kije can dakin zulai ta tayaki gyarawa dan duk yayi kura, gani tayi kamar laughing stock suka maida ita ta nemi guri ta zauna kamar zatayi kuka tace "Mummy dan Allah ki kaini gidan Aunty Raudha ko Anty Radiya, "Lagos zaki bi Raudha, Radiya kuma kinsan halinta, duk yadda kuke shiri bazata raga miki gurin hidimar gida ba, kiyi zamanki anan na lokaci ne, Mummy ta fadi tana mikewa zata koma gida, Sallama tayi ma Goggo wacce ke amsata da kyar saboda laifukan da tayi mata ciki harda korar Badariyya da mijinta Yayi... Da kyar Goggo ta yarda Zulai ta wanke mata bayi, sai a sannan Badar ta shiga a kyankyame tayi fitsari ta fito da sauri, kan gadon Goggo ta kwanta tana maida numfashi.... "Fito kici Abinci, Goggo ta fadi tana fiffita tuwon a cikin faranti, badan taso ba sai dan tana jin yunwa ta sakko a gado ta fito waje, yadda yaukin miyar ke bin hannun Goggo da zulai yasa komawa daki da sauri, da karfi tace "Tuwo da rana tsaka Goggo, kuma miyar yauki kamar majina ta karashe fadi kar zatayi amai, wannan wace irin jarabawa ce, kudi ta fito dashi a jakarta ta kira Rilwanu ya siyo mata Abinci a restaurant mai kyau.... ko kallonta Goggo batayi ba ta cigaba da kai lomar tuwonta... Tunanin Musaddiq kwanta takeyi, ta ya za'ace babu aure a tsakaninsu, dan kawai sun sa nono daya, Allah yasa Liman ya gano wani hadisin da ya halasta hakan, in ba haka ba walalhi daga ita har shi saidai su mutu ba aure, dan duk wacce yayi yunkurin aura sai ta kasheta..... ******** Danna wayarshi yayi ya kira layin wayar da ya ba Nadeeyah a karo na ba adadi, har lokacin ba'a kunna wayar ba, juyi kawai yakeyi a kan makeken gadonshi, gaba daya ya rasa abinda yake mishi dadi, tun dawowarshi daga gidan su Nadeeyah ya kasa sukuni, ko abinci kwakwkwara bai iya kaiwa bakinshi ba, bacci kuwa sai dai dan barawo ne ya saceshi bayan ya idar da Sallar asuba, Ya gama sawa ranshi sha biyu nayi in yaji ba'a kunna wayar ba zai koma gidan koma me zai faru ya faru, Soyayyar Nadeeyah na neman yi ma zuciyarshi illa, yama za'ayi ya iya rayuwa babu ita, kallon kofar da aka murda yayi yaga Momma ta shigo dauke da kayan break fast, "Gud morning my Tee, Morning Momma, kin tashi lafiya? Lafiya kalau nd u? Nt bad ya fadi hade da mikewa zauna, 'Tee me yake damunka, yau baka fito ba kwata kwata, sannan jiya ina lura dakai dakyar ka tsakuri abinci, yar hirar da muka saba ma baka zauna munyi ba, tell me, meye matsalarka, Bazai iya boye komai na daga dangin farin cikinshi ko akasin haka daga gareta ba, gyara zama yayi ya rike hannuwanta, raunanannun idanuwanshi suka tara ruwa yace "Zan rasa ta Momma, Nadeeyah zatayi ma rayuwata nisa, Zan rasa farin cikin da ya ziyarceni a lokacin da na fidda ran zuwanshi, Fuskarshi ta tallaba da hannayenta biyu cike da tausayin shi tace "bazaka rasa ta ba, baka taba neman abu ka rasa ba Tee baza'a fara akan wannan ba da yardar Allah, ka kwantar da hankalinka kaci abincinka kamar ka sameta ka gama, Anjima da yamma zan kira *Kawu Tidjani* in fada mishi ya taho muje nema maka aure, Murmushin farin ciki yayi yace thank u Momma, Allah yayi miki sakayya da aljanna firdaus, Ameen my Boy, tashi maza kayi wanka ka shirya ka tafi gym wannan tumbin da ka fara ajiyewa ka gyarashi kafin ranar aurenka, shafa tumbin yayi yana dariya yace "ina tumbi anan Momma, sai dai in so kikeyi ya shafe da bayana, dariya tayi hade da mikewa tace "in kayi wanka kazo zan aikeka, gyada kai yayi yace "to Momma bari in fara wankan sai inci abincin.... ******** _Agadaz_.... *DIYA MURADUN AHMEDOO TIDJANI YALLO PALACE* Karar busar algaitar dake fitowa daga katafaren gidan shi ya bawa mutanen gurin damar mimmikewa saboda alamu ne na fitowar sarki, kirari dogarai suka fara yi cikin farasanci ana kodashi kamar yadda akewa sarakuna, Cikin daya daga jerin motocin da aka jera mishi ya shiga, nan ma fadawa suka dinga masa kirari har saida sukaga kurewar motar.. Wani katafaren gida motocin suka shiga, da sauri aka bude mishi kofa ya fito suka taka mishi har kofar parlon, suka murda ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156