Skip to content

Chapter 58

Chapter 58

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

suka faru kamar yadda kika ji na fadesu, yanzu kin yarda da maganata na cewa ban taba magana da mijinki ba, na yafe miki zargin da kikayi min, domin a yau bana fatan abun da zai bata min rai, a cikin farin ciki nake matuka na ganin Abdallah na ya samu abinda yayi shekara da shekaru yana kawaicin tambayarsa duk da nasan babu ranar da zata fito ta fadi ba tare da yayi tunanin rashin mahaifi ba, kullum in na kalli murmushinsa nakan hango damuwa a bayan murmushin, wannan suna da ake kiranshi dashi na *ABDALLAH HANNE*, yana matukar yi min ciwo, ansha zuwa gabanshi a kirashi da dan mace, duk damuwar da Abdallah zaiyi bai taba yarda yayi ta a gabana ba, sakin Goggo tayi hade daga hannun sama tace "Alhamdulillah, Allah zan cika maka alkawarin da na dauka na yin azumi duk ranar da ka cika min buri na... Murmushin farin ciki Baffa yayi yace "Alhamdulillah, Allah mun gode maka da ka dawo mana da saifullahi, ina ma Allah zai dawo da Suwaiba ta dawo taga dan biyun ta, sai dai kashh Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, kallon Mamaki Anni tayi ma Baffa tace "kana nufin Abdallah yan biyu ne? Kwarai kuwa Baffa ya fadi yana gyara zama, Gaba daya ya manta da Ma'u da bai samun katabus in tana guri, ya cigaba da cewa "su biyu mahaifiyarsu ta haifa, kamar yadda kika sani shi mun dauka ya mutu, to ashe shi din ne rayayye ita kuwa Suwaiba tabi mahaifiyarsu, watanni kenan da mutuwarta, ta rasu ta bar 'ya'ya uku, HAFEEZ shine babba, sai Nadeeyah da Zainab, "_Hafeez_" Papy ya maimaita wasu hawayen masu zafi suka biyo bayan furucinshi, "Tabbas jini ba karya bane Anni ta fadi tana share nata hawayen, soyayyar da Abdallah ya nunawa Hafeez daga ganin farko ashe ba haka kawai bace, ashe Jini ne yayi aikin shi, dalilin zuwan Hafeez karatu Gombe ba karatun bane, wannan haduwar itace silar zuwanshi, duk inda alkhairi yake baya taba faduwa kasa banza ta karshe tana goge idonta da gefen hijab dinta, waya Papy ya dauko ya danna number Hafeez, "Kana ina ne?, ya tambaya murya a shake, "Muna kofar gida, mu zo ne? Hafeez ya amsa cike da girmamawa, "eh kawai papy yace ya kashe wayar, Hankali a tashe ya shigo gidan saboda yanayin da yaji muryar yasan babu lafiya, kusa dashi yaje ya tsuguna "Gani Papy, Wani irin kallo yayi mishi wanda yake nuna tsantsar soyayya ga mai yinshi, hannunshi ya rike hade da hada jikinshi da nashi da karfi, "kai jinina ne Hafeez, ashe kai dana ne, ina ma nasan wannan tun ranar farko, da kome zakayi tare zamuyi shi, da ban barka kayi wahalar komai da kanka ba, cikin rashin fahimta Hafeez ya da dago ya kalli idon Papy da yayi jajur, zaiyi magana Papy yayi saurin kada kanshi yace "kai jinina ne Hafeez, kai dan yar uwata ne, dan wacce muka kwanta a mahaifa daya ne, Wani irin kukan farin ciki ne ya kufcewa Hafeez, duk yadda yakai da hangenshi bai hararo kusancin nasu har ya kai haka ba, shidai yasan kamannin Baffa sosai yake gani a jikin Papy sai fari da ya banbanta su, sake rungumeshi Papy yayi yace "yau ranar farin ciki ce ba ta kuka ba, Mummy da karyayyar zuciyarta ta tsumu sosai tace "kukan ya zama dole, kuka ne na farin ciki, Shi yanzu nasan kukan tunowa da Suwaiba yakeyi, share hawayen tausayi tayi tace "ina ma Lokacin da suwaiba ta debo mai tsawo ne ta ga wannan ranar, kallonta Papy yayi yaga ita din ma tana dan yanayi dashi yace "kema yar---- cike da murna Baffa ya katseshi da cewa yayarka ce, ita ce Babba, nuna Ma'u yayi yace "wannan ita ce ta haifeta, su biyu ne, Allah yayi wa Halima rasuwa da dadewa, sai ita kadai ta rage mana, ashe wani farin cikin na tafe zuwa garemu, ashe ina da rabon ganin Magaji na kafin kasa ta rufe min ido, Wannan kalma ta *MAGAJI* ita sanya Goggo jin wani dumi tun daga kanta har cikinta, Ido ta zurawa Baffa da yake ta sambatu a gaban Papy da Anni, duk yadda taso su hada ido dashi sam yaki dan gaba daya ya manta Allah yayi halittar ta a gurin, Yasan dai tana makale cikin ranshi amma ganin Papy ya sanyashi mance duk wata soyayya in ba tashi ba, ji yakeyi ina ma ace da kuruciyarshi da sai yayi zagaye da Papy a bayanshi ba tare da ya gaji ba.. Wani irin kugin taji a cikinta tunda Anni ta fara basu labarin shi dawo mata, ganin yadda tun yanzu Baffa ya ki koda kallonta ya tabbatar mata da lallai akwai aiki a gaban ta, Mikewa tayi da niyyar tafiya bayi dan cikin nata jinshi takeyi kamar zata kasayar da ya'yan hanjinta, Tana mikewa taji kafarta tayi mata nauyi saboda yadda zawon ya taho mata gadan gadan, dakyar ta daga kafarta, tana dagawa zanin jikinta ya sabule ta feso shi ba tare da sanin inda zashi ba, Wani irin ihu Radiya ta saki tana fadin "I'm dead" wayyo Allah na, "Dariyar Ruwaida ce ta cika gurin tana yi tana fadin *nyan nyan nya* disgusting! Papy kagani da kace "in an min abu in dinga hakuri Allah zai saka min, yau gashi naga ni da idona, wayyo cikina, she deserve more old lady karo mata,, Janyota Mami tayi da karfi ta sake maida idonta cikin mayafinta kamar yadda kowa yayi a gurin, kunnenta taja tace "ke wace irin yarinya ce, in sake jin kince pim kiga abun da zan miki, Mummy ce ta tashi da sauri tana tare Goggo tana fadin Goggo lafiya, Hawayen takaicin da Goggo ke rikewa ya zubo a kuncinta, cike tsoron ganin hawaye a idon wacce babu abin da ke sata kuka Mummy ta ja hannunta sukayi bayi, shi kuwa Baffa maida kallonshi gurin Radiya dake kuka tana kyankyame jikinta yayi yace "je ki wanke jikinki mana, ko so kikeyi warin ya kashe mu, baki ganin muna cikin farin ciki ne, karaff kalamanshi a kunnen Goggo, wani Kukan ta sake fashewa dashi a zuciyarta tana tambayar kanta ta inda aka samo matsalar, Damuwa ce karara a fuskar Mummy dan iya rayuwarta bata taba ganin hawaye a idon Goggo ba, bayan ta gama kimtsa ta suna jiyo muryar Baffa yana basu Labarin Suwaiba da 'yayanta, ita kanta Radiya cike take da mamakin yadda yake basu labarin suwaiba da 'yayanta dan a da ko labarinsu baya son ji bare ya ba wani, Kallon Goggo Mummy tayi tace "kiyi ma Baffa uzuri, shekaru sama da arbain rabonshi da dan da ya cire rai da kasancewarsa a duniya, sannan kuma shi kadai ya zame mishi namiji, kinga dole yayi farin ciki, ni kaina cikin farin ciki nake, dan a yanzu na fita a sahun ni kadai, mun zama biyu, ďan uwa dadi gareshi Gog---- dogon tsaki taja wanda ya katse mummy da karasa maganar ta, "Ba tun yau na lura da cewa ke din bakya kishi na da kanki ba, inama Allah Halima ya bar min ya daukeki Goggo ta fadi cikin gushewar hankali, Zaro ido Mummy tayi zatayi magana ta jiyo muryar Baffa yana kwala kiranta, bai

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156