Skip to content

Chapter 30

Chapter 30

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

bata lura da yanayin tafiyar Atika ba, daki ta shiga ta yayo yayi ta fito ta dauko dutsen kyasta wuta, kyasta shi tayi cikin yayi nan take haske ya bayyana, bata kara bi takan Atika ba ta wuce daki ta dauko ragowar Tuwon da sukaci da rana, saka iya wanda zai ishesu tayi a tukunyar kasa dan ta dumama, ta zubawa Atika mai sanyin a cikin roba ta tura mata, dakyar ta iya dukawa ta mika mata Boddo, sannan ta dauki tuwon, can baya taje ta zauna dakyar tanajin radadin a can kasanta, tsabar yunwar da takeji yasa bataji sanyin abincin ba ta dinga turashi tana zubar da hawaye, muryar Bingel taji akanta tana share mata hawaye tana bata hakuri, wani sabon kukan ne ya kufce mata hade da rungume Bingel wacce itama kukan takeyi.... 11:34pm●●●● Tsugune take tana wanke geron safe tana gyangyadawa hade da shashshekar kuka, sanyin dake shigarta ta sama da kasa shi ya haifar mata da rawar sanyi sosai, jingina tayi jikin kwaryar ta fara kiran sunan Allah a cikin ranta, nutsuwace ta fara ratsata kaďan kaďan har bacci ya soma ďaukarta, ko mintina biyar batayi ba taji muryar Baffa da ya lallabo ya fito yazo inda take, murya kasa kasa yace "Atika, Atika, tashi muje ki kwanta, Kuka sosai ta fashe mishi dashi cikin yarenta na larabci wanda bayaji tace "Dan Allah ka kaini gurin "ummi Aisha", sunan Aishan da yaji ta kira ne yasa shi cewa "Mai babban suna? Gyada kanta tayi jikinta na rawar sanyi, Yace "to me mai babban suna tayi? Ganin da tayi bai gane abun da tace bane yasa ta mike ta fara tafiya dakyar, wani tausayinta ne ya ratsashi ya tuna abin da ya mata dazu kuma bai samu damar tsayawa ya taimaka mata ba saboda kar ma'u ta dawo, takawa yayi da dan sauri ya isa gareta ya kamo hannunta ya zaunar da akan dakali, dan ihu ta saki ta mike tsaye saboda zafi, "yi hakuri ya fadi jiki a sanyaye tsoro duk ya cikashi, yaayi ya debo da yawa ya iza wuta ya daura ruwa, saida ya tabbatar ruwan yayi zafi sannan ya juye mata cikin kwarya yayi mata nuni da ruwan, da sauri ta matso kusa da ruwan bata damu da tsayuwar da yayi a gurin ba, ta cire kaya ta tsugunna ta fara tsarki tana kuka sosai saboda azaba, saida ta tabbatar daga zafi ta fara jin dadi sannan ta watsa sauran ruwan a jikinta, kayanta ta dauka tasa ta wuce dakin da take kwana ta runtse idonta ko baccin da ta fara zaizo ya dauketa, saidai fa bacci yace ki nemani inda kika ajiye ni, mikewa tayi tana adduo'i tana rokon Allah abin da yafi zama mata alkairi koda kuwa ace mutuwa ce, ta tabbatar da yanzu bata da ragowar gata daga Allah sai Hardejo, shi kuma Hardejo sam bashi da masaniyar halin da take ciki, da wannan tunanin ta fara gyangyadi har bacci mai cike da mafarkai yayi gaba da ita..... Watanni uku sun shude, watanni masu cike da tsananin wuya ga Atika, duk wani aikin gidan na karfi ita take yinsu, kama da wanki, surfe, da sauransu, a cikin watannin an samu sauyi na cigaba sosai a kauye, cigaba daga bangarori da dama, sannan ci baya ga Baffa, kullum kwanan duniya sai shanayen da aka bar musu da wadanda ya siyo da kudinshi sun kasa, saidai ya yanka ya kaisu kauyuka domin a saya, a haka ne ya zamto mahaucin karfi da yaji, bai kara marmarin bi takan Atika ba saboda kar tsautsayi yasa har ma'u ta gane, a cikin wannan halin Ma'u ta dage da sana'oi kala domin ta yi hidimar gidanta da ya'yanta, Atika itace karfin sana'oin domin ita ke yinsu amma ko dankwali Ma'u bata taba tunanin siyan mata ba... Yammacin ranar asabar Ma'u na tsugune tana gasa naman gafiya, nan take kamshi mai hade da kauri ya gaurayen gidan, sannu a hankalin kamshin ke ziyartar hancin Atika dake tsugune tana goga gero a jikin dutse, tun tana daure jin kamshin har ya gagareta tayi saurin mikewa baki cike da amai ta dinga kwaro shi, saida ta amayar da komai na cikinta, ta zaune a gurin tana maida numfashi bayan ta dauraye bakinta, Bingel wacce ta zamo kawar hirarta ita ta matso da sauri tana shafa mata kai, ita kuwa ma'u sam bata kawo komai a ranta ba sai ma cigaba da gashi da tayi, duk tunaninta shawara ce ke damunta, tana gama gashin ta kalli Atika shekeke tayi mata nuni da geron, a hankali ta mike ta koma bakin aikinta, tana kallon ma'u ta kasafta naman ita da ya'yanta, dama naman bai bata sha'awa ba samm, aikinta ta cigaba dayi, in kaga yadda take aikin sai ka dauka baiwa ce..., Jin nama tayi a saitin bakinta, da sauri ta dago taga Bingel a tsaye tana mata murmushi, a kasonta ta cire mata da yawa dan taga ba'a bata ba, wani aman taji ya kara tahowa gadan gadan, wannan karan a gurin ta sakeshi, wata irin Ashar Ma'u ta saki tace "A kan gari na kikayi min amai, bata karasa maganar ba taji ta kara kwararo Aman har akan dutsen, "A'a wannan ba lafiya ba, Ma'u ta fadi tana matsowa kusa da ita, hannunta ta finciko ta duba, jiki na kyarma ta daga mata riga, ganin da tayi nonuwanta sun ciko kansu yayi bakikkirin ya sata sakin wata yar kara hade kiran sunan Allah, ciki gareki? Ciki gareki Atika? Babu mayafi haka ta fita ta nufi gidan Haire dan taga Atikar zata bata mata lokaci, a tsakar gida ta samu Haire da maryam yar Hardejo tana koya musu karatu, "Haireeeeee ta fadi da karfin gaske, a kidime Haire tace "lafiya Ma'u? Kuka ne ya kufce mata tace "Haire Atika ciki gareta, mikewa Haire tayi tace "ci me? Ciki Ma'u ta fadi cikin rawar murya, Gaba daya idonsu ya rufe sun manta akwai Maryam da yar Hairen kawar maryam a gurin, "anya ma'u ciki ne, ba kince Baffa bai taba kusantarta ba, to waye ya mata cikin? Ma'u tace "nima tunanin da nakeyi kenan, mayafi Haire ta dauko tace "muje gidan, Suna fita maryam tace ma Laraba "bari inje gida bayan la'asar zan dawo, Laraba tace "to sai kin dawo, kinga zanyi aiki da na raka ki, "babu komai maryam tace sannan ta kwashe yan littafanta tayi gida... Da gaske kike Maryama? Wallahi ummi (sunan da Atika ta radawa mai babban suna kenan) dagaske nake, Aisha batayi kasa a gwiwa ba tasa yaro yayi mata magana da Hardejo, kwashe komai tayi ta fada mishi sannan tace "Dama Laminjo tasha fada min halin da Atika take ciki a gidan, bana kamawa ne saboda kowa yasan Laminjo yawancin maganganunta karya ne, rai a bace Hardejo yace "ki shirya zansa Bala ya rakaki sai kuje ku taho min da ita, tunda Muhammadu ya fara tafiye tafiyen nan nasan lallai rayuwar Atika na cikin garari.. cikin gida Aisha ta shiga ta shirya tsaff da mawafi, Bala shaho wanda a yanzu ya zamto shakikin gidan Malam Harďejo shi yayi mata rakiya har gidan.. A tsakiya suka sata suna ta jero mata tambayoyi irin na kurame, da haushi ya ishi ma'u ta tashi ta dauko sandar

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156