Skip to content

Chapter 66

Chapter 66

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

dawo gidan ba sai 1 na dare suka dawo tare dasu Papy, anan ma hirar suka zauna yi har 1:30, ya nunawa Papy gurin da yake sa ran zai mishi gini in yazo ya dinga sauka, Tana jiyo su dan ta kasa rintsawa, tana jin Papy na cewa nan da shekara daya shima zai baro Gomben ya dawo nan kaduna cikin yan uwanshi, ganin irin farin cikin da Baffa yakeyi shi ya sake tunzura zuciyar Goggo ta dau alwashin aiwatar da abin da tayi niyya shekarun baya.... "Gaskiya bazan sha wannan kunun ba Goggo, walhi bazan karya da wadannan kazantar ba, haba common tea ma sai kice bazaki bani in sha ba, Badar ce ke maganar kamar zatayi kuka saboda takaicin karo da kunun da tayi, tabe baki Goggo tayi tace "Sai dai kar kisha, tun da na tashi nake jiran Rilwanu bai zo ba, ni kikeso in fita in siyo miki kayan shayin, Da tsufana me zanyi da shayi ni, in kinga dama kar k---- Assalamu Alaikum, sallamar da akayi ta katse Goggo daga karasa maganarta, kaya niki niki taga Jamal da Hafeez suna shigowa dashi, a bayansu kuma ta hango Anni da Mami, papy ne ya shigo a karshe sai Rilwanu da Garzali suma dauke da wasu kayan, fitowa Baffa yayi da sauri saboda jin muryar Papy, kallonshi Anni tayi cikin zolaya tace "Alhaji karka fadi, irin wannan sauri haka, shima saurin yazo ya ganka ne ya hanashi ya barmu sai anjima muzo, Dariya Baffa yayi yace "marabanku, ai sai ki bani kunya, yanzu dai bari in boye murnata, Dariya dukkansu sukayi Papy ya tsuguna ya gaida Baffa, bai amsa ba ya dauko tabarma ya shimfida musu, saida ya zauna sannan suka gaisa dukkansu cikin farin ciki, Hira sosai Baffa sukeyi da Anni tana bashi labarin yarintar Papy har zuwa girmanshi, da irin nasarorin da ya samu, gaba daya Baffa ya manta da Goggo dake tsaye kasake tana kallonsu, ko tafiyar Badariyya makaranta bata sani ba, Kallon Anni yayi yace "tun jiya nake ta tunanin abun da zan miki in saka miki abin da kikayi min, Na tattaro duk abinda na mallaka naga sun yi min kadan in baki a matsayin tukwicin abin alherin da kikayi mini na taimakon dana da kikayi har ya zama abun da ya zama, na kwana ina miki addu'ar Allah ya sanyaki cikin farin ciki duniya da lahira, Allah shi kadai zai biyaki da aljanna firdausi, nagode nagode sosai Hanne, Kafin Anni ta amsa Ruwaida tayi saurin cewa "Ameen mijin Anni, baban Papy, kaka na ni kadai banda yaya Jamal, garammmm Goggo taji maganar kamar saukar aradu, tsayuwace ta gagareta ta dawo cikinsu ta zauna saboda shurun da taji sunyi, kallon kallo suka shiga yi a gurin Mami tayi saurin cewa Jamal ya kai Ruwaidah gurin su Nadeeyah, "suna makaranta Hafeez ya fadi yana rike hannun sarkin katobara, yace muje ki rakani.. Suna fita Anni tace "yarinta hoo, ita a dole farin ciki takeyi taga babanta cikin yanayin da yafi na da, "Yarintarta Ruwaidah akwai hikima a cikinta Anni, Papy ya fadi yana gyara zama.. Kallon Baffa yayi yace "Baffa kana son sakawa Anni, baka da abun saka mata dashi, dan Allah ne kadai mai saka mata, "abu daya zakayi ka kwatanta kyautata mata shine ka aureta, Ta zamto matarka, makwafin mahaifiyata, wannan shine kadai zai sani farin ciki, Anni ta ki yin aure saboda ni, bata jure ganin kowa ya wulakanta ni, shiyasa ta hakura da aure domin taga auren wani mabudi ne na wulakanci a gareni, Dan Allah Baffa ka auri ANNI, kallon Goggo da ta kureshi da ido yayi yace "INNA dan Allah kisa baki, auren shi kadai ne abun da zamuyi mu saka mata...... Kafin Goggo ta gama tattaro amsar bayarwa Baffa yayi murmushi yace "yo har sai ka roka, ni da nake neman abun da zan bada tukwici, ai na karbi wannan karramawar, kuma in shaa Allahu zata ga karamci domin wannan din ma wani sabon karamcin ne da yake bukatar tukwici, Dariya Mami tayi ta kalli Anni dake share kwallar da ta gangaro mata, hannunta ta kama tace "Alhamdulillah Anni, dan Allah ki amince, kuka ne ya kufce mata tace "na Amince Maimuna, wannan ya wuce tukwici, domin kuwa zan shiga cikin jerin matan da nake fatan in mutu cikin sutura, zan shiga jerin matan da zasu mutu ana maraba dasu, hannu ta daga sama tace "Alhamdullillah ala kulli halin, Karkiyi saurin Hamdallah Goggo da ta gama charge ta fadi tana mikewa da kyar, kiyi gaggawar maida murnarki domin a haka zaki mutu babu aure1, Mijina bai min kishiya tun da jajayen sawunmu ba, sai yanzu da muke rai a bakin rami, in banda kwadayi ma me zakiyi da wannan tsohon, me ya rage mishi da zaki suďa, "Murmushin ilimi Anni tayi dan a ganinta kishi ne, tace "ko ban samu abin sudewa ba zan samu martabar zama matar aure, kwantar da Hankalinki bazan zo dan yin kishi dake ba, zanyi aure dan in samu cikar kamalar da na dade ina nema, "Aiko zaki mutu baki samu wannan kamalar ba in dai mijina zaki aura, bakin da ya furta miki cewa zai aureki shi zai dawo yace miki ya fasa, Shekeke Baffa ya kalli Goggo, dauke kanshi yayi da sauri da yaga suna kokarin hada ido dan idanuwanta kan sanyashi manta komai, yace "Aure babu fashi, sati ma in shaa Allahu, Kallon Papy yayi yace "ka daukesu ka maidasu gida sai ka dawo mu nemo magina su fara aikin ginin nan.. Sallama Papy yayiwa Ma'u dake tsaye galala masifarta ta makale saboda furucin Baffa, Bin su tayi da ido har suka bacewa ganinta sannan ta fada dakin da sauri, kofar bayin ta shiga bugawa tana masifa tana fadin "baka isa ba, walhy Muhammadu baka isa ba, alkawarin da kayi min kenan, ni zaka butulcewa duk irin halaccin da nayi maka, to wallhi ka fito nan ina jiranka, saidai ka zaba koni ko ita, dan wallhi bazan zauna da kishiya ba.. Yana gama wanka ya bude kofar ya fito ba tare da ya kalleta ba, kaya ya dauko yasa yace "Ma'u halacci babu wanda ban miki ba, shekararmu sama da hamsin dake ban taba yunkurin yi miki kishiya ba da kaina ba, sai yanzu da nake son saka alkhairi da alkhairi, yanzu ke ba abun kunya bane ki ts---- ka kalli idona ka fadamin haka Muhammadu, ta katseshi da karfi tana juyo kafadunshi, juyar da kanshi yayi ya dauki turare ya fesa yace "kallon idonki na daina shi har in koma ga mahallincina, kallon cikin idanuwanki sun sanyani fita cikin hayyacina har na aikata ma diyar cikina abubuwan da har na mutu bazan yafewa kaina ba, ki rike idanuwanki in rike rayuwata da mu'amalata, yana kaiwa nan yasa kai ya fita ya bar Goggo da masifa kamar zata ari baki, kayan dake tsakar gidan yasa Rilwanu kwashewa yasa mishi a dakin waje.. crates din kwan Goggo ta farfasa su da tabarya, ta dinga bin kayan tana tsine musu, Dakyar Rilwanu ya kwashesu, yana gamawa yayi mata sallama yace "gobe zai koma garin su, mahaifinshi baida lafiya, bata bashi ansa ba ya cigaba da cewa "ina tunanin dawo dashi garin nan Goggo zan kaishi asibitin dutse a duba shi,

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156