Skip to content

Chapter 150

Chapter 150

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

nima dai ban sani ba, Rilwanu yace inzo gida ba lafiya, a hanzarce suka fita dan zuwa gidan suga abinda ke faruwa.. Mummy dake can sama gurin Musaddiq itama tayi saurin mikewa ta biyo bayan Radiya da ta kawo mata rahoto... Da sauri Malam Mato mahaifin Rilwanu ya debo ruwa ya mikawa matarshi dake tsaye kan Goggo tana taimaka mata, wani irin ihu takeyi tana fisgar gashin jikinta haďe da firzar da ruwan da ake zuba mata a baki, "Gishiri, Gishiri, hakan ta dinga faďi tana zaro harcenta da yayi fari tass kamar mayya, Gishirin rilwanu ya debo a cikin buhu ya kawo musu dan a tunaninsu ciwukan jikinta zata sawa, yana kawo mata ta yafa kusan rabin kofin a bakinta, A firgice suka fara kokarin kwace kofin suka kasa saboda a wannan lokacin karfin ba ďaya bane, ko jariri ne wanda bashi da zunubin komai sai ya fuskanci barazanar wannan rana bare mutum irin Goggo wacce ta naďi kayayyakin bil adama marasa adadi... Sarketa gishirin yayi ta shiga tari kirjinta na ďagawa sama kamar zai rabu da jikinta, yaye zanin jikinta tayi saboda tsabar azaba ta mike ta fara zubar da kayan dakinta tana ihu sosai.. Halacci da iyayen Rilwanu suke ganin an yiwa dansu shi ya hanasu barin dakin duk ko da irin warin dake fita a jikin Goggo... Wasu gungun hotuna ta zubo har gaban malam mato, saura kiris glass din da ya fashe ya taba kafarshi, da sauri ya matsa baya ya tsuguna ya fara tattara hotunan ya umurci Rilwanu da matarshi da su riketa, yana gama tattara hotunan ya ajiyesu a kan table zai komo gurinta.. Tsayawa yayi cakk ya waigo da sauri ya sake duban hoton saman wanda bashi da kala samm, dauko hoton yayi jiki na rawa yace "Ma'un Ukari, *Nankwat Manasir* shigowar su Baffa ne yasashi mayar da hoton da bazai taba manta ranar da akayi shi ba, "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun.. shi kawai yake maimaitawa cikin ranshi tare da tunanin inda mutanen nan masu matukar karamci suka san mace marar imani irin Ma'u... Mummy ce ta karaso ciki ta dauko zani dan rufe mata tsiraicin jikinta tana kuka sosai, Baffa kuwa hannunta ya rike yana faďin "Ma'u zauna kiyi ta salati, a yanzu ihu ba naki bane, da karfinta ta fisge tayi hanyar waje tana ihun da ko gida uku ne tsakaninku zakaji ta, da azama suka bita suka rikota suka maidata daki suka garkameshi dan yadda take jiyar da mutane ciwo.... Malam Mato kasa rike abun yayi a ranshi yace "Marar lafiyar nan itace Ma'u wacce naga hotonta da kananan yara biyu? Da sauri Baffa yace "Eh itace, ka santa ne? Juyayi Malam Mato ya shiga yana tunanin ta yanda zai fara sanar dasu abubuwan da ya sani shekaru da dama wanda babu wanda yasan dasu sai ubangijin talikai sai shi da ita kanta Ma'un, Nufar inda yake Baffa yayi zaiyi magana sukaji ihun Goggo tana faďin "Na shiga uku, ku kira min Bokan Ukari yazo ya tamaikeni, yagar naman jikina akeyi, wayyo, wayyo, ku kirashi yazo ya taimakeni, yayi min alkawarin bazan mutu ba, yayi min alkawarin karashe rayuwata har kowa ya mutu ya barni.. "Mai kashewa shi ke tsoron mutuwa, shin akwai adalci a cikin wannan? Malam ya Mato yayi tambayar ba tare da jiran amsar kowa ba, da sauri ya nufi dakin ya buďeshi domin a yanzu samm ya daina tausaya mata... "Ai bai kamata wanda yake da karfin zuciyar sanadiyyar rayukan mu'imunai da dama tsoron mutuwa ba, *JUMMA'ATU BABBAN RANA* Ranar yin katako daga kauyen ukari zuwa Gembu, *Ma'u yar gidan Manasir*... Tunaninki zai iya tafiya shekaru hamsin da doriya suka wuce, in kin manta ni bazan manta ba, zan fara tuna miki in yaso sai ki karasa da bakinki.. Tunda ya fara maganar azababben jikin Goggo ya saki, maganarshi tafi ciwon azaba... "Harďejo, Musulman kauyen Gembu, suna Sallar Jumma'a... ko zaki iya tuna abun da faru a ranar, cikin dabara yace "Faďin ainihin abin da ya faru shine kadai zai taimaki rayuwarki ki dawo kamar yadda kike da, sannan babu zancen mutuwa har sai dan kanki kinji duniyar ta isheki... Saboda jahilci da kuma tsabar son duniya, Goggo ta fara faďin dukkan labaran da suka faru a baya, har kawo mutuwar Atika da yunkurin kashe Papy da kuma irin ukubar da ta bawa Mamma Suwaiba, har yadda tayi ta raba Daddy da Mamma suwaiba ta hanyar asiri, wannan confession din tayi shi ne cike da sa ran ciwon zai barta sannan bazata mutu ba, ta sa rai bayan ta rayu zata yi asirin da zai mantar dasu komai... *Goggo dai tazo duniya zama ne, tazo ne kawai ta karaci rayuwarta cikin asarar da lokacinta gurin yiwa wasu sihiri domin kawai gamsar da zuciyarta*.... Ajiyar Zuciya Malam Mato yayi ya kalli duk mutanen gurin da suka mutu a tsaye saboda jin rashin imanin Goggo, "Alhamdulillah da Allah ya taimakeni ta faďi da bakinta domin inata tunanin yadda zan gamsar daku, a lokacin da Ma'u ta sanar da yan ta'addan nan cewa akwai Musulmai a kauyen Gembu, bani da bakin magana domin na riga na ce musu ni ba musulmi bane, bayan mun shiga garin na saukesu sai na nufi can wani guri na samu maboya, ganin irin kisan gillar da sukayi ma musulman kauyen yasani barin garin Taraba gaba dayanta saboda tsabar tsoron wata rana wannan abun zai faru dani ko wani nawa, a kullum kwanan duniya cikin shekarun nan sai na tuno da wannan al'amarin, rashin sanin inda zanga mai aika aikar yasani barin wa cikina komai, da nasan a gidan nan take wallahi da kaina zan mikata ga hukuma su hukunta ta tun da sauran karfinta, amma yanzu ko an mikata ga hukuma babu amfani domin hukuncin ubangiji ya fara tun anan duniya kafin ta riskeshi a lahira.... Wani irin kuka Baffa ya durkushe a gurin ya fara yi cikin kunan rai, shekara da shekaru yana tare da wacce ta rabashi da ahalinshi, a harzuke bayan kukan ya lafa ya mike ya nufi inda take zaune tana yakushin jikinta ya kaiwa wuyanta shaka.. A gaggauce su Papy suka share hawayensu suka nufi gurin Baffa, dakyar suka iya rabashi da Goggo wacce take ihun ceton rai.. "Karka zama irinta Baffa, sai ka kwashe dukkan zunubbanta, ka barta da abunta ta girbe abun da ta shuka da hannunta.. Daddy ne ke magana cike da takaicin haďa iri da wannan zuri'a karo na ba adadi, dole ya dinga fuskantar kalubale kala kala a cikin tashi zuri'ar... Mummy samm ta kasa motsawa daga inda take, juya maganganun ta dingayi a cikin kwakwalawarta, rashin imanin mahaifiyarta har ya kai haka, tabbas dole ta dinga ganin jarabawa kala kala, Allah bai bata uwa ba, wannan wacce irin uwa ce wacce sam babu kwayar halittar imani a cikin zuciyarta... Zaburar da Goggo ta sakeyi ita ta dawo dasu daga duniyar sake saken da suka tafi, babu wanda yayi yunkurin bin ta sai Papy da Anni, kafin su kai inda take har ta kusa kofar gida.... Da gudu wani mai baro wanda ya lodo karafe da langar kwanon aluminum tsofaffi ya taho dan wucewa yana jin wakarshi, tsayawa yayi a gefen gidan su Baffa dan siyan rake ya parka baron a

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156