Skip to content

Chapter 54

Chapter 54

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

Allah yayi ma fuskokinsu gamo, ko wanne saida ya tsorata da ganin fuskarkokinsu cikin na juna..... Mrs Tijjani Shattimah...... [18/03 8:06 AM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣8⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Dammmm..... gaban Baffa yayi mummunar faduwa, karasa mikewa zaune yayi har lokacin bai dauke idanuwanshi kan Papy ba, shi din ma Papy hakan take gareshi, saboda tsananin faduwar gaba bakinshi ya gaza furta koda kalma daya ne, Hafeez dake bayansu ya tsuguna zuciyarshi wasai saboda a yau yana tunanin warwarewar SARK'AK'IYAR da ya shiga watanni bakwai da suka wuce, kallon Baffa yayi hade da dan taba kafadunshi yace "Baffa wannan shine Papy wanda nake zaune a gidanshi a Gombe, a razane Baffa ya dawo hayyacinshi yace "au to madallah, an gode fa, Papy bai amsa shi ba ya zauna sosai zuciyarshi sai kai kawo take, ko tantama bayayi wannan mahaifinshi ne da Anni ta dade tana fada mishi, kamannin sun wuce kamanni kawai, tabbas akwai jini mai karfi a tsakaninsu, gaishe da Baffa yayi hade da tambayar jikinshi, Goggo ce ta iya amsawa babu inda a cikin jikinta bai saki ba, saida sukayi kusan minti biyar a zaune babu wanda ya sake magana, kowa da abun da yake tunani a ranshi, karfin Hali Baffa yayi dan ya gama hange hangenshi a yan uwa yasan babu wanda ya rage mishi na kusa, sannan yasan dai bashi da wani ďa banda wanda ya binne da hannunshi, kuma yasan bai taba yin aure a wani guri ba bare har yayi tunanin ya barta da cikinshi, wannan abun al'ajabin kamanni sun yi yawa, bazai iya jure barin shi a ranshi ba, dole yana bukatar sanin daga inda halittar nan mai tsananin kama dashi ya fito, kallon Papy Yayi yace "dan nan idan bazaka damu ba ina so inyi maka tambaya, takalma da safa Baffa ya cire ya gyara zamanshi sosai a kan tabarmar, ganin yatsun kafarshi ya kara daga hankalin Ma'u, shin meke shirin faruwa ne?, magana Baffa zai fara-- tayi saurin katseshi tace "daga mutum yazo gaisheka sai ka tsareshi da magana, ka sani ko sauri yakeyi, Murmushi Papy yayi yace "babu komai karki damu, ko bai tsayar dani ba nima babu inda zani domin akwai wani al'amarin da yake shirin faruwa, wannan al'amarin zai fitar da rayuka da dama cikin tunanin da suka shekara da shekaru suna yinshi, bude baki tayi da niyyar sake yin magana Baffa ya rigata da cewa "nasan kaima kana cikin zullumin da nake ciki, duk wanda ya ganmu ni da kai yasan jini daya ne saboda kamanni, wasu ka iya cewa yan biyu ne saidai yanayin tsufan da jikin shine kadai ya banbanta, dan Allah ina son ka fada min wanene mahaifinka dan inason sanin ko inada wani sauran dan uwa wanda kaddara ta boye min shi, ina son sanin inda mahaifinka yake dan inje mu gana, in baya raye to dan Allah ka bani tarihin shi wanda zai iya warware min komai, Papy baiyi magana ba ya fito da wayarshi, dannata yayi hade da karata a kunnenshi, "Hello Maimunah, hadani da Anni a waya, Papy na...., Ruwaidah ta fadi murya a shake, "Mama na, kuka kike yi? Kukan ta sake fashewa dashi kamar zata tsaga wayar, rage murya yayi yace "wanene, daina kukan and tell me, M-a-mi ce ta fadi tana ajiyar zuciya, tsaki yayi a hankali, yasan abin da aka mata bai taka kara ya karya ba, "yi hakuri Mamanah, jeki kai mata inji dalilin saki kuka, da dan gudunta ta tashi taje kitchen inda Mami da mai aikinsu ke kwashe mangyadan da ta zubar, a darare tace "Maami Papy ya kiraki, kwafa tayi ta goge hannunta a jikin tsumma ta karbi wayar, yana jin sallamarta yayi saurin amsawa, ba tare da jin dalilin kukan Ruwaidah ba yace "ina Anni? tana bacci lafiya dai ko, mami ta tambaya cike da zullumi, ajiyar zuciya yayi yace "lafiya kalau Maimuna, gobe da safe ku shirya guraren tara zan kira Badamasi yazo ya taho daku kaduna, zama Mami tayi gabanta na tsananta faduwa tace "Dan Allah ka fada min abin da yake faruwa, ina JAMAL da HAFEEZ?, murmushi yayi cike da tsokana yace khairan in shaa Allah ruďaďďiya, ke dai ku shirya kinji, gyada kai tayi har lokacin gabanta bai daina faduwa ba... Kallon Baffa yayi bayan ya ajiye wayar yace "Sanin abubuwan da ka tambayeni wannan sai maihaifiyata tazo, domin nima ban san kaina ba, tashi nayi na ganni a hannun mahaifiyata ba tare da uba da yan uwa ba, ni kadai na rayu a gabanta, tare muka sha wahalhalun rayuwa, na dai san a kullum tana fada min ina da uba, amma bata san inda yake ba, A lokacin da Ma'u na tsaye to tabbas da ta kai kasa, kokarin mikewa takeyi Papy yace "inna dawo ki zauna ayi komai a gabanki, yau da za'a bincika zuciyata a gani to tabbas da an gano tafi takarda haske, kallon shi Ma'u tayi tace "ďan nan ina ganin dai kamanni ne, dan mu nan bamu da da namiji ko daya, sannan duk wasu y'an uwa namu na kusa duk sun mutu, kasan Allah yana iya halittar mutane masu kama da juna, akwai su da dama sab--- katseta Hafeez yayi cikin girmamawa yace "Goggo wannan ya wuce kamanni kawai, akwai jini mai karfi, ki duba girman makarantarmu duk daliban dake ciki ace dani kadai ya shaku har ya kaini gidanshi cikin iyalinshi, sannan kuma idan kika ga Jamal da Ruwaidah a nan ne zaki tabbatar da su ďin jinin mu ne, Daka mishi tsawa Goggo tayi "kai dalla rufe mana baki, manya na magana kana yi saboda tsabar rashin kunya, tashi ka fita kaba mutane guri, mikewa Hafeez yayi yana fadin kiyi hakuri, harara ta bishi dashi har ya bacewa ganinta sannan ta dawo da kallonta kan Papy tace "to bawan Allah mun gode da ziyara, sai anjima, sake gyara zama Papy yayi yace "Inna, bazan boye miki ba, barin gidannan a guri na sai da daddare, sannan gobe da wuri zanzo domin kuwa ina hango cikar burina na sama da shekaru arbain da doriya zai tabbata, cike da faduwar gaba ta kalli Baffa da ya kasa dauke idonshi a kan Papy, yanayin maganarshi, da komai irin nashi ne, gayu, gogewa da yarinta ne kadai ya banbanta su, taba shi Goggo tayi tace "lokacin Sallah ya kusa tashi ka shiga kayi alwala, da sauri Papy ya kalli agogon hannunshi yace "uku da kwata ne yanzu Inna lokaci baiyi ba, tun Goggo na daurewa kar ta fara nuna mishi halinta, har saida ya kaita bango ta dakawa Baffa tsawa tace "ya tashi su wuce daki, wannan mutumin in ba aljani bane to maye ne, jiki a sanyaye Baffa ya tashi yace ma Papy "yaya Sunanka, da sauri papy yace "Abdallah" nan Baffa yayi ajiyar zuciya yace "ba SAIFU bane, Ma'u ba saifu bane, duk tunanina shine shiyasa na cika da tsoron ya za'ayi wanda ya mutu ya dawo, nasan ni na binneshi da hannuna, kallon Papy Goggo tayi tace "kaji ko, dan Allah tashi ka fitar mana a gida, kuma karka sake zuwa kaje can ka nemi ubanka.. Nan tsakar gida suka barshi zaune yana ta nazarin abubuwa, kodai da gaske bashi bane mahaifinshi, sai

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156