Chapter 85
Chapter 85
ruwa ta mayar ta rufe, tun da ta kwanta ciwo kusan watanni takwas bata kara bi takanta ba domin itama ba lafiyar gareta ba, girgiza kurciyar tayi tana kuka tana fadin *YARIMA ADAMU* wayyo Allah Kunzo a kurarren lokaci, nasan duk inda Yareema yake a yanzu to kasa ta rufe idonshi, wannan kurciyar rayuwar Yareema ce, Allah na tuba, wayyo ni Allah, haka ta dinga fadi hankali tashe, Da karfi ta saki mutum mutumin hanunta ya tarwatse a tsakar gidan, nan tabi kowane kai ta cire dabaibaiyin da aka mishi, runtse ido Sarki Tidjani yayi saboda juyawa da yaji kanshi nayi, dakyar Shareefah ta tallabe shi ya zauna a kasa ba tare da duban dattin gurin ba, itama hakan ce ta kasance da ita, saidai ita ta kasa fahimtar komai, sabanin Sarki Tidjani da komai ya shiga yawo a kanshi, yadda abubuwa suka faru ya dinga tunowa kamar yanzu ake yinsu, kusa dasu Hajja taje dan itama wani karfi taji a jikinta, burinta ta sanar dasu komai da suka sani da wanda basu da masaniya... "Nasan yanzu wasu abubuwan sun fara dawowa a kanku da kuma daukacin mutanen da suka san Yareema a Agadez, to saidai abin da baku sani ba shine dalilin da yasa ya kaurace muku ya tafi can wani guri inda babu wanda zai ganshi bare har yasa shi waiwayen gida, "Adamu Yallo... sarki ya dinga maimaitawa a bakinshi, fuskarshi yake kallo kamar yanzu suka rabu cikin lambun *Shehrah Agadez*, ina dan uwanshi ya tafi har tsawon wannan lokacin, yana kallon fitarshi daga lambun lokacin bakinshi yayi mishi nauyi ya kasa kiranshi bare har ya tambayeshi inda zashi, sai yau yaji tunanin ya dawo sabo dal game dashi, Da sauri ya maida idonshi kan Hajja yace "ina Adamu? Me ya sami Adamu? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, me ya shiga kaina har na manta da dan uwa kuma aminina, Ya salam ya fadi hade da dafe kai.. "Ba laifinka bane Yallabai, Laifin namu ne, bakai ba ma kowa a garin Agadez a yau sai ya tambayin dalilin da yasa ya manta da Yareeman da suke matukar so fiye da sarkin Kanshi... har ke ma Shareefah, a karancin shekarunki zaki iya tunawa da *Yeeman ki* , *Yeeman Pappalinto* nan take mafarkinta ya dawo mata sabo, sunan Yeema take yawan fadi cikin mafarkinta, wani irin kuka ne ya kufce ma Shareefah ta dinga nanata sunan a ranta, tabbas ta tuno kuruciyarsu saboda mafarkinta bai rage mata komai ba, cikin kuka tace "Bani labarin Yeema nah! Bani labarin dalilin da yasa yayi nesa dani..... *TUNA BAYA.......* ********** Ranki ya dade kici abinci dan Allah, rashin cin abinci zai iya zame miki illa, kuma kin sani sarki bazai fasa abun da yayi niyya ba, cikin Kuka Fulani Ayyu tace "Hajjara yanzu anyi min adalci, ace sarki ya rasa da wacce zai hadani sai da *Kuyanga Rosalin* , kuyangar da na bawa yarda tasan sirrina fiye da kowa, tayaya zan iya kallon mutanen gari, wannan ai cin mutunci ne a gareni da masarauta baki daya, Gabanta Jakadiyya Hajjara ta dawo tace "ki kwantar da hankalinki, ki barshi yayi auren, zamu san yadda zamuyi da ita, da kalamai masu dadi Hajjara ta kwantar mata hankali har taci abinci.... Wata hudu bayan auren *sarki Abdallah Yallo* da Kuyangarshi mai kula da komai na alamuranshi *Rosalin Mujdaha* mahaifinta shine mai bawa sarki kariya, bayan rasuwar mahaifiyarta mahaifinta ya bawa sarki ita domin ta zama mai aikinsu ta jikinsu wacce zata kula dasu, garin binciken shi na rashin haihuwa Rosalin ta fado ciki har malaminshi ya fada mishi alherin da ke tattare da aurenta, bai damu da kalubalen da ya fuskanta daga yan uwa da matarshi ba aka sanya rana, har Allah yasa ta zamo matarshi, kyakykyawar gaske ce doguwa sambal, ga biyayya da hakuri, hakan yasa yake matukar kaunarta, babu irin asirin da Fulani Ayyu batayi ba dan taga bayanta amma Allah cikin ikonsa duk ta tsallake, saboda tsoron Fulani da Rosalin keyi hakan yasa bata fita ko nan da can, duk abin da zai hadasu tana neman hanyar kaucewa saboda bata san tashin hankali, mugun hakuri gareta ga kawaici da sanin ya kamata, Babu wanda keda masaniyar tana dauke da ciki domin tsakaninta da bayinta yar kallon fuska ce, ko mikewa a gabansu batayi, A ranar da cikinta ya cika wata tara ranar akayi haihuwa a gidan, wazirin sarki wanda ya zamo kani ga sarki, a gurin barka ne kowa ya fahimci ciki gareta, ranar Fulani mutuwa ne kadai batayi ba, gaba daya kansu ya kulle ita da Hajjara suka rasa ta inda zata bullowa al'amarin.. Ranar suna Yaro yaci sunan *TIDJANI*, A daren ranar sunan Rosalin ta tashi da nakuda, sarki da kanshi ya sa aka kira unguwar zoman gidan ta karbi haihuwar, yana daga bakin kofa yaji kukan jinjiri, wani irin kuka ya fashe dashi na murna wanda yaki dauke mishi har saida yaji dumin danshi a jikinshi, nan gaba daya gari ya dauka Sarki Abdallah Yallo ya samu magaji....., kwana goma akayi ana buduri a garin, gidan kuwa zama yayi kamar gidan gala, domin cike yake tun safe har washe gari, babu abin da akeyi sai ciye ciye da raye raye, ko ina ka zaga cikin garin farin ciki ke dauke a fuskar kowa saboda sarki ya zamo mai kyautatawa a garesu.... Shekarar Yareemah Adamu bakwai rikonshi ya koma gurin Fulani Ayyu da tayi sanadiyyar mutuwar Rosalin da karamin ciki bayan barin da ta dinga yi, sarki yayi kuka yayi bakin cikin mutuwar Rosalin mace mai matukar nuna kula a gareshi.... Duk yadda Ayyu takai ga son kuntatawa Yareemah Adamu hakan yaki yiwuwa saboda sarki yana sanya ido sosai akanshi, sai kuma matar waziri mahaifiyar Tidjani wacce yake yini a gurinta bacci kadai ke maidashi gida gurin mahaifinshi, Albarkacin Adamu Allah ya azurta Fulani da samun ciki a lokacin da ta fidda rai, saidai kashh tayi matukar bakin cikin ganin ya mace ta haifa, haka nan tayi ta dakon kiyayyar Adamu a ranta, shi kuma Allah ya daura mishi kaunar yarta Shareefah haka itama Shareefan, ko ina zasu tare suke zuwa... Yana shekara goma sha shida sarki ya fara barin mishi kujera yana ganin yadda yake gudanar da al'amuran sarauta, Adalin sarki Abdallah, ashe a lokacinshi bai kwatanta adalci kamar yadda Adamu ke kwatantawa yanzu ba, Izza ta mulki da kasaita gaba daya sun tabbata a jikin Adamu, wani irin farin jini Allah yayi mishi wanda ya sanya ko ina a garin ake maganarshi da yabonshi, A rana in baiyi abun alkhairi sau goma ba to zaiyi fin goman, gaba daya kowa a garin ya tabbata cikin walwala saboda zuwan Yareemah Adamu.... *Mummunan Kaddara* Ranar da ya cika shekara Ashirin ciff, ranar kaddara mummuna ta afka mishi, a ranar al'amura marasa dadi suka faru a cikin garin agadez.... *Yadda Abun ya faru* Cikin farin ciki Sarki ke sanarwa da fulani Ayyu ya game shirin komai na hutawa ya barwa Yareemah kujerarshi, sannan ya fada mata an kawo mishi yaran sarakunan da zai aura mishi saboda cikar kamalar sarki, nan ta nuna mishi farin cikinta sosai harda cewa zata tayashi zabe a cikin matan.. Tana barin gurinshi zuciyarta kamar zata buga ta kira Hajjara, nan suka kulla duk shirinsu na kawar da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156