Skip to content

Chapter 84

Chapter 84

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

kamar zata buga ta kira Hajjara, nan suka kulla duk shirinsu na kawar da Abdallah domin a cewarta in ta kuskura ta yarda aka nadashi sarki kuma yayi aure wasu familyn zasu zama iyalan sarki su kuma su zama yan kallo.. Makudan Silalla ta bawa Hajjara ta shirya tafiya can kauyensu Sassoun burum, cikin sa'a, da kuma lokacin akwai wani boyayyen al'amari wanda Allah ya boye a rayuwar Adamu Hajja ta samu bokan da yayi nasarar yin aikin, ya kuma bukaci auren Hajja, a take ta yarje mishi domin dama tana bukatar yin auren, bayan sun kammala aikin ta koma agadez ta karbo sha tara ta arziki daga gurin fulani Ayyu.... Cikin Kuka Hajja tace "kudi ne wadanda basu rufe shekara ba suka kare suka barmu da wahala, saboda muhimmacin Amana naki yarda in watsa asirin, amma fa duk wata tana bibiyar asirin kamar yadda mijinta ya koya mata.... Shuru gurin yayi bayan Hajja tayi shuru, sai kuka dake tashi a gurin, Murya a dashe Sarki yace "Bazan manta ranar karshe da na ganshi ba, ranar muna tsaye a lambu muna hirar sarautar da za'a bashi, yana tsinko ma shareefah yalon lambu, a kasa ya zubar da yalon ya nufi kofar fita, yana kurewa ganina na bishi na hango Haroun da abokanshi, suna Kallon Adamu ya gifta gefensu babu wanda ya gaisheshi bare ya tambayi inda zashi shi daya... Ashe abubuwan da akayi mishi ba kanshi kadai ya tsaya ba har dukkan mutanen agadez, koda na koma gida babu wanda ya tambayeni shi kowa harkarshi yakeyi har sarki bai damu da tambayar inda yake ba domin babin yareemah shafewa yayi a cikin garin agadez, Ya Allahu ina zanga Adamu, ina zan ganshi.... Ganin kukan bazaiyi musu ba suka fita a gidan Hajja domin babu wani hukunci da zasuyi ma musaka irin ta, hukuncin Allah ma ya isheta, Motocin sarkin sassounburum suka shiga suka je gidanshi suka sallemashi sannan suka wuce airport din katsina domin hawa jirgi zuwa agadez, saboda sassounburum tafi kusa da garin daura.... Shawara suka yanke na baza malamai ayi adduar da Allah zai kawo sanadin haduwarsu in har yana da rai, domin basu yarda da maganar Hajja na ya mutu ba.... *Bawan Allah Adamu tun a cikin garin Agadez ya fara watangaliliya, duk inda ya wuce babu wanda ke ganeshi bare har ya bashi girman dan sarkin da suke matukar so, har ya samu motar da zataje zinder, a can ma saida yayi shekara biyu yana wahala, irin masu shigowa daga kawo kaya daga kano zuwa zinder su yabi zuwa nigeria, A kano ma saida ya shekara daya da watanni har Allah ya hadashi da Alh jogana, nan ya kaishi gidanshi dake kaduna dan yi mishi gadi, anan ne ya bude shago har kaddara ta hadashi da Suwaiba, barin agadez, zuwanshi kaduna, haduwarshi da Suwaiba, rabo ne na ya'ya, wanda Allah swt ya boye wasu al'amura a garesu, Tabbas haihuwar da namijin da suwaiba tayi a farko rubutaccen al'amari ne, mulki na Allah ne, shine yake bada aronshi ga wanda yaso koda kuwa almajiri ne.......* *A gurguje na takaita muku labarin Adamu saboda mu kai inda muke san zuwa a kan lokaci* _Akwai shagalin biki a page fifty...... ku cinka_ Mrs Tijjani Shattima.... [01/04 9:50 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣1⃣ By *Aysha Ya'u kurah* *EMIR PALACE SASSOUN BOROUM* Sarkin sassoun boroum ne tsugune a gaban sarki "TIDJANI YALLO" yana mika gaisuwa kamar yadda sarakuna keyi wa na gaba dasu, bayan sun gama gaisawa aka cika kayayyakin abinci da sha a gabansu saboda girmamawa, babu abinda Sarki Tidjani da Shareefah suka kalla, bare har su kai ga cin shi, cikin nutsuwa da kasaita suka gabatar da dalilin zuwansu, nan da nan aka wakilta dogarai dan suje can rugar Haldo su nemo Hajja yar Ruga su taho da ita, da yake rugar bata da nisa da gidan sarki sai gasu sun dawo, cikin girmamawa suka ce bata da lafiyar da zata iya zuwa, daka musu tsawa sarkin sassoun burum yayi yace "maza su koma su dauko ta, dakatar dasu Shareefah tayi hade da mikewa tace "su barta kawai, su zasu isa zuwa gidanta, Duk yadda sarkin sassoun burum yaso nuna musu kaskancin zuwa rugar Haldo hakan bai hanasu zuwa ba, a cewarsu su suke nema a gurin ta, ya zame musu dole su ganta yau kota halin kaka..... Wani irin wari dakin Hajja ke fitarwa, warin ma marar misaltuwa, tana kwance a kan tabarmar da takai rabi saboda cinyewa, dakyar aka iya dagota ta jingina da wani sudadden pillow, "wani dan kara tayi saboda wani ciwo da yayi mata rami a mazaunanta, yaron dake kula da ita ne ya sa mata wani pillow a gurin ciwon, saboda tausayin halin da Hajja ke ciki ya sanya Shareefah sharar kwalla, Dakyar muryar Hajja ta iya fita tace "sannunku da zuwa, da kai suka amsa hade da gyara zama akan daddumar da dogarai suka shimfida musu, saboda son jin abun da ya kawosu ko kyankyamin dakin basu ji ba, "Daga ina ranka ya dade? Hajja ta fadi baki na rawa, Shareefah ce ta fada mata sunanta da dalilin da yasa suka zo gurinta, bude ido Hajja tayi sosai ta kure shareefa da ido, *SHAREEFAH YALLO* kece? murmushi Shareefah tayi tace "nice, ashe ma kin sanni, kuka Hajja ta fashe dashi tace "farin sani, ni na raineki tun kina tsumma, nafi shekara ashirin a gidanku tun kafin a haifeki, ashe zan sake ganinki, rabona da ke inaga in banyi karya ba yakai shekara arbain, dan tun kina shekara goma sha biyu na bar agadez, ashe ina da rabon sake ganinki ta karashe da kuka hade da tari, Cike da kosawa sarki Tidjani yace "sai hakuri Baba, dama haka rayuwa take, kuma duniya fadi gareta, wata rana in da rai dole a hadu, yanzu gashi sanadiyar mutuwar UMMU AYYU Allah ya kawo mu gurinki, yanzu bamu da isashen lokaci zuwa mukayi ki fada mana labarin da Ummu tace ke kadai ce kika san dashi, labarin YARIMA, wani kukan ne ya kufcewa Hajja a zuciyarta tace "yau labarin da yayi shekara da shekaru a kunshe, hali yasa zata bayyana shi, labarin da ya zame mata tamkar kwai a cikin zuciyarta saboda riritarshi, ajiyar zuciya tayi tace "babu mamaki fitar labarin nan ya zama silar samun warakarta, Nuni tayi ma yaron dake kula da ita wani gurin dake cike da kaya, mikewa yayi ya dauko wata jakar saka ya mika mata, hannu na rawa ta karbi jakar ta dauko wani ginin mutum mutumi wanda yake kewaye da kawunan mutane babu adadi, Saboda tsananin tsorata saida shareefah ta rungumi kafardar mijinta, abun ba karamin tsoro ya bata ba kuma ya daga tsigar jikinta matuka, yadda aka yanyame shi da wasu abubuwa kamar kwari yasanya har sarki jin tsoro amma kadan, wani guri ta daga a gefenta, inda take ajiyar abubuwa, nan ta mike dayar ruwa nabin bayanta ta fita tsakar gidan ta daki wani dakali dake kofar dakinta, nan take gurin yayi rami, hannu tasa ta ciro layu masu tarin yawa, daga can kasa ta hango kurciyar da suka binne shekara da shekaru kwance babu rai ga layu kewaye da ita, a gigice ta ciro kurciyar da duk wata sai ta bata

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156