Chapter 139
Chapter 139
tsari daga sharrin zuciya ya raba jikinshi da nata, da sauri ta wuce ciki tana maida numfashi da sauri sauri..... Cikin kwanaki uku soyayya mai karfi ta wanzu a cikin gidan wanda har saida duk mutanen gidan suka gane, Amal da ta sawa ranta auren Taheer tayi gaggawar cirewa dan tasan dama tuni Nadeeyah yake so, a take tayi wa kanta addu'ar samun duk abin da zai zamo mata alkhairi.... Ga mamakin Nadeeyah sosai Anty Saude ta sake mata ta dinga lallabata tana nuna mata kauna ta musamman.. Hakan ba karamin daďi yayi ma Taheer ba.. A daren ranar alhamis suna zaune dukkansu a parlor Taheer na yanke ma junior farce yana tsoma baki cikin hirar tasu.... Kallon shi Anty Saude tayi tace "Munyi magana dazu da kawu Tidjani, na faďa mishi maganar zuwa neman aurenka, na sanar dashi ina son ayi komai cikin sati ďaya dan banasan wata matsala ta biyo baya, Mikewa Nadeeyah tayi ta wuce ďaki da sauri, Dariya yayi yace "Sai su taho ranar sati dan mu haďu tunda gobe zamu tafi, ni zanso ma a ďaura auren a ranar Mommah tunda babu wani shirin da ya rage.. Buďe baki tayi cikin mamaki haďe da sakar mishi dakuwa, Dariya yayi sosai ya dauki Junior suka wuce dakin Nadeeyah...... ******* *Kaduna* Toshe hanci Raudha tayi kamar zatayi amai, hawayen idonta ta share tace "Ya Allah ka sassauta mana, mun wahala iya wahala, mun gina ramin mugunta mun auka ciki, wuyar da muka so wata tasha ita muka haďiya har na tsawon shekaru takwas... Audugar da ta share ruwan ciwon dake fita a jikin Goggo ta yar a bola.. mistakely ya sauka cikin waken da Radiya ke gyarawa, Wata ashar ta sakar mata haďe da mikewa tace "wallahi bazan dafa abincin ba, ni na gaji wallahi, duk ku kuka jamin, yanzu ga Shamsu ko waiwayata baya yi, yana can ya koma Italy da zama shi da yarinyar da tayi min aikatau, wannan wace irin masifa ce.. Mummy dai jinsu kawai takeyi tana kokarin daga Goggo ta daurata akan pour, Kafin ta daurata har ta saki kashin a gurin, a sittin su Raudha sukayi waje dan dama su ba aikin sukeyi ba, Shekara uku kenan Goggo na fama da ciwon da babu wanda yasan irinshi, asibiti sun gaji sun maido ta gida, wani katon rami mazaunanta yayi saboda zama, ga wasu ramuka da jikinta yayi yana fitar da ruwa mai matukar wari, Mummy ce kullum ke hidima da ita saboda a yanzu komai ya fice mata a rai, gara tayi wannan, ta yiwu Allah ya yafe mata sanadiyyar hakan, Dakyar ta iya wanke mata kashin ta canza mata gurin kwanciya, saida ta gyara dakin tsaff sannan ta fita dan shan iska.. Tana zama taji sallamar su Papy da ahalinshi da su Anni, nan fa ta mike ta dinga musu maraba, yadda ta fita hayyacinta sai wanda dama ya santa shi zai ganeta, duk da yanzu suna samun gata domin Raliya na taimakonsu sosai.. Bayan sun duba jikin Goggo suka koma dayan dakin suna ta hirar yaushe gamo, Awan su ďaya sai ga su Hafeez da 'yayanshi uku.. Suwaiba, Adam, da Autan wanda yake hannu mai sunan Papy, sai Husna da ta zama big madam, Dakin suka shiga suka gaida su Mummy sannan suma suka zauna akayi hirar dasu.... Daddy ka dawo ne? akwai abin da nake so mu tattauna.. Raliya ta faďi cikin girmamawa kamar yana gabanta, "Eh Raliya, muna kaduna, jibi zan koma lagos kina iya zuwa gida yanzu, Cike da jin daďi ta mike ta fara shirin zuwa gidan su Goggo dan ta taho dasu Mummy, dama tun last week ta gindaya ma Anty Reemah karyar Goggo ta shiga coma tazo su dubata.. Anty Reemah ta tabbatar mata yau suna nan tafe, saida ta kaiwa su Fadeel abinci makaranta sannan ta wuce gidan Goggo... Taji dadin ganin su Papy, nan take ta shirya plan din da yasa duk suka shirya tafiya gida.. Goggo kaďai aka bari a gida sai Rilwanu dake zaman jiran zuwan iyayenshi.... Suna isa gidan Mummy ta fara hawayen bakin ciki da dana sani, lallai in baka godewa Allah ba to tabbas zaka godewa azabarshi, A darare ta karasa cikin gidan saboda gudun wulakanci a gurin mamallakin gidan... A lokacin da yaji sallamar su yana parlor yana kallon news, da sauri ya mike ya taro Papy yana faďin maraba da proff, bismillah shigo, bai lura da mutanen bayanshi ba saboda yadda yayi kewar ganinshi shekara da shekaru, Saida suka nutsu cikin gaisuwa sannan ya kalli sauran mutanen parlon, yana sauke idonshi kan su Mummy mood dinshi ya canza gaba ďaya, Cike da masifa ya mike zaiyi magana yaji Sallamar su Anty Reemah, nan take fuskarshi ta sauya yace "A'a yau gida yayi albarka, Allah ya sanya alkhairi a wannan taron.. kafin a amsa da Ameen Muryar little Nadeeyah ta karaďe parlorn, *HABIBI*, *YAA OMRI*.. Ta sama Musaddiq ya leko dan jin muryarta kamar amsa kuwwar speaker.. ganin parlon a cike yasashi sakkowa da sauri.. Da ita ya fara tozali rike da kugu tana mishi wani irin kallo, karasowa yayi ya dagata sama ya dinga juyata tana kyalkyala dariya, Wani wawan duka Hilal ya kai mishi a baya sai a sannan ya dakata ya rungumeshi, haka nan ya tsinci kanshi cikin farin cikin da ya rasa na meye, Cikin parlon suka karasa suka gaiggaisa da mutane, Mummy ce kadai ya gimtse fuska kafin ya gaisheta, shi dinma dan yaga su papy ne a zaune da Anty Reemah dake yawan matsa mishi, hirar yaushe gamo palon ya karaďe dashi, Sudai su Mummy suna ra'be kamar Mamma Suwaiba lokacin da take da rai bata da galihu, *Allah kenan*, babu yadda bai iya ba..... Murďa kofar dakin sukaji anyi an shigo ba tare da sallama ba, Yara biyu farare cikin kayan fulani kafarsu tayi butu butu suka shigo suna ta ďari ďari da kafarsu dan kar su faďi, can bayansu kuma mace ce ta shigo naďe da zani akanta hannunta rike da kullin dankwali, sai wani namiji fari da riga budaddiya da layu a duk jikinshi har kunne, Babu wanda a cikinsu ya gane Badariyya, sai Mummy wacce ko a cikin dubu ne zata tsamo ta, "BADARIYYA! "Na'am Mummy ta amsa haďe da fashewa da kuka, karasowa inda take tayi ta rikota haďe da yin wurgi da kayan hannunta, kowa a cikin parlon da ido ya bita cike da mamaki, Zama yaran sukayi a gefe suka matse juna su a dole suna tsoron tiles, Shi kuwa Yareemah Suhail gani yakeyi duk ya fisu muhimmanci a parlon, Hafeez ne kaďai yayi mishi kwarjinin da zai iya tsuguna mishi, direct gaban Hafeez yaje ya tsuguna har kasa irin gaisuwar da akema sarki yace "Ina wuni ranka ya dade, Shi Hafeez abin ma tsoro ya bashi, da sauri ya maida kafarshi baya yace "Ga iyayenmu can su ya kamata ka fara gaisarwa, "Duk cikin runkar nan babu mutum mai muhimmanci, daga kai saini, ranka ya daďe, sauran duk mu ya kamata su gaisar... Kallon mahaukaci duk sukayi mishi suka maida dubansu kan Badariyya wacce take kuka tana neman gafara, Labarin abinda ya faru da ita ta fara basu, har yadda ta taimakawa su Mummy suka raba Nadeeyah da Musaddiq saida ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156