Chapter 10
Chapter 10
me nayi,? Dan Allah kiyi hakuri, Wai me yake faruwa ne? kuka mamma takeyi iya karfinta gunin ban tausayi, kallonta Malam Adamu keyi hawaye na zuba ta gefen idonshi a ranshi yana mai Jin dadin kukanta domin ko ba komai zata samu saukin nauyin dake cikin ranta, sai da tayi mai isarta ta share hawayenta, ta kalli Nadiya dake kuka tana share hawayen idon mahaifinta tace "tashi maza kije kiyi wanka kiyi sallah, bari in nemo miki abin da zaki ci, Nadiya ta share hawayenta tace "ki barshi kawai, bari nayi wanka in daura mana, zauna ki kula da baba, Gyada kai mamma tayi kawai, dan bata son tasan abinda ke faruwa, Nadiya na shiga bayi mamma ta fita shagon Tasi da ya kara cika ba kamar da ba, Indomie da Kwai ta ce ya bata, dakyar ya bata dan yana bin ta bashin kusan dubu daya da dari hudu, da sauri tayi cikin gidan, ta hado yayi, ta sauke ruwan dumin da ta daura ma mijinta, ta iza wutar ta daura Indomien cikin karamar tukunya.. Wanka da sallah Nadiya tayi, ta saka doguwar rigar deep blue material mai gajeren hannu ta shan iska,, ko mai bata shafa ba ta daura jar hula a kanta, kyawu mai sirri da cikar budurci suka bayyana a tare da ita, wani irin kyau Nadiya ke dashi marar hayaniya, wanda ya kara fitowa saboda dan hutu da kuma rufin asirin da suka samu,, kusa da Mamma ta tsaya tace "sannu da aiki mamma, ina Zainab? "Tana islamiyya,, mamma ta bata amsa tana tura leda cikin murhun, Tambayoyi ne cure cikin zuciyar Nadiya, ta rasa wanda zata tambaya ya bata amsarsu, ko zata mutu tana tambayar mamma bazata amsa koda tambaya daya cikin tambayoyin da take dasu ba,, Daki ta shige gurin mahaifinta da ya fara bacci numfashin shi na fita dakyar, Kure shi tayi da ido tana addu'a tana tofa mishi, Mamma na kwashe Indomien zainab ta shigo gida da gudu jikinta yayi futu futu, "mamma yunwa nake ji, zainab ta fadi murya a sarke saboda tsabar gajiya.. kallon Indomien mamma tayi tace to bari kiyi wanka ko? , noke wuya tayi kamar zatayi kuka tace cikina na murda min, je ki wanke hannu kizo muci, Nadiya ta fadi tana fitowa daga daki, rungumeta zainab tayi tace "yaushe kika dawo anty? Dazu kina islamiyya, da fatan kina karatu a makaranta, Nadiya ta tambayeta tana shafa kanta,, gyada kai zainab tayi tace Sosai ma, kin kawo min chocolates, Kumatunta Nadiya taja tace "eh yana jaka ta, maza wanko hannu muje muci abinci.. Mamma kinci abincin ne? Nadiya ta tambaya idonta kyar akan mahaifiyarta, mamma dake kofar daki tace "eh munci sosai, bansan zaki dawo ba da na ajiye miki, zainab da ta kai Loma kamar zata shake tace "mamma yaushe kika ci abinci?, bayan tafiya ta makaranta, shine kika cinye baki ajiye min ba, mamma ta saci kallon Nadiya, tayi saurin maida kallonta gurin zainab tace ba gashi kina ci ba, maza kici karki kware, Nadiya dai hannu kawai take juyawa cikin abincin har zainab ta kai karshen shi harda sid'e kwanon, meya ke faruwa mamma??? Tambayar ta fito a bakin Nadiya cikin rashin sanin fitowarta, me kika gani? Mamma ta amsa ta cike da fargaba, rarrafowa Nadiya tayi ta dafa cinyarta tace "mamma boyemin abin da ke damunki bashi da amfani, nasan bani da maganin shi amma atleast zaki ji sauki in kin fada min..... ********** Ohh ni!!! "wacce iriyar rayuwa ce wannan? d'aki kaca kaca sai kace ba na mata ba, mummy ke mitar tana tafe tana tsintar kayayyaki a kasa da takalma, Husna dake kwance tana duba littafi tace "kema kin San ko aikin waye mummy, "ni gaskiya na gaji wallhy, canza min daki za'ayi, bazan iya wannan rayuwar ba, kwance take cikin matsatstsiyar jar riga da yellow mini skirt, Gashinta Parke a tsakiya da yellow ribon, kunnenta dauke da earpiece alamun bata ma San me sukeyi ba, kada kanta kawai takeyi tana bin wakar hade mutstsuka santala santalan kyawawan kafafuwan ta, kafarta mummy taja a hankali, juyowa tayi tana cire earpiece din kunnenta cike da rashin da'a tace "ya akayi ne mum" mummy ta ajiye kayan makarantar ta a gefen gado tace "babu komai baby na, kinci abinci dai ko? gyada kai Badar tayi alamar eh sannan ta juya ta mayar da kanta kan pilo tana cigaba da jin waka hade da chatting,, "hmmmm" kawai Husna tace ta sakko daga kan gado tace "mummy zanje gidan Anty Raudha, "me akeyi?? mummy ta tambaya tana gyara ma Badar skirt dinta, "birthday din Amal diyar Anty Laura, Husna ta bata amsa, gyada kai mummy tayi tace "too jira Badar ta shirya ku tafi tare, hanyar bayi husna ta nufa tace "bata San me muke fadi ba sai ki fada mata dan gaskiya ina shiryawa zan tafi, Badar da ke saurarensu da kunne daya tace "kifi ruwa gudu, ke kika damu da local partys, duk inda kika ji sha'ani jiki na rawa kin tafi, 'anyways baki yar a kasa ba, maida earpiece dinta tayi ba tare da ta kalli mummy ba ta cigaba da danne dannen waya, Husna kuwa bayi ta shige cike da bacin ran irin rainin da Badar ke ma mummy, abin da ke kara bata ranta bai wuce yadda mummyn ko a jikinta ba, duk rainin da badar ke mata sai dai tace "yarinta ke damun ta, ita kuwa komin kankantar abu in tayi mummy ta dinga masifa kenan kamar zata ari baki, watsa ruwa tayi cike da takaici da tunani iri iri.... Mrs Tijjani Shattima... [04/12 09:47] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU By Aysha Ya'u Kurah 1⃣2⃣ A hankali take maimaita kalmar "innalillahi wa Inna ilaihir rajiun" ruwan hawaye na tsere akan kumatunta, kirjinshi take dannawa tana share kumfar jinin dake fita a bakinshi, nishi yakeyi Sama Sama yana kakari da karfi, magana yake fisgowa daga can kasan makoshinshi, muryarshi ta kara karfi tamkar amsa kuwwar loud speaker, "kiyi Hakuri suwaiba! , kiyi Hakuri da rayuwa, nasani ban jiyar dake dadin duniya ba saboda talauci na, gashi zan tafi in barki cikin rayuwar talaucin da babu mataimaki, kiyi hakuri suwaiba, Allah kadai yasan tanadin da yayi mana a lahira, ki cigaba da hakuri da duk yadda kika tsinci kanki, nasani kin iya kanki, ki rike yaran nan,, basu da kowa a duniya sai ke, ki fadawa Hafizu in ya dawo na yafe mishi,! na yafe mishi,! na yafe mishi,!!! Idonshi da yake lumshewa ya daga Sama, ga azabar zafin fitar rai ga kuma radadin barin iyalanshi cikin yanayi na rashin garkuwa, Ya Allah! ka iya ma zuri'ata abin da bazasu iya yi ma kansu ba, LA' ILAHAILLALLAH----- kukan mamma ya karu saboda tsabar firgici, A gigice Nadiya ta farka daga gajeren baccin da ya dauketa saboda jiyo kukan mahaifiyarta, fitowa tayi daga daki da sauri har tana turgude kafa ta karasa dakin baban su, kasa shiga tayi saboda hangoshi da tayi damke da karfen gadon dakin hade da hannun mamma, yana haki da sauri sauri. Juyawa tayi ta fita a gigice, "wake ta takalmi ko mayafi a wannan lokacin", gudu takeyi da iya karfinta, ita dai tasan jefa kafafuwan ta kawai takeyi, bata ma San akan abinda suke sauka ba,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156