Skip to content

Chapter 56

Chapter 56

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

Harira, wacce ta kunso cikin shege aka korota daga garinsu ta dawo nan, ashe kai ka kunsa mata, gashi dai kamanni sun bayyana min komai, wallahi kaji kunya, ta karasa fadi tana haki.. "innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai Baffa da Papy ke fada, ganin shurun da Baffa yayi ya kara hassala Ma'u ta fara surfafa masifa da bala'i, babu inda baya rawa a jikinta, da dai Anni taga shuru bazai taimakesu ba tace. "Wallahi tallahi ban taba koda magana dashi ba... shuru Ma'u tayi tana hararar Hanne tana fadin rainin hankali, uban wa zaki rainawa hankali? "gyara zama Anni tayi ta kalli Baffa tace "in ka yarda dani ka bani dama inyi maka bayanin komai, idonta ta mayar kan Goggo tace "in kikaji labarin abinda ya faru, da kuma yadda ya faru ni nasan gode min zakiyi ba zargi da zagi ba, ni ko a yau Allah ya dauki raina walhy naji dadi saboda zan cika buri na, kullum bani da tunanin da ya wuce ta yaya zan wankewa Abdallah zuciyarshi, ta yaya zan hada shi da mahaifinshi, nasan duniya tana da fadi wata rana ina da yakinin Allah zai amsa min addu'ata, sai gashi ta dalilin Hafeezu adduar da na dade ina yi Allah ya amsa... Alheri danko ne... Kallon su Radiya dasu Hafeez tayi tace "dan Allah ko yaran nan zasu dan bamu guri, "babu inda zasu, Ma'u ta fadi tana tafa hannu, kallon Jamal Mami tayi tace "dauki Ruwaidah ku tafi mota, noke wuya tayi tace "um um, zare mata ido Mami tayi zatayi magana Anni ta dakatar da ita, "zo takwara, zo kuje ku siyo min Goro kinsan kin fishi wayau naki yafi kyau, Jiki na rawa ta mike zata wuce ta taka kafar Radiya, da karfi ta hankada ta cikin ihun azaba saboda tsinin takalmin tace "ke makauniya ce? baki ta bare ta fara kuka idonta kyar akan Radiya, da sauri Hafeez ya ja hannunta suka fita yana rarrashinta, Harara Mummy ta sakarma Radiya tace "sai kace kina yi da sa'arki, turo baki tayi tace "mummy zafi wallahi, "tashi ki bamu guri dalla,mummyn ta fadi a hassale, da sauri Goggo tace "babu fa inda zata, gyara zaman ki, abun kunya ce suka kwaso suji kunyar su kadai, Girgiza kai Anni tayi tace "babu komai ma, zauna! labarin an yishi ne, ba kirkirarre bane, kaddara ce.. Kamar yadda kika sani ni kanwar Harira ce, mahaifina asalinshi dan Gombe ne, mahaifiyata ce yar jalingo.. Allah ya jarabceni da soyayya da dan kanin babanmu, mun dade tare dashi, kullum in na fita tallan nono a gurin yake zama har ya kare, mu tafi gida.. wata rana nono na yayi kwantai, yakai ni dare, a hanyar mu ta dawowa gida kaddara ta afka mana, kaddarar da dan adam bai isa ya tsallake ta ba, kaddarar dake sanya rayuwar budurwa da iyayenta cikin mawuyacin hali... kaddarar da ta sanya Mahaifina rasa rayuwarshi... Bayan an fahimci ina dauke da ciki, saboda tsabar kunya irin ta fulanin "da" mahaifina ya kashe kanshi ta hanyar fadawa cikin teku, a cewarshi bazai iya fuskantar jama'a ba.. mahaifiyata da kishiyoyinta suka sani a gaba, bani da katabus cikin kauyenmu, ko kofi na taba babu wanda yake dauka, haka in na fita gari an dinga darewa kenan, shi kuma wanda yayi min cikin an nemeshi ko sama ko kasa an rasa, daga baya ne muka samu labarin mutuwarshi, nan fa na cire duk wani tsammani na samun mijin aure, saboda tsabar tsana da iyaye da yanuwana suka min na fita hayyacina na kare na lalace, mahaifiyata ma kunya ta sanyata ta rame, saida abin ya isheta tace "in shirya in tafi jalingo gurin mahaifiyarta, To acan ma hakan take domin kuwa saida na gwammaci zama a Gombe da zaman jalingo, duk ranar jumma'a sai Yakumbo kakata ta turani Gembu gidan Harira saboda gudun kunyar jumma'a, tana tsoron kar mutane su shigo su ganni, gaba daya yan uwa sun tsane ni ta ko ina, bani da gurin shan iska... wata ranar jumma'a mai cike da ban alajabi da tsoratarwa, Jumma'ar da manta ta ga yan uwan mutanen kauyen Gembu abu ne mai matukar wahala.. Tun cikin dare nake jin kaina kamar bani ba saboda yadda cikina ya dinga murda min, a hakan Yakumbo tace in fito in wuce Gembu, tun a hanya cikin ke murda min har al'amarin yaso fin karfina, cikin ikon Allah cikin ya lafa min har muka shiga cikin kauyen, a daddafe na karasa cikin kauyen nayi gamo da tashin hankalin da yasanya cikina kadawa har kafata ta gaza daukata, ina kallonka sanda ka dauko matarka da wata mace kuna gudu, da rarrafe na bi bayanku har nazo lungun shiga gidanku, nan gaba daya karfina ya kare, haihuwar ta taho min gadan gadan, Cikin ikon Allah na haifi 'yata mace, dankwalina na cire na nadeta dashi hade da mahaifar, koda na duba ta na dinga jijjigata na tabbatar bata raye, anan ne nayi kuka sosai har muryata ta dashe, ban kara sanin inda hankalina yake ba saboda zubar jinin da nakeyi.. Iska mai karfi ce ta taso a kauyen wacce kafin ruwa ya sauka saida ta dauke gidaje, wannan iskar ita ta farkar dani nayi saurin mikewa da gawar yata na fada cikin gidan ka, koda na shiga babu kowa a gidan sai kasar da ke tashi tana rufe ko ina na gidan, Daki na shige da sauri, har cikin dakin kasar ke shiga saboda iskar ba ta wasa akeyi ba, Iskar na lafawa ruwa ya tsuge kamar da bakin kwarya, A nan ne naji ihun jariri daga waje, da sauri na fito na iso gurin na hango dan Mala'ikan Allah cikin zani kwance a kirjin mahaifiyarshi, Share hawayen idonta tayi tace "Allah shi ke raya Matacce a lokacin da yaso, in ba Allah ba waye zai raya wanda kasa ta rufe idonshi, ko da na dagoshi jini ne ke fita daga cikin cibiyar da ba'ayi mata yanka da kyau ba, nan take nayi daki dashi na gyara yankan cibiyar na daureta da tsumma, ruwan bai tsagaita ba sai can gurin magriba, yana tsayawa na kunshe yata na mayar da ita cikin gawar da Allah ya nuna ikonsa akanta, A tare na rufesu da kyau saboda ko yadda aka zuba kasar wata rana ruwa ka iya dago gawar saboda sam kabarin baiyi zurfi ba.. A lokacin ne na fahimci wani abu guda daya game da cikin da nayi, wannan abu kuwa shine bak'in zare mai shara shara wanda babu mai ganinsa sai ubangiji, wannan zaren kuwa shine zaren kaddara! kaddarar rainon Abdallah ta nuna Baffa tace "danka, ita ta sani na dauki ciki har sanadiyar shi nazo har wannan kauyen.. Da fari a kullum ina tunanin ni kadai ce Allah baya so a duniyar nan da ya jarabceni da yin cikin shege a cewar bahaushe, haduwata da Abdallah na fahimci dama nazo duniya ne domin shi, koda na koma gida Yakumbo tayi tayi ta rabani dashi, a lokacin ne na nuna musu nima ina da hakki akan dana, tunda ni na haifeshi, babu wanda ya taba samun labarin bani na haifeshi ba, A lokacin da na bijirewa yakumbo sai ta koreni tace in tafi gurin uwata ita bazata iya da wannan abun kunyar

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156