Chapter 17
Chapter 17
ta matso da kunnenta kusa da bakin Nadeeyah, rada tayi mata a kunne wanda Allah kadai yasan me tace mata, sai ko Zainab ta kyalkyace da dariya hade da rungume Nadeeyah, tace "dagaske kikeyi Anti? Gyada kai Nadeeya tayi tace "eh, hawayen da ta boye ne ya fara bin idanuwanta, ta kankame zainab tana zubar dasu ba tare da ta bari ta gansu ba, wayyo mutuwa.....! @ Mrs Tijjani Shattima....! [07/03 6:31 AM] fareedah: ●ZUMUNCINMU A YAU● 1⃣9⃣ By Aysha Ya'u Kurah Had'a kayayyakinsu cikin jaka Nadeeyah keyi, idanuwan nan nata sai ambaliyar ruwa suke, Hafeez ke tayata had'a kayan yana labarta mata abubuwan da suka gifta tsakaninshi da iyayensu a yan watannin da suka shude, jan numfashi yayi kamar karamin yaro, daga zuciya har idaniyar shi zubar ruwan hawaye sukeyi, "yan kudaden da suka fara shigowa hannuna su suka ruda ni, na canza abokai, kullum bani wancan club bani wancan, ban tsaya nan ba har sai da na koma harkar mata, tun ina boyewa, su Baba basu sani ba har takai ga mata har gida suke biyoni, bazan taba manta daren da zan bar gida ba, Baba ya fito zai tafi Sallar asuba ya jiyo muryata da SAILUBA yar gidan Hinde mai tuwo, ranar a daki na ta kwana, Koda Baba ya bude kofar, Sailuba na kwance a jikina, duk yadda na kai ga tureta in suturta jikina ta kafe ta danneni, na kasa tabuka komai, saida Baba ya juya, nayi karfin halin turata na mike nasa jallabiya nabi bayanshi, Kuka na tarar dashi yana yi a tsakar gida, a tare muka iso inda yake ni da Mamma, ajiye butar hannunta tayi ta fara tambayarshi dalilin zubar hawayenshi, bai kai ga yin magana ba Sailuba ta fito da daurin kirji da kayanta a hannu tana sawa tana fadin "Zo ka sallameni Hafeezu in tafi kar a nemeni a gida, wani irin juwa Mamma ta ji a tsakiyar kanta, bakinta da kyar yake iya furta innalillahi wa inna ilaihir rajiun, daki Baba ya jata ba tare da ya dubi inda na ke ba, koda na biyosu ciki da sauri Baba ya dakatar dani yace "fitar min a daki da kazantar dake jikinka, tafi kaje ka sallameta, ka wadata ta da duk wani nau'i na jin dadi tunda kaima ta jiyar da kai dadin, ubangiji Allah ya shiryar dakai Ameen, Har na iso kofar dakina ina jiyo sautin kukan mamma, Baba yana ta bata hakuri.. Da kudin da ni kaina bansan yawansu ba na sallami Sailuba, sai na wuce nayi wanka nayi sallah, shaidan ya dinga raya min in bar gidanmu in tafi can inda babu wanda yasanni, tunda ina da kudina inje in ci karena babu babbaka, a haka nabi umurnin zuciyata na shirya kayana tsaff na sasu a mota, Zainab na gani a kofar shagon Tasi, na bata dubu biyar ta kaiwa Mamma, nace ta fada musu nayi tafiya, tun kafin ta shiga gidan na shige mota nayi gaba, a tunanina duniyata zatayi kyau tunda babu mai samin ido, ashe tafiyar da zata kashemin zuciya ta barni da dana sani har karshen rayuwata nayi... ya karashe maganar cikin matsanancin kuka... Takalman Zainab Nadeeyah ta tura cikin ledar dake hannunta, wacce tun fara bata labarin ta budeta da niyyar zuba takalman, ledar ta jike sharkaff saboda hawayen da ke sauka a kanta, kallon Hafeez tayi tace "Yaya Allah yayi mana jarabawa mai zafin gaske, rayuwa ce yanzu zamu fara ta wacce bamu san inda zata kaimu ba, ka godewa Allah da yasa suka yafe maka, sannan kaji tsoron Allah, ka nisanci duk wani aikin alfasha, kasani duk abinda zakayi yanzu za'a tada su Mamma ace su tashi suga dansu, shin irin wannan tarbiyar suka baka, kasani yanzu babu wani wanda zai fada maka gaskiya, rayuwa ce zakayi ta ta rashin mafadi, kai da kanka zaka zama mafad'in kanka, ni da zainab kuma duk inda zamuje na tabbatar bazamu rasa mai kwaba mana ba, kaga mummy yanzu ta canza, matsalata daya itace "Bad----- shigowar Hinad cikin dakin ya katseta, ta kallesu tace "Nadeeyah Mummy tace kuyi sauri, hawaye ta share ta dauki karamar jakar, Hafeez ya dauki babbar suka fito sukayi waje, loda kayan sukayi a motar Hafeez, sannan kowa ya shiga mota, Hinad da Nadeeyah motar Hafeez suka shiga, makota suka kewaye su Nadeeya anata musu fatan alkhairi, Tasi ya leko ta windon motar, ya miko mata ledar lolli pop idonshi cike da kwalla yace "ki ajiyewa Zainab, Allah ya hadaku da alkhairi Nadeeyah, Wani kukan ta fashe dashi na tuno memories dinsu na lokacin da dukkan iyayenta suna da rai, da irin kara kainin da sukayi tsakanin gida da shagon Tasi, Tasi ya bada gudunmuwa mai karfi a rayuwarsu, bai taba kazawa gurin tallafa musu da bashi da kuma kyauta ba, kallonshi tayi yana share hawaye tace "mun gode Tasi Allah ya saka maka da gidan aljanna.... Islamiyyar su Zainab suka biya dan daukota, motar Mahmoud suka tarar a kofar makarantar, kafin suyi parking suka hango Musaddiq rike da hannunta sun fito daga ciki, baya ya bude mata suka shige, Mahmoud yaja motar suka wuce, Bayansu Hafeez yabi, zuciyarshi ta dan rage zafi da fargaba saboda yasan in shaa Allahu Musaddiq da mahaifinshi bazasu bar kannenshi cikin garari ba..... A katafaran gidan "Alhaji Mukhtar Kyari dukka motocin sukayi parking, Ta window Badariyya take lekensu daya bayan daya, Husna da dawowarta daga saloon kenan ta fito daga bayi tana kallon Badariyya a jikin Window tana leke, murmushi tayi ta zira Hijab dinta ta fito tsakar gidan tana ma mummy barka da dawowa, dan ita ba gidan rasuwar take kwana ba, gidan Anty Raudha take bin ta su kwana, yau ne kadai bata je gidan rasuwar ba taje saloon dan wanke kanta, Anty Radiya da Anty Raudha suka kalleta cike da shakiyanci suka ce "Amarsu ta ango, cikin rashin fahimta ta waiga bayanta taga babu kowa tace "wacece haka? Dariya suka kwashe da ita suka ce ke mana! Zatayi Magana Anty Reemah tace "wani irin sakarci ne wannan, ku dan matsa daga can mu wuce sai ku cigaba da shakiyancin tunda sa'arku ce Husnan, darewa sukayi ta wuce ita da Anty Raliya, harara Raudha tabi Raliya dashi tayi tsaki tana kunkuni a ranta, "su in an barsu mutanen kirki, Radiya tace "manta dasu dallah, taja Husna sukayi ciki, mummy tayi kamar bata jinsu tace ma Nadeeyah su kamo kayan su shigo, A d'arare ta dauki jakar ta fara tafiya, kama gefen jakar Hinad tayi suka karasa cikin parlon, wani irin faduwar gaba Nadeeyah taji, idanuwanta suka ciko da kwalla, tuno abubuwa mabanbanta da suka faru da mahaifiyarta na rashin dadi ta dingayi, wani lungu ta zauna inda suka saba zama da mahaifiyarta in sunzo gidan..... Labulen windon Badariyya ta saki kirjinta kamar zai fado saboda bakin ciki, bata hango Nadeeyah ba, amma ganin Zainab a gurin Musaddiq suna magana yana dariya ya tabbatar mata da lallai su Nadeeyah sun dawo gidansu da zama, bata karasa tunaninta ba taji an shigo dakin ana dariya, Cikin kaguwa Husnah tace "Anty Raudha tell me, waye amaryar plss, Radiya ta ajiye yaronta Fadeel a kan gadon tayi hanyar bayi tace "ke mana, kece amaryar Hafeez, wata dariyar suka sake kecewa da ita sannan Radiya ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156