Skip to content

Chapter 140

Chapter 140

Zumuncinmu A Yau Book One Complete Hausa Novels 1 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

faďa musu sannan ta roki gafararsu domin ita yanzu rayuwarsu ba irin tata bace... Cike da takaici Daddy yayi daya sanin haďa zuri'a da jinin Ma'u, Wani irin huci ya furzar na bakin cikin irin halayyarsu, mugunta ma har ga kanka sai kayi ta domin biyan bukata, tirrr da dabiyar karnuka irin tasu Goggo ya faďi da kausassar murya... Ke Badariyya... ,tashi maza ki fitar min a gi---- Jiniyar da sukaji ne ya sanya shi yin shuru domin sauraron daga inda jiniyar ke fitowa.... A take Yareemah Suhail ya durkusawa Hafeez kamar zai bauta mishi, Allah yaja ran sarki mai jiran gado, Abubuwa masu Muhimmanci Allah ke yinsu, Mu aron mulki mukayi ta karfin tsiya, kai kuwa Allah ne ya baka shi daga fadar shi, wannan mulkin rubutacce ne a cikin allon Allah, Allah ya baka nasara... Buďe baki Hafeez yayi ya koma can baya, da sauri Husnah ta riko hannunshi suka koma daki dan a ganinsu wata cutar yarima suhail zaiyi mishi..... Mrs Tijjani Shattimah...... [12/06 7:23 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 7⃣1⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Cikin azama ta fara tattara langunan gabanta tana turasu cikin lokar katakon dake kofar dakin da aka bata, "Badariyya ina naman da kande tace mu raba? Kinga bana son tashin hankali, ki fito dashi kawai mu raba, wannan ma ai keta ce, Sharce zufar da ke goshinta tayi ta kalli Marakisiyya tace "Na cinye, na bawa Tanimu da jazuli suma sunci, kinga sunci kason uwarsu, ni nawa 'yayan ko kamshi basu ji ba, "Marakisiyya ina namanmu? gashi can su Hannafi suna ci suna mana gwalo, "Tanimu ďan Marakisiyya na farko ya faďi cike da dacin rai.. Maida kallonta gurin Badariyya tayi zuciyarta na k'una ta kasa yi mata magana sai nuni da tayi mata da hannu na "kina jin abin da Tanimu yake faďi? Tsaki mai karfi Badariyya taja ta wuce daki tana goge fuska da zaninta da yasha jiki, Tana sanya kafarta cikin dakin taji an shako wuyanta harda haďawa da labulen tsummar dake kofar dakin, Marakisiyya bata jirayi komai ba ta fara naushin bakin Badariyya tana faďin ina naman mu yake?wallahi in baki fito da naman nan ba sai na yagi na jikinki ya zame mana naman shekarar da bamu ci ba, "Ke ni fa a yanzu saidai a mutu a gidannan, dan wallahi kiriss ya rage in fara maita, in banda mugunta naman da kika san sai shekara muke cinshi shine kika haďa da nawa da naki kika cinye saboda haďama, Wallahi ko ki fito min da naman nan ko inyi fata fata da naman cinyarki, yin karar suya bazai min wahala ba ko Tanimu yayo... Yadda take maganar tana haki idanuwanta yayi jawur ya sanya Badariyya tsurewa, "Tabbas Marakisiyya ta fara maita, cikin muryar azaba jini faca faca da bakinta tace "Sakeni zan baki! Sake shake ta Marakisiyya tayi tace "Ai saidai muje tare, wallahi babu inda zaki ke daya, matsiyaciyya mai bakin hali, Kuka Badariyya ta fashe dashi ta fara tafiya har ta isa gurin da ta boye naman, tana sa hannunta taji an wafce langar harda hannunta sannan ta hankadata jikin katakon, kusar dake jiki ta caki tsakiyar goshin Badar, Wani irin ihu ta tsala wanda ya tattaro hankalin mutanen cikin yalwataciyyar bukkar sarkin, Kande ce ta isa gareta ta toshe mata gurin jinin sannan ta shige da ita daki, ita kuwa Marakisiyya ko a jikinta, namanta ta tusa a gaba suna yaga ita da 'yayanta..... ****** Nayi Nadama, Na tuba, wallahi na yarda zan zauna da kai, yanzu 'yayana biyu da kai, Hannafi, da Suwidi, ina zan tafi in barsu? dan Allah ka yenta ni kamar yadda ka yanta gimbiya Sailuba, na saduda zan zauna dakai, wahalar da nake sha a gidannan ta isheni, ka taimakeni ka kaini inga iyayena ko sau ďaya ne takk, nayi alkawarin bazan bujire maka ba duk abin da kake so shi zanyi---- ta karashe cikin matsanancin kuka.. garin maganin da aka sa mata a goshi ya murmuso mata a ido... Dariya yayi sosai yace "Wuya makarantar kare, To ai dama laifinki ne da kika biye wa mai son zuciya irin Marakisiyya, da a yadda aka kawoki gidannan kinyi min ladabi da babu abinda zai hanaki fin Sailuba fada a guri na, to sai kika nuna kinfi Marakisiyya rashin imani, shiyasa na nuna muku karfina a kanku, na sanya ku kuka zamto tamkar karnuka, tunda kin gane kanki yanzu to baki da matsala, zan kaiki kiga yan uwanki nan bada jimawa ba, amma sai naga kamun ludayin nadamarki, in har kika canza hali gaba daya to babu wanda zai kaiki jin dadi duk cikin matana domin na fi kaunar kasancewa dake.... Janyota jikinshi yayi cikin wani irin siga ta sha'awa, karfin turaren dake tashi a jikinshi ya kusa zautata saboda tsabar rashin dadi, wasu zafafan hawayen dana sani ne ya dinga kwaranya a cikin idanuwanta, dana sanin rashin kasantuwarta mutuniyar kirki har halayyarta da kaddararta ta sanya wannan masifar afkuwa da ita, tunano irin rashin mutuncin da ta dinga yi ma yan uwanta musamman Nadeeyah da Musaddiq tayi, da ace lokaci zai sake bata dama, da ta kaunaci har mai gadin gidansu, da ta nuna ma yan uwanta kauna domin tana tsananin kewar su... Ta sha wahalar da ko makiyinta bata fatan yasha, mace kamar ita ace bata da zanin kirki da take daurawa, dakin baccinta babu ko katifar da zata sanya hakarkarinta, ba'a ma maganar hasken lantarki domin bata taba ganinshi a gidan ba, duk yadda mai karatu ke auno kuncin rayuwar da Badariyya take ciki ya wuce haka domin kunci ne na mutane marasa galihu da 'yancin kai, 'ya'yanta da ta samesu ta hanyar tursasawa, tamkar almajirai saboda tsabar wahala da suke sha, tasan tabbas in akayi bincikenta abin da za'a fara cin karo dashi a tare da ita shine infection, sannan wasu ciwukan su biyo baya, Runtse idonta tayi saboda azabar da takesha na cakalkalata da yakeyi, saida yayi fin awa yana abu daya, bayan ya gama yayi mata albishir da indai tana san ganin yan uwanta to ta cigaba da kasancewa mai biyayya da dauriya a gareshi kamar yadda ta kasance mishi a yau...... *Canada* Ohhh.. ya Allah Mukhtar ai sai ka karyani, ajiye remote din hannunta tayi ta karbi cupin da ya bata, "Mashaa Allah, nasan jika na is the best, Allah ya albarkaci rayuwarka.. ta karashe haďe da sumbatarshi... "Barka da gida Aunty!! Nadeeyah ta faďi a ďan russune, "Barka dai ta amsa babu yabo babu fallasa, ta cigaba da yi ma junior wasa.. Ciki Nadeeyah ta wuce ba tare da ta damu da yadda Anty Saude ta amsa mata gaisuwarta ba, ko wacce uwa hakan zatayi in dai danta ya fuskanci abunda Taheer ya fuskanta, soyayyar da take nunawa Junior shi yake sanya zuciyarta sanyi a duk lokacin da ta ga irin halin ko in kulan da Anty sauden ke nuna mata, kula babu wacce bata yi mashi, ita ko me zata ce mata banda godiya, sannan tana rokon Allah ya kawo lokacin da zata saka musu da mafificin alkhairin da sukayi mata..... "Me zaka ci?, noodles ko peppersoup? Kallon Taheer Junior yayi yace Daddy me zamu ci? A'a my dear ba cin abinci yanzu sai anyi wanka, jeka Mamma tayi

Table of Contents

Chapters

156 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156