Chapter 94
Chapter 94
number wayarshi ta bukata nan take ya karanto mata sannan yayi musu sallama suka wuce....... Tashin Husna Nadeeya ta dinga yi akan taje ta tada Musaddiq kar ya makara dan jirgin 6 zaibi zuwa lagos, mikewa tayi tana turo baki tace "kije ki tasheshi mana, ni bazan iya ba, hakuri ta shiga bata har ta samu ta yarda ta wuce dakinshi, kamshin turarenshi da taji ne ya bata tabbacin ya tashi, a tsaye ta sameshi yana gyara links din hannun rigarshi, "ashe ka tashi?, alhamdulillah na huta, dariya yayi yace aikin Mummy ne, tun dazu ta tasheni, ina matata? Hamma Husnah tayi tace "tana daki ita ta matsa min inzo in tasheka karka makara, sosai yaji dadi har cikin ranshi yace "muje in ganta kafin in wuce, A kofar shigowa suka kusa karo da Mummy rike da plate din indomie da kwai, Cup din hot choco kadai ya karba ya yi hanyar dakin su Nadeeyah, "Ina zaka je? Mummy ta fadi tana bin bayanshi, "amm zan je.... zan ---- dawo nan ka zauna kaci abinci, ko jirgin na ubanka ne in lokaci yayi bazasu jiraka ba, "Mummy, Nadeeyah bata da lafiya ne zai duba ta.... wani mugun kallo tabi Husnah dashi wanda yasa ta saurin murda kofa, "zo nan sakarya wacce bata san ciwon kanta ba, sum sum Husnah ta dawo inda Mummy take, kunnenta ta kama tace "wallahi kinji na rantse, wannan rawar kafar da kikeyi akan Nadeeyah in baki daina ba sai na ci miki mutunci, kuma in sake jin maganar tafiya Gombe a bakinki sai na tattaka ki, marar mutunci kawai.. ta karashe hade da dungure mata kai, kafa Husnah ta fara bugawa a kasa tana fadin "ni wallahi sai naje, hanyar dakin Daddy tayi Mummy tayi saurin tareta dan karansu na daren jiya baiyi mata dadi ba, yanzu in ta bari Husnah ta kai kararta tofah tasan bazai mata da kyau ba, "Ina matsayin mahaifiyarki kike kokarin bijire min har kike yunkurin kaini kara, ni zakuyi ma tawaye? Babu komai kuyi abin da kuka ga dama ta karashe tana matso kwalla, kewayeta sukayi suka shiga rarrashinta, dakyar ta hakura ta tasa keyar Musaddiq har mota sannan ne ta samu kwanciyar hankali..... Dubu dari biyu Papy ya bada kudin sadakin Nadeeyah, sai dubu dari na gaisuwa... cike da farin ciki Daddy da abokinshi Alh Abubakar suka karbi kudin, nan Daddy yasa biki wata biyu dan yana so ya samar musu gida a can lagos dan suyi nesa da duk wani tashin hankalin gida..... *(Shaff ya manta Raudha na lagos kuma duk tafi kowa matsala cikin 'yayan nashi,)...* ******* Woww mashaa Allah my little brother ya girma, yaushe aka sa bikin Daddy? "June amma bamu cire date ba, Maganar shirye shirye na kira inyi miki, inaga zan turo miki kudi ku shiga Dubai kuyi mishi siyayya, sannan zan bawa su Raliya su siyo wasu anan dan mahaifiyarku tace babu hannunta, dariya Anty Reemah tayi tace "ko sisinka karka kashe Daddy, zamu hadu mu hada mishi lefe na gani na fada, "wallhy naji dadin wannan hadin dan dama bana son Nadeeyah ta kufce mana, kullum cikin tunaninta nake.. "Ajiye kofin zobon dake hannunshi yayi ya dafe kanshi da ke sara mishi, "shikenan ya rasa Nadeeyah, tunda har akasa ranar auren ya fidda ranshi da tunanin ko Allah zai taimakeshi ta zamo tashi, maida kwallar da ke kokarin fito mishi yayi da sauri yace "wish u all the best Nadeeyah, Allah ya dawwamar dake cikin farin ciki... yasan Musaddiq na can yana nemanshi, haka itama Nadeeyar, bashi da karfin kunna waya yayi magana da ko daya daga cikinsu, dan raunin da yake ciki bazai barshi ya danne zuciyarshi ba, dole ya koka musu har su gane yana cikin damuwa, Yana cikin wannan tunanin yaji Anty Reemah ta dafashi tace "shine baka fadamin wannan abun dadin ba, yanzu sai mu fara shiri daga bangarenmu, dan bazan bar kowa yayi mishi kayan lefe ba, kai kuma sai ka shir---- Mum kinsan ina Msc, kuma mun kusa fara exams, dakyar zan samu zuwa, "cike da Mamaki tace "Hilal... Musaddiq ne fa, kada kanshi yayi cike da damuwa yace "Mum bance bazani ba, amma for nw banda karfin shirye shirye, plsss ku barni inyi karatu... Mikewa tayi cike da tausayin danta tace "take ur time dear, Allah ya bada sa'a... tana kaiwa nan ta wuce kitchen ranta duk a dagule..... Gaba daya Nadeeyah ta mance damuwarta tunda tazo garin gombe, gidan karamci, wani irin ji dasu Mami takeyi kamar ita ta tsuguna ta haifesu, Yawo kuwa babu gurin da basu je ba a cikin Gombe, ga wani shiri na musamman da Mami tasa akewa Nadeeyah wanda ya kara fitar da kyawunta ta ciko tayi bulbul, fatar jikinta sai sheki takeyi ga santsi kamar tarwada... Husnah da Hafeez kuwa wata shakuwa mai kama da soyayya ce ta musamman ta shiga tsakaninsu, tun Hafeez na dari dari har ya saki jikinshi sosai da ita, raba dare sukeyi suna tsaftattaciyar hirarsu mai ban sha'awa, da Papy ya lura da hakan ya kirasu duk su biyun ya tambayesu, Husna ce ta fara amsawa da tana sonshi, sannan ne Hafeez ya samu karfin gwiwar bada tashi amsar, farin ciki marar misaltuwa Papy ya shiga.. sallamarsu yayi hade da kiran Daddy ya labarta mishi, Daddy cike da jindadi yace to ai bazamu jira ba, gara a hade bikin ayi shi rana daya, nan suka gama tsara yadda zasuyi sannan sukayi sallama cike da jindadi.... Kwanciya Daddy yayi yana kabbara da girmama hukuncin ubangiji, wato ubangiji ya hanashi auren Suwaiba saboda wannan ranar da auratayya zata bullo a tsakanin jinin da suka yi tsaftattaciyar soyayya ta tsakani da Allah, lallai *kaddara* itace jigon rayuwar dan Adam, domin da ita yake yawo duk inda zashi.... ina ma Suwaiba zata dawo taga hukuncin ubangiji, taga yadda rayukan 'yayanta suka canza, wata yar kwallar murna ya share yayi adduoinshi hade da runtse idanuwanshi...... Hauka ne kadai Mummy bata yi ba da taji labarin hade auren harda na Husnah da suka gama maganarta da kawarta Hajiya Safara'u, babu irin masifar da batayi ba, shiko Daddy ko a jikinshi kudin kayan kitchen ma yayi mata transfer zuwa account dinta dan sauran da kanshi zaiyi su, Sa kai yayi ya fita ya bar gidan dan lagos ma zai tafi da daddare akan maganar gidan da aka samu... Kuka ta zauna a parlor tana yi sosai kamar an mata mutuwa, bakin cikin da take ciki yau har gwammaci dama bata taba sanin Daddy a rayuwarta ba, Badar ce ta fito tana hamma, duk wainar da ake toyawa a gidan bata da masaniyarsu dan ba zaman gidan takeyi ba, da sauri ta isa gurin Mummy tana tambayar abun da yasa ta kuka, Ganin da tayi wa Badariyya ya sa hankalinta dan kwanciya, dan wani abu da ya darsu a ranta, tasan Badariyya ce kadai zata iya yi mata maganin damuwarta... Hannunta ta rike ta sake rushewa da kuka tace "Badar na shiga uku, Musaddiq zai auri Nadeeyah, Hafeez kuma Husnah, kinji a inda zan kare a ya'yan da basu da asali, yayan mai gadi ni zainab..... Wani irin ihu Badar ta saki tace "Whattt? Nadeeyah zata auri Musaddiq dina.... ta fadi hannu na rawa tana dafe kirji....... Mrs Tijjani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156